Yadda ’yan bindiga suka kashe mutum 4 suka sace 39

’Yan bindiga sun sace mutane 39 bayan sun kashe wasu mutum huɗu a wasu yankunan Abuja da kuma Jihar Neja.

Yadda ’yan bindiga suka kashe mutum 4 suka sace 39

‘Yan bindiga

’Yan bindiga sun sace mutane 39 bayan sun kashe wasu mutum huɗu a wasu yankunan Abuja da kuma Jihar Neja.

A ranar Juma’a ’yan  bindiga suka kutsa yankin Azu a Jihar Neja, suka kashe mutane uku suka sace wasu takwas.

Kafin nan a ranar Alhamis ’yan bindiga sun kai hari a yankin Kuduru, Karamar Hukumar Bwari a Birnin Tarayya, suka yi garkuwa da mutane 18.

Da farko a ranar Asabar, 23 ga Disamba, ’yan bindiga a Jihar Neja sun mamaye yankin Garam da ke makwabtaka da Bwari, suka kashe wani faston Cocin Redeemed (RCCG), suka yi garkuwa da wasu mutane 13.

Wata ’yar yankin Garam, Misis Juliana, ta ce a gidan farko da ’yan bindigar suka yi kuskuren shiga suka tambayi gidan faston.

Ta ce: “’Yan bindiga sun shiga wani gida, suka tisa keyar wasu yara maza biyu domin su kai su gidan faston.

“Da zuwansu sai suka yi garkuwa da daukacin iyalinsa, amma da suke barin gidan, sai suka harbe shi har lahira a gaban matarsa da ’ya’yansu uku.”

“A hanyar tafiya da mutanen da suka sace, matar faston ta nemi komawa ta dauko jaririnta mai wata shida da ta bari a gidan.

“Sai mace tilo da ke cikin ’yan fashin ta tisa keyarta su koma gidan, sauran kuma suka wuce da mutanen 13 da aka sace.”

Sai dai saboda gudun kada a tafi a bar ’yar bindigar, sai ta bi saura ta bar matar faston, wadda malamar wata makarantun sakandaren gwamnati ce a Bwari.

Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kuma shiga gidan wani soja, suka nemi matarsa ta ba su bindigarsa da kakinsa.

Ya ce, “Matar ta gaya wa ’yan bindigar cewa mijinta yana bakin aiki, amma duk da haka, sun yi awon gaba da ’ya’yansa biyu.”

Ya ce, mutane 13 ne sace, amma ’yan bindigan sun yi watsi da daya daga cikin ’ya’yan faston dan shekara biyar a gefen kogi saboda ya kasa tsallaka kogin.

Daga baya ’yan banga da suka bi sawun ’yan bindigar ne suka dawo da yaron.