Yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da raba Zamfarawa da garuruwansu
Idan muka yi sa’a muka samu abinci muna ci, amma idan ba mu samu ba ganye muke dafawa.
Ta’asar ’yan ta’adda a wasu yankunan Jihar Zamfara na ci gaba da ta’azzara a kusan kowace rana, duba da yadda wasu kauyuka da birane ke rayuwa cikin firgici da kuncin rayuwa tare da zama cikin zullumin a koyaushe za a iya kai musu hari a kashe su ko a tarwatsa su.
A baya bayan nan, harin da aka kai wanda ya daga hankalin jama’a shi ne na kauyen Sakajiki inda ’yan bindiga suka yi kwana uku a jere suna hari; tun daga ranar 14 zuwa 16 ga Oktoban nan.
- Atiku zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Litinin — PDP
- Za a kammala bututun iskar gas na Ajaokuta-Kano a 2024 —NNPC
Daruruwan fusatattun matasa a kauyen sun fito don nuna rashin jin dadinsu inda suka rufe hanyar da ta bi kauyen a hanyar Kauran Namoda domin hana mutane wucewa.
Wannan al’amari ya ja hankalin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Muhammad Dalijan da Sarkin Kauran Namoda, Dokta Sanusi Muhammad Ahmad Asha, wadanda dole suka fito suka bai wa wadannan matasa hakuri kafin su bude hanyar.
’Yan sanda sun yi alkawarin kawo cikakken tsaro a yankin domin dakile wannnan mummunan ta’addanci ta ’yan bindiga.
Sai dai, bayan mako daya da wannan alkawari na ’yan sanda, wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewar babu wani karin ’yan sanda da aka kai musu.
Wani rahoto da aka samu a ranar 22 ga Oktoban nan an sake samun wani harin a yankin Kauran Namoda tare da sace wasu mazauna yankin.
Haka a Karamar Hukumar Tsafe, a ranar 20 ga Oktoba wasu gaggan ’yan bindiga sun tare wasu matafiya tare da kashe daya daga cikinsu, wasu suka ji raunuka a kauyen Machiya.
Wani mazauni yankin ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun bude wa matafiyan wuta a daidai lokacin da direban wata mota dauke da fasinjoji ke tafiya.
Yanzu haka wadanda suka tsira suna Babban Asibitin Tsafe suna jinya.
A wurare da dama na Jihar Zamfara, wakilinmu ya gano cewa kauyukan da suka fi fama da ta’addanci sun hada da Munhaye, Yankuzo, Danjibga, Mashayar Zaki, ’Yan Warin Daji da Kurar Mota da sauransu.
Sai dai, wani mazaunin yankin da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa wani shugaban ’yan bindigar Dan Karami da Bebo sun samu farraka a tsakaninsu a makon da ya gabata yayin da rashin jituwar ke shafar kauyukan yankin Tsafe ta yadda ake kai wa al’umma hari babu dalili.
Malam Nasiru Muhammad wanda ya yi hijira zuwa Gusau daga Tsafe saboda ta’azzarar hare-hare a yankin, ya shaida wa Aminiya cewa ya shafe tsawon shekara hudu a Gusau tun hijirarsa daga kauyen Danjibga da ke Karamar Hukumar Tsafe.
Magidancin mai ’ya’ya 4, Muhammad ya ce ’yan bindigar sun tarwatsa kauyuka da dama ta yadda, “Ba za ka iya samun ko da kare ba a wasu kauyukan da abin ya shafa sakamakon sun yi awon gaba da shanu da duk wani abu mai amfani tare da tursasa mazauna yankin yin hijirar dole don tsira da rayukansu.
“Babu wani kauye da yake zaune lafiya kalau a yanzu a Karamar Hukumar Tsafe saboda lokaci zuwa lokaci ’yan bindiga na kawo hare-hare babu kakkautawa.
“Mazauna kauyuka da dama sun mika wuya ga ’yan bindigar. Suna yi musu aiki a gonaki da gidagjensu duk lokacin da suka bukaci hakan, wannan ne kadai hanyar da za su zauna da ’yan bindigar lafiya.
“Duk wanda yake son zama lafiya to sai ya bi umarni da sharuddan wadannan mutane ko ya yaba wa aya zakinta,” in ji shi.
Wasu yankuna kamar kananan hukomomin Anka da Gumi yanzu sun zama wuraren da ba a iya zuwa ko da wasa tsakanin matafiya da mazauna garin.
Duk da Anka na da dan saukin yanayi amma kauyuka kamar Mai Galma, Gurusu, Makakari, Duhuwa da Kirsa suna nan babu ko da kiyashi da ke rayuwa a cikinsu.
Haka a Karamar Hukumar Maru, kauyuka da dama kamar ’Yar-Tasha, Dan Gulbi, Mayanchi, Dansadau, Kanoma, Dankirbi, Magami da kuma Bindin a Jihar Kebbi da suke da iyaka da Maru sun tabu matuka saboda ta’asar ’yan bindigar.
Malam Auwal Isa mazaunin kauyen ’ Yar-Tasha, ya tabbatar wa wakilinmu cewa, “A yanzu kaso 10 ne kacal suke zaune a kauyukansu yayin da kaso 90 suka yi hijira. Muna cikin yanayi marar dadi.
“Ba mu da wani katabus a kasuwanninmu, kan hanya ko gidajenmu. Kai babu wani wuri da ke zaune lafiya a wannan yanki. “Muna iya noma iya kaso 20 ne na gonakinmu.
“Kaso 80 na nan ya zama juji saboda ’yan bindiga. Wannan al’a’mari ba karamin taba harkar noma ya yi ba a Zamfara.
“Maru na daya daga cikin wuraren da ake samun kayan noma sosai amma yanzu wannan ya zama tarihi domin mutane ba za su iya zuwa su yi noman.
“Matafiya dole sai sun tsaya a ’Yar-Tasha na kwana biyu sannan su dangana da kauyen Magami su yi kwana biyar kafin a samu sojoji su yi musu jagaba zuwa Gusau.
“A haka muke tafiya rayuwa a wannan yanki. Ina mai tabbatar maka cewa mutane suna cikin kunci da wahalar rayuwa a wannan yanki,” in ji shi.
Maman Jummai wata mace ce da ta yi hijira daga Dansadau zuwa Gusau, kuma ta shaida wa Aminiya cewa rayuwa cikin firgici ne ya sa ta yin hijira saboda suna zaune a karkashin ikon ’yan bindigar.
Ta kara da cewa duk da suna zaune ne a cikin wani kango a Gusau, hakan ya fi musu kwanciyar hankali a kan zamansu a kauye a karkashin ’yan bindiga.
“Wasu ’yan bindiga sun shigo kauyenmu a ranar wata Juma’a da maraice suka tarwatsa mu, muka shiga cikin dazuzzuka domin tsira da rayukanmu.
“Daga nan ne muka fara hijirar dole domin ba za mu iya komawa ba,” in ji ta.
Hauwa’u Halliru, uwa ce mai ’ya’ya 8 da ta yi hijira daga kauyen Rijiyar Tsakar Dawa zuwa Gusau saboda miyagun hare-haren ’yan bindiga.
Ta ce, “Sun kashe min uku daga cikin ’ya’yana. Sun tafi da da yawa daga cikin mutanen kauyenmu, yayin da suka kawo wannan hari.
“Sun kawo harin ne lokacin da muke tsakiyar barci kafin asuba, sai kawai muka fara jin karar harbeharben bindiga ta ko’ina.
“Kafin ka ce kwabo, sun kashe wasu sun fara dibar mana kaya. Sun sace mana da shanu da awaki da duk wani abu mai amfani.
“Idan muka yi sa’a muka samu abinci muna ci, amma idan ba mu samu ba ganye muke dafawa ko mu ci danyensa mu zauna da ni da ’ya’yana.
“Haka muke rayuwa a cikin wannan kango,” in ji ta.
Daya daga cikin ’ya’yanta, Abubakar Halliru ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da harin ya auku yana makarantar kwana a Damba da ke cikin garin Gusau, sai kawai jin bakin labari ya yi.
Ya ce ya yi yunkurin zuwa kauyen don neman ’yan uwansa amma hukumar makaranta ta hana shi.
“A ranar Alhamis da yamma na hadu da wani mazaunin kauyenmu. Shi ne yake shaida min cewa ’yan bindiga sun tarwatsa garin koya ya gudu yayin da suka kashe wasu da dama.
“Daga nan ne hukumar makarantar suka dukufa wajen neman ’yan uwana inda daga baya na yi nasarar haduwa da su a wannan kango,” in ji shi.
Aminiya ta tattara bayanan yankunan da suka fi haduwa da hare-haren ’yan bindigar inda bincike ya nuna cewa babu isassun jami’an tsaro a yankunan musamman ’yan sanda da jami’an sibil difens.
Yunkurin jin ta bakin hukumomi kamar Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Zamfara, Muhammad Dalijan da bangaren gwamnatin jihar ya ki yiwuwa yayin da dukkan kokarin samun hadin kan Mai ba Gwamna Shawara kan Harkokin Yada Labarai, Suleiman Bala Idris da Kakakin ’Yan sandan Jihar Zamfara, SP Yazid Abubakar kan lamarin ya ci tura.