‘Yadda ’yan bindiga suka kashe dana suka sace iyalina 17’

Wani magidanci da ’yan bindiga suka harba tare da kashe dansa sannan suka kwashe iyalan gidansa 17 a kauyen Udawa da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna, ya ce bai yi tunanin zai rayu ba. Magidancin mai suna Yakubu Gurmi ya ce ’yan bindigar sun harbe shi ne a kafafunsa biyu a hanyarsu ta […]

‘Yadda ’yan bindiga suka kashe dana suka sace iyalina 17’

Yakubu Gurmi

Wani magidanci da ’yan bindiga suka harba tare da kashe dansa sannan suka kwashe iyalan gidansa 17 a kauyen Udawa da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna, ya ce bai yi tunanin zai rayu ba.

Magidancin mai suna Yakubu Gurmi ya ce ’yan bindigar sun harbe shi ne a kafafunsa biyu a hanyarsu ta zuwa gona.

Lamarin ya faru ne a kusa da Gonar Lema a ranar Asabar da ta gabata a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari lokacin da ’yan bindigar suka yi musu kwanton-bauna.

Ya ce a lokacin ’yan bindigar sun harbi mutum uku ciki har da Baby Yakubu da Blessing Yakubu sai Omega Yakubu sai shi.

Sun kuma tafi da sauran iyalan gidansa su 17 ciki har da mace mai shayarwa mai suna Abigail da danta.

“Akwai wacce aka harba a nono sai kuma wacce aka harba a kafada har ta samu karaya. Ni kaina ban taba tsammanin zan rayu ba,” inji shi.

Ya shaida wa Aminiya cewa an kwashe wadanda suka samu raunuka zuwa wani asibiti a Kaduna domin duba lafiyarsu.

Sai dai ya ce daga bisani an koma da su zuwa wani asibiti a Birnin Gwari saboda ba su da kudin da za su kula da su a Kaduna.

Daya daga cikin wadanda aka raunata, Omega ya rasu a asibiti a daren Litinin da ta gabata.

Ya ce har yanzu ba su samu labarin halin da sauran suke ciki ba domin ’yan bindigar ba su kira su ba.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ba ta ce komai ba dangane da lamarin tun ranar Lahadi da aka tuntubi Kakakinta Mohammed Jalige wanda ya ce zai binciki lamarin.

Shi ma Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan bai amsa sakon waya da aka tura masa don jin ta bakinsa ba.