Yadda ’yan bindiga suka sace mutane 30 a Abuja

A daidai wannan lokacin ne kuma wasu ’yan bindingan suka sace wasu mutum bakwai a unguwar Arab road da ke Garin Kubwa da ke makwabtaka da Dei-Dei, washegari Lahadi.

Yadda ’yan bindiga suka sace mutane 30 a Abuja

Al’ummar Garin Dei-Dei da ke kusa da babban titin Kubwa zuwa Zuba a yankin Birnin arayya Abuja sun samu kansu a cikin halin rudu a sakamakon sace sama da mutum 23 a yankin da ’yan bindinga suka yi a ranar Asabar tsakanin karfe 8 zuwa 9 na dare.

A daidai wannan lokacin ne kuma wasu ’yan bindigan suka sace wasu mutum bakwai a unguwar Arab road da ke Garin Kubwa, makwabtakan Dei-Dei, washegari Lahadi.

’Yan bindigan sun saci mutum 27 ne daga wasu rukunin gidaje uku a unguwar Apiyawai da ke bayan kasuwar dabbobi wato kara ta Abuja da kuma mahauta a yankin na Dei-Dei.

Mai unguwar yankin, Alhaji Ibrahim Galadima, wanda ke matsayin jagoran kungiyar ’yan sintiri na gundumar, ya ce bayan samun labarin aukuwar lamarin ya jagoranci mambobinsa zuwa inda aka wuce da mutanen zuwa cikin jeji, inda suka dawo da mutum 7 da ’yan bindigan suka sako.

A zantawarta da Aminiya, daya daga cikin wadanda aka sakon, mai suna Amininat Mustapa, ta ce, ’yan bindigan su kutsa cikin falonta da ba su kulle da sakata ba, kasancewa lokacin misalin karfe 7 na dare ne.

“Sun haska min fitila a fuska suka kwace wayata sannan suka umarce ni na bi su tare da yarona mai shekara 2 da kuma ’ya’yana mata hudu.

“Wani mai kula da gidan makwabtanta mai suna Shmasu Armaya’u Muhammad, ya ce ’yan bindigan sun dauki mutum 8 daga gidansu ciki har da yaro dan wata 6, sai kuma matan aure sai kuma wasu matasa hudu mazauna daki guda.”

Wata matar aure mai suna Maman Gambo da ke zaman alfarma tare da sauran iyalai a wani gida bayan baro yankiunsu na Jihar Katsina da ke fama da rikici, ta ce ’yan bindigan sun kutsa zuwa cikin gidansu suka tilasta wa mai gidan wanda tsohon soja ne tare da wani abokinsa dan sanda da ya ziyarce shi, da su bi su bayan kwace wayar da ke hannunsu.

Haka kuma ’yan bindigan sun yi garkuwa da wani da ya dawo cikin motarsa tare da wata da suke tare, baya ga karin wasu da suka yi kicibis da su a yayin barin unguwar, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Cikin mutum 7 da suka saken akwai jariri mai wata shida, amma suka ci gaba da garkuwa da mahaifiyarsa, sai kuma wadanda su ka sace a kan hanya.

A yankin Arab-Road na Kubwa kuwa sun sace wata matar aure da danta mai wata 6 da ’ya’yanta uku sai kuma ’yar aikinta guda.

Haka kuma sun sace wata matar aure mai suna Zainab Hassan a yayin barin unguwar kafin daga bisani suka sako ta tare da jaririn da kuma ’yar aikinta.

A zantawarta da Aminiya, Zainab Hassaan ta ce ’yan bidigan sun daure fuskokin mazaje da suka yi garkuwa da su, a yayin da mata ke galabaice.

Ta ce yawancinsu daga yankin Dei-Dei aka sato su kamar yadda ta gano a dan zaman da ta yi da su.

Sai dai a zantawarta ta waya da wakilinmu, babbar jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ’yan sanda na Abuja S.P Josephine Adeh ta karyata faruwar lamurran biyu, inda ta bukaci al’umma da su yi watsi da bayanin.

Mahaifiyar Gwamnan Jigawa ta rasu

Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

An horar da mutum 500 dabarun adana ruwa don inganta muhalli a Gombe