Yadda ’yan bindiga suka karkashe juna a Katsina
’Yan bindiga da dama sun sheka lahira a fadan da kungiyoyinsu suka gwabza a Safana
’Yan bindiga da dama sun sheka lahira bayan kazamin fada ya kaure tsakanin kungiyoyinsu a Karamar Hukumar Safana, Jihar Katsina.
Gungun ’yan bindiga karkashin wani mai suna Mani Sarki sun gwabza fada da bangaren Dankarami wanda ke da goyon bayan gungun Abu Radda a kauyen Illela na Karamar Hukumar.
- Abu 5 da ke sa masoya batawa a lokacin hira
- Na yi wa mata 50 fyade da fashi a gidaje 100
- Duk wanda ya karya dokar COVID-19 zai yi wata 6 a gidan yari
- Kotu ta kwace kudaden tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari
Majiyarmu ta ce sauran ’yan bindigar na ganin Mani Sarki a matsayin zakka saboda ya tuba daga harkar ya rungumi shirin afuwar Gwamnatin Jihar Katsina.
Musabbabin rikicin
Majiyar da Aminiya ta zanta da ita ta ce bayan Mani Sarki ya tuba ne ya koma kauyen Illela domin fara sabuwar rayuwa, amma wasu yaransa ba su bi shi ba.
“Wasu ’yan bindiga karkashin wani Dan Da daga gungun Alhaji Dankarami sun kai hari Illela, amma daya bangaren ya fatattake su suka tsere suka bar makamansu, ciki har da wata babbar bindia da aka samu a matsayin ganima. Abin da ya fusata su ke nan, ba su manta ba.
“Sannan wani kanin Sarki Mani ya taba yin garkuwa da matar wani dan bangaren Dangwate sai da aka ba shi N500,000 kudin fansa kafin ya sake ta.
An kashe kanin Sarki da matarsa
Wata majiyar kuma ta ce an kashe wani kanin Sarki mai suna Chirwada da matarsa aka kuma jikkata wasu mutum uku da a halin yanzu ake jinyar su a Katsina.
Bayan haka bangaren Sarki ya taba hana wasu ’yan bindiga shiga kai hari ko shiga kiwo da dabbobinsu yankin, duk da yawan ciyawar da ke yankin.
Wasu rahotanni sun nuna cewa Dankarami, Dangwate da Mai Komi sun kai harin ramuwar ne da nufin kwato bindigarsu da kudinta ya kai Naira miliyan biyar.
Wadannan abubuwan ne ake ganin sun haifar da gaba a tsakanin bangarorin.
Majiyar ta ce kimanin mahara 300 ne suka kutsa shiga Illela suna ta harbi kan mai uwa da wabi da misalin karfe 5 na yammacin ranar Alhamis na makon jiya.
Ba su sani ba ashe bangaren Sarki na sane da harin na su, sun kuma shirya musu.
“Sabanin ra’ayi”
Wata majiyar kuma ta ce fadan ya auku ne sakamakon bambancin ra’ayi tsakanin ’yan bindiga masu goyon bayan shirin afuwa da zaman lafiya na Gwamnatin Jihar Katsina da masu adawa da tsarin.
“Daya daga cikin yaran Sarki mai suna Mani da yake goyon bayan shirin ya baro dajin ya koma Illela da zama amma bai mika wa gwamnati makamansa ba. Saboda haka, marasa goyon bayan shirin ke ta hakon sa.
“’Yan bangaren Dangwate sun shigo Illela ne domin su kama mutumin. Da suka zo sai suka rika duba gida-gida suna neman shi.
“Da suka shiga gidan Sarkin Fawa Mu’azu, sai suka samu bindiga harbi-ruga, suka yi zargin shi dan banga ne, kuma da ma ba a shiri tsakanin ’yan banga da ’yan bindiga.
“Ya gaya musu cewa shi ba dan banga ba ne amma sai da suka suka harbe shi suka kashe shi.
“Sun kuma raunata wasu mutum hudu a kauyen, yanzu haka mutanen na asibiti ana jinyar su”.
Majiyar tamu ta ce maharan sun shafe kusan awa takwas a harin da suka kai kauyen inda suka kona motoci da shaguna suka kuma yi awon gaba da dukiyoyin jama’a.
“Sai dai ba su cimma burinsu na kama Mani ba, wanda ke goyon bayan shirin gwamnati na zaman lafiya,” inji majiyar.
Ta ce da suka koma daji sai suka far wa bangaren da Dankarami ke jagoranta, suka kashe da dama daga cikinsu.
Majiyar tamu ta ce ana hasashen an kashe sama da mutum 100, ciki har da kananan yara.
“Shi kansa Dankarami da kyar ya sha saboda an ma harbe shi a hannu,” inji majiyar.
Game da ko jami’an tsaro sun kai dauki a lokacin harin, wata majiyar ta shaida wa Aminiya cewa “ba su zo ba saboda sun san fada ne tsakanin ’yan bindiga ba da mutanen gari ba.”
Ta ce an kashe mutane da dama amma ba za ta iya fadin yawansu ba.
Mun tuntubi kakarin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya shaida mana cewa suna kan gudanar da bincike tukuna.