Yadda ’yan bindiga suka kashe juna wajen rabon kudin fansa

An tsinci gawarwakinsu a warwatse da cikin daji.

Yadda ’yan bindiga suka kashe juna wajen rabon kudin fansa

Dajin da Sheikh Gumi ya yi wa ‘yan bindiga da’awa a Jihar Neja, daya daga jihohin da ke fama da matsalar tsaro. (Tsohon hoto).

Kwanan wasu masu garkuwa da mutane ya kare a Jihar  Taraba bayan da hayaniya ta kaure a tsakaninsu lokacin da suke kokarin raba kudin fansar wani wanda suka yi garkuwa da shi.

Fadan ya kaure a tsakaninsu ne a lokacin da suke shirin raba kudin da suka karba a hannun wani dan kasuwa da suka kama a garin Jalingo a makonnin baya.

Majiyarmu ta gano cewa rikicin ya kaure ne a karkashin wani dutse da barayin suke boyewa a kusa da wani kauye a Karamar Hukumar Ardo Kola da ke Jihar Taraba.

Mutanen kauyen  sun ce sun ji hayaniyar ’yan bindigar da tsakar dare a lokacin da suke fada da juna, da gari ya waye kuma suka tsinci gawarwakinsu a jejjefe a wurare daban-daban.

Aminiya ta gano cewa mutanen da ke zaune a yankin da abin ya faru sun san cewa ’yan bindigar suna zaune a karkashin dutsen, amma kuma ba su sanar da hukuma ba saboda gargadin da barayin suka yi musu.

“Mukan ga suna wucewa  ta jikin  Kogin Mallam Garba a kan babura zuwa wuraren buyarsu amma ba za mu iya sanar da hukuma ba saboda gargadin da suka yi mana; A wasu lokutan mukan ga har yadda ake kawo masu kudin fansa a cikin daji,” a cewar wani mazaunin kauyen.

Sai dai  mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya ce ba su da labarin aukuwar ala’amarin a hukumance, saboda ya yi tafiya zuwa wani wuri a lokacin da aka yi kokarin ji ta bakinsa.

Ya ce da zarar ya samu dawowa zai yi kokarin bincike a kan al’amarin.