Yadda ’yan bindiga suka sheke ayarsu a karshen mako
Yadda aka sace basarake da dangin ’yan majalisa a karshen mako
Birnin Tarayya da wasu jihohi biyu ne ’yan bindiga suka ci karensu babu babbaka ta hanyar sace da mutane ciki har da iyalan masu fada a ji a karshen mako.
Ga yadda jihohin Katsina da Neja wadandan matsalar ta yi wa katutu da ma Birnin Taraya suka dandana kudarsu a hannun masu garkuwa:
– Katsina
A daren Asabar, ’yan bindiga suka dauke mata da ’ya’yan dan majalisa mai wakilatar Karamar Bakori Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Dokta Ibrahim Kurami a kauyen Kurami na karamar hukumar.
Wani shaida ya ce da misalin karfe 9:15 na dare “Yan bindiga sun kai hari gidan Hon. Ibrahim Kurami a ranar Asabar suka sace matarsa da ’ya’yansa biyu sannan suka harbe wani dan agaji wanda a halin yanzu ake jinyar sa a Babban Asibitin Bakori ”.
Kusan shekara guda ke nan da shi kansa dan majalisar aka yi garkuwa da shi, sai dai a lokacin da aka kai harin na ranar Asabar, ba ya gida.
Wata majiya ta kara da cewa ’yan bindigar sun tare hanyar Funtua zuwa Katsina na dan lokaci a yayin da suka yi awon gaba da iyalan dan majalisar.
“Bayan sallar Ishaa’i muka fara jin harbe-harbe, kafin mu farga sun sun ja daga a muhimman wurare a garin don dakile duk wani yunkurin mutane,” inji Muhammad Kurami, mazaunin garin.
Mazauna unguwar da ’yan banga a yankin sun fara bin bayan lamarin.
A Jihar Katsinar dai, ’yan bindiga sun kai hari kauyen Tafoki na Karamar Hukumar Faskari, suka sace kanwar Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Shehu Dalhatu Tafoki.
Tafoki ya ce, “’Yan bindiga sun sace kanwata, Asma’u Dalhatu bayan sun shiga garin da misalin karfe 1 na dare suka wuce kai tsaye zuwa gidan mai garin, wanda dan uwanmu ne suka sace kannena mata biyu.
“A hanya ne ’yan banga suka yi musayar wuta da su, a nan ne daya daga cikin ’yan matan ta tsere, dayar kuma sun tafi da ita,” inji shi.
Ya ce Asma’u ta kammala makarantar sakandare ana kuma dab da aurenta, kuma har yanzu masu garkuwar da ita ba su tuntubi iyalan ba.
– Abuja
A Abuja, Birin Tarayya kuma an sace wata mata mai shekara 45, Misis Oladapo Bukola, da ’ya’yanta mata biyu a unguwar Pegi da ke Karamar Hukumar Kuje.
An sace ’ya’yan nata da hada da mai shekara da wata mai shekaru 14 ne kwana biyu bayan an sace wani magidanci, Abdullahi Benda, da dansa Jibrin, mai shekara 23, a kauyen Yangoji da ke Karamar Hukumar Kwali.
Wani dan garin ya ce da misalin karfe 1:04 na safiyar Lahadi ne maharan dauke da bindigogi kirar AK-47, suka ketara katangar gidan suka balla kofofi.
Shugaban Kungiyar Ci gaban Al’ummar Pegi, Taiwo Aderibigbe, ya yi tir da garkuwa da mutanen da aka yi, ya kuma bukaci hukumomin tsaro su musu kawo dauki a yankin.
“Abin da masu garkuwa ke yi wa Pegi da Kuje abin damuwa ne kuma matakan tsaro sun yi kadan,” inji shi.
Aminiya ta gano cewa mijin matar, Fasto Gabriel Oladapo, ba ya Abuja lokacin da masu garkuwar suka kai harin.
Kakakin ’yan sanda na Abuja, ASP Daniel Ndiparya, ya ce, “Rundunar na kokarin ganin an ceto wadanda abin ya rutsa da su”.
– Neja
A wani labarin kuma, an yi garkuwa da wani basarake, Dodo na Wawa, a Gundumar Wawa ta Karamar Hukumar Borgu ta jihar Neja, Dokta Mahmoud Ahmed Aliyu.
Majiyarmu a fadarsa ta ce ’yan bindiga dauke da muggan makamai sun kutsa cikin fadar da misalin karfe tara na daren ranar Asabar suka tafi da shi.
“Sun zo kan babura sanye da kayan sojoji, kusan takwas daga cikinsu, dauke da muggan makamai. Da shi kadai suka yi garkuwa,” inji shi.
Ya ce masu garkuwar ba su tuntubi dangi ko fadar basaraken ba.
Kakakin ’yan sandan jihar Neja, ASP Wasiu Abiodun, ya ce, “An tura tawagar ’yan sanda da ’yan bangar yankin domin farautar ’yan bindigar da nufin ceto basaraken da kuma cafke bata-garin.”
Daga Sagir Kano Saleh, Tijjani Ibrahim (Katsina), Abubakar Sadiq Isah (Abuja), da Abubakar Akote (Minna)