Yadda ’yan bindiga suka fal wa garinmu da sanyin safiya -’Yan gudun hijirar Rukubi

A makon da ya gabata ne wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari a kauyen Rukubi da ke yankin raya kasa na Ikya a jihar Nasarawa, da sanyin safiya, inda suka kashe sama da mutum 40. A sakamakon haka  al’ummar  yankin da dama sun yi gudun hijira […]

Yadda ’yan bindiga suka fal wa garinmu da sanyin safiya -’Yan gudun hijirar Rukubi
Yadda ’yan bindiga suka fal wa garinmu da sanyin safiya -’Yan gudun hijirar Rukubi

A makon da ya gabata ne wadansu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari a kauyen Rukubi da ke yankin raya kasa na Ikya a jihar Nasarawa, da sanyin safiya, inda suka kashe sama da mutum 40. A sakamakon haka  al’ummar  yankin da dama sun yi gudun hijira zuwa wadansu kauyuka da suke makwabtaka da su.
Wakilinmu ya ziyarci wadanda lamarin ya shafa da suke zaune a makarantar firamire da ke garin Doma (Central Primary School Doma) inda ya tattauna da su game da lamarin da kuma jin asarar da suka yi.
Malam Ane Adenu Abubakar daga Rukubi ya bayyana cewa, “A gaskiya an yi mana abin da ba mu ji dadi ba kuma ba zamu manta ba. An kone mana gidaje da motoci da kuma Babura, duk wadannan abubuwa mun rasa su, shi ya sa muka gudu nan. Da muka zo nan kodashike gwamnatin jihar nan ta taimaka mana da abinci, amma a gaskiya abincin ya yi karanci don muna da yawa sosai a nan. Wadansu shugabannin Cocin Katolika da ke nan garin Doma su ma sun taimaka mana da buhunan shinkafa guda uku da rabi da wadansu kayayyakin abinci. Kiran da zan yi ga gwamnati shi ne ta turo jami’an tsaro da dama zuwa wannan yanki, musamman kauyen Rukubi inda abin ya fi muni don mu samu damar komawa gidajenmu mu cigaba da harkokinmu na yau da kullum.”
Sai wani maisuna Agbadu Adegezin wanda ya yi bayani kamar haka, “Ni dai na rasa kannena guda biyu maza kuma an kone min gida da baburana biyu. Gwamnati ta taimaka mana da abinci da muka zo nan. Amma kamar yadda dan uwana ya bayyana maka abincin ya kasa mana, don idan ka lura za ka ga masu gudun hijiran suna da yawa. Sabodahaka ina kira ga gwamnati da mawadata da su taimaka mana . A kuma tabbatar an tura jami’an tsaro da dama yankin don kamo wadanda suka aikata wannan aikin shaidan din.”
Wani maisuna Emmanuel Husaini kuma ya bayyana cewa, “Ni daga Rukubi nake, a cikin kauyen Rukubi kam an kone gidaje da yawa an kuma kashe mutane da dama. Mutane da aka kashe za su kai guda 40. Ni kaina an kone min baburana uku an kuma kone min gida. To, ga shi mun gudu daga gidajenmu mun zo nan. Gwamnati ta taimaka mana da abinci sai dai bai ishe mu ba . Ba wani ko wata kungiya da ya zo ya taimaka mana da abinci ko wani abu daban, bayan buhun shinkafa uku da rabi da shugaban Cocin Katolika a nan Doma ya ba mu. Sabodahaka muna rokon gwamnati da ta cigaba da taimaka mana don muna da yawa a nan, kuma a halin yanzu wadansu ma na cigaba da zuwa.”
Shi ma wani mai suna Timothy Juga ya bayyana cewa, “Ni daga Ogbata ne. A gaskiya mun yi asarar rayuka da dukiyoyi da dama sakamakon harin da wadansu ‘yan bindiga da bamu san ko su wane ne ba suka kai mana a makon da ya gabata. Kuma abu na biyu shi ne yawancinmu da kake gani a nan manoma ne, abincin gonanmu da muka adana a gidajenmu duk an kone. Abu na uku kuma shi ne, abincin da gwamnati ta ba mu bai ishe mu ba. Ina so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga masu hannu da shuni da kuma sauran kungiyoyi a jihar nan da kasa baki daya da su yi koyi da abin da wadansu daga Cocin Katolika na nan garin Doma suka yi mana. Sun ba mu buhunan shinkafa da sabulu da magi da kayan miya, da dai sauransu. Gwamnati kuma ta kara zage damtse wajen kama duk wadanda suka aikata wannan danyen aiki ta kuma turo isassun jami’an tsaro zuwa yankin don ba mu damar komawa gidajenmu mu cigaba da harkokinmu na noma.”
 Wakilinmu ya samu damar ganawa da wadansu mata  masu gudun hijiran guda hudu, watau Misis Kasuwa Moses da Jummai Inusa da Matina Adamu da kuma Misis Fibi John, wadanda suka bukaci daya daga cikinsu, wato Misis Fibi John ta yi bayani a madadinsu, inda ta bayyana cewa, “kwarai da gaske wadansu ‘yan bindiga sun kai mana hari a kauyen Rukubi da sauran kauyuka da ke yankin, inda suka kone mana gidaje suka kuma kashe mana mutane da dama. Ni da nake magana da kai nan ma an kashe mijina da ‘yanuwana uku a wannan hari. Ba ni da abin da zan ce sai dai in ce Allah Ya isa. Ina da yara biyar, maza biyu mata uku, a halin yanzu ban san wanda zai taya ni kula da su ba. Taimako kam gwamnati ta taimaka mana da abinci tunda muka zo nan garin Doma, amma kiran da zanyi shi ne, a tura jami’an tsaro da dama wannan yankin namu, don ba zamu iya komawa gidajenmu ba a halin da ake ciki.”
  Aminiya ta garzaya zuwa Cocin Katolika da ke garin Doma don jin ta bakin shugabannin cocin game da wannan batu amma hakan ya ci tura, kasancewar shugabannin ba sa nan sun tafi wani taron shugabannin Cocin Katolika a Bauchi, kuma babu wanda wayarsa ke tafiya a cikinsu.
Da Aminiya ta tuntubi  jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa DSP Mike Ada, ya tabbatar  da aukuwar  lamarin ta bakin mukaddashinsa, kuma ya bayyana cewa a halin yanzu kura ta lafa, don tuni rundunar ta turo jami’anta da dama zuwa yankin don shawo kan lamarin ta kuma gudanar da bincike don kamo wadanda suke da hannu cikin lamarin.
Daga nan sai ya yi amfani da wannan damar inda ya yi kira ga al’ummar jihar baki daya da su daina daukar doka a hannunsu kuma su rika bin doka da oda ta hanyar  kai kara ga hukumomin da suka dace duk sa’adda suka samu wata matsala da wani, don a cewarsa, rundunar ‘yan sandan za ta dauki mataki a kan duk wanda aka kama a jihar yana tada zauni tsaye, musamman a wannan lokaci da jihar ke fuskantar kalubalen matsalar tsaro.