Yadda ’yan bindiga suka sace mutum 49 a Katsina- Mai unguwa

Mai unguwar kauyen Wurma da ke karamar hukumar Kurfi ta Jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammed, ya bayyanawa manema labarai yadda daruruwan ‘yan bindiga suka kai hari garin, kuma suka yi awon gaba da mutum 49. Yayin da yake wa manema labarai karin haske kan lamarin, Mai garin ya ce “Yan Bindigan sun shigo da bindigogi. […]

Yadda ’yan bindiga suka sace mutum 49 a Katsina- Mai unguwa

Mai unguwar kauyen Wurma da ke karamar hukumar Kurfi ta Jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammed, ya bayyanawa manema labarai yadda daruruwan ‘yan bindiga suka kai hari garin, kuma suka yi awon gaba da mutum 49.

Yayin da yake wa manema labarai karin haske kan lamarin, Mai garin ya ce “Yan Bindigan sun shigo da bindigogi. Sai dai basu kashe kowa ba amma sun tafi da mutum 49. Amma daga baya sun sako mutum 11”, in ji shi.

Ya kara da cewa, “Muna kira ga mai girma Gwamnan Jihar Katsina da ya taimakamana da Jami’an tsaro domin magance wannan matsala, saboda a kullum muna cikin firgici.

Mai garin ya ce, aduk lokacin da ‘yan bindigan za su kawo hari suna samun labari ne ta kauyen da ke kusa dasu (Tsakiya), yana mai cewa ko wannan karonma sun samu labara ne daga mazauna kauyen, inda suka sanar dasu cewar ‘yan bindigan sun taho, kuma suna da yawa.

“A lokacin da suka zo ina bacci sai na fara jin harbin bindiga. Sun shigo har gidana suka same ni a dakina kuma suka nemi na basu kudi ko su kashe ni.” In ji Maigarin.

Wani wanda aka dauke Matarsa da Yayansa guda uku, mai suna Badamasi Wurma, ya ce “Ina tare da abokaina da misalin karfe 11:30 na dare sai muka ji ana harbi, da muka ga abin ya yi yawa sai muka gudu don tsira. Bamu sake ganin juna ba sai washegari.” In ji shi, yana mai cewa ‘yan bindigan sun haura mutum 300.