‘Yadda ’yan bindiga suka kashe Albani a gabana’

daya daga cikin wadanda suke cikin mota daya da marigayi Sheikh Albani mai suna Malam Bello Nakaka dalibi ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bude musu wuta har suka kashe malaminsu, inda ya nuna cewa bude musu wuta suka yi ta ko’ina. Malam Bello, wanda wakilinmu ya gana da shi a asibitin da yake kwance, ya […]

‘Yadda ’yan bindiga suka kashe Albani a gabana’

daya daga cikin wadanda suke cikin mota daya da marigayi Sheikh Albani mai suna Malam Bello Nakaka dalibi ya bayyana yadda ’yan bindiga suka bude musu wuta har suka kashe malaminsu, inda ya nuna cewa bude musu wuta suka yi ta ko’ina.
 Malam Bello, wanda wakilinmu ya gana da shi a asibitin da yake kwance, ya bayyana cewa, “Ni a iya abin da na gani ko zan iya tunawa shi ne muna cikin mota ana tafiya, mun zo daidai Central sai malam ya tsaida mota, tunda da ma shi ne yake tukawa, ya shiga wani shago ya yi sayayya sannan muka taso, muna cikin tafiya, mun kawo wajen wadansu tsofaffin gidaje kuma a wajen akwai irin tulluwar nan ta hanya, to ya daga kafa ke nan sai kawai wani mai babur ya zo da sauri, sai wanda yake goye da shi ya fara yin harbi, kuma Malam ya fara harba.”
 Malam Bello ya kara da cewa, “Abin da na lura da shi shi ne su wadannan makisa suna sanye da bakaken kwat ne kuma kafafuwansu akwai takalma but, amma ni ban ga fuskar kowa daga cikinsu ba, kawai na ga jiki ne, to daga nan sai kawai muka ji an bude mana wuta ko ta ina, kuma ban san adadin mutanen ba, ban da wadannan mutanen biyu da na gani, sai dai kawai mun ji ta ko’ina kawai ana harbinmu ne, kuma suna da yawa, kuma a zatona sun yi mana kwaton-bauna ne, suka rufe mu da harbi, wasunmu suka kwanta, sai salati da addu’a muke ta yi. Bayan sun gama harbinmu sai muka ji kamar an yi ruwa an dauke, to malam jikinsa duk jini, sai ya yi kokarin fita, bayan ya bude kofar motar ya fita, sai jini ke ta zuba, to daga nan sai ya fadi, sai ni da Usman muka ja shi gefe. Daga nan sai muka shiga kiran ’yan uwa, kafin nan duk wanda ya zo da mota muka tsaida shi don ya taimake mu sai ya gudu, can sai ga wani saurayi ya zo da mota, sai muka kama Malam ni da Usman, jini yana ta zuba muka sanya shi a mota.”
Ya ci gaba da cewa, “Wadanda suka mutu ma ban sani ba, saboda hankalina yana kan Malam, sai daga baya ake min bayanin cewa wane da wane sun mutu. Kuma kamar yadda na yi maka bayanin cewa wadanda suke harbinmu a mashin suka zo, sai dai ban san iya adadin wadanda suke wajen a kwankwance ba, don gaskiya suna da yawa, amma ni ban ga mota ba. Wannan shi ne iya abin da na sani.”
Haka kuma wani wanda bai so a ambaci sunansa ba, shi ma ya bayyana wa Aminiya yadda al’amarin ya faru inda ya ce, “Ina cikin motata, sai na ga wata bakar mota Golf da wata C-Class sun sanya ni a tsakiya a guje, sai  ita C-Class din ta sha gaban motar da malam yake ciki, sannan wadansu kuma suna kan babur sai kawai suka fara ruwan harsasai, ni ma kaina Allah ne kawai Ya tsare ni. Daga nan sai na ji shiru, na ji suna magana da Hausa da Turanci, kafin sauran su hau mota su tafi abinsu, kuma mikewa suka yi ta gaban makarantar malam suka wuce, duk mai motar da ya zo, sai ya juya ya tafi abinsa. Daga nan ne muka samu wadanda suka fara tsayawa don kawo mana dauki.”
A yanzu haka dai duk an sallami wadanda suke kwance a asibitin koyarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sai mutum daya mai suna Faruk Ahmad Rabi’u, wanda aka harbe shi a kafada, wanda hukumar asibitin ta ce ba za a ba mu damar mu gan shi ba sai kamar  mako daya, a dalilin halin da yake ciki.
Washegarin bayan faruwar lamarin, Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Mukhtar Ramalan Yero ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Sheikh Albani, inda ya ba su tabbacin cewa gwamnati za ta yi iyakar kokarinta ta gano wadanda suka aikata wannan kisan.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Aminu Lawal ya ce sun fara farautar makisan. Ya kara da cewa, kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kaduna ya umarci kwamandoji tare da DPO na kowane yanki da ke fadin jihar da su kara sa ido domin ganin an samu yadda ake so.
A ranar Asabar da ta gabata (1/02/2014) ne dai wadansu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka yi sanadiyyar mutuwar wannan babban malami mai wa’azin addinin Musulunci, Sheikh Auwal Adam Albani Zariya tare da matarsa da dansa ta hanyar harbinsu da bindiga.
Wakilinmu ya ruwaito cewa Sheikh Albani ya rasa ransa ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gidansa da ke Gaskiya Layout a Tudun Jukun da ke Zariya, bayan ya kammala karatun da yake gabatarwa na Sahihul Buhari a makarantar Markas da ke Tudun Wada Zariya.
Mutuwar wannan Malami ta tayar wa al’ummar musulmin Zariya da na sassan duniya hankali, domin a lokacin da labarin rasuwarsa ya  bayyana kowa ka gani za ka ga akwai alamar damuwa a tare da shi, har da wadanda ba ma musulmai ba ne.
An yi wa gawar Albani jana’iza da karfe goma na safe. A wannan lokacin, a Zariya, tun daga

A yayin jana’izar Sheikh Albani

hanyar gidansa har zuwa inda aka rufe shi a makabartar Dambo da ke kan hanyar Jos, komai ya tsaya cik, don babu wajen walwala tsawon kilomita biyar.
Kafin rasuwar Sheikh Albani a wa’azozin da yake gabatarwa yakan rika yawan magana a kan hadin kan musulmai, kuma mutuwar tasa ta nuna an amsa wannan kira da yake yi, domin kuwa a wajen jana’izarsa babu maganar bangare na addini.
Daga cikin manyan malaman da suka kasance a wajen jana’izar akwai Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano, wanda ya bayyana cewa, kisan da ake yi wa malaman addinin Musulunci yana nuna gaskiyar wannan addini ne, don haka harka ta wa’azi ko ba sa so ba za a fasa ba.
Shi kuwa Malam Musa Sahabi, babban limamin makarantar Sheikh Albani, wato Markas, cewa ya yi, rashin Albani a wannan lokaci ba karamar asara ba ce ga al’ummar Najeriya, domin jarumi ne, mai kishin addini tare da tattalin zaman lafiyar jama’a.
Shi ma da yake tsokaci, jami’in hulda da jama’a na Sheikh Albani, Dokta Abdulganiyu Abdulrafi’u ya karyata wani mai suna Muhammadu Lawal ne da ya fito a kafar wata jarida mai suna Sahara Reporters, ya ce shi aminin malam ne, kuma ya nuna cewa su suna zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne suka aikata wannan kisan. Dokta Ganiyu ya ce wannan mutum ya furta haka ne domin a boye ainihin wadanda suka yi kisan.
Ya bukaci al’ummar musulmi su taya su addu’ar Allah Ya tona asirin wadanda suka yi wa Albani kisan gilla, tare da rokon kowa ya zauna lafiya.