Yadda ’yan bindiga suka yi ta mana fyade —Matan Katsina

Masu garkuwa sun yi mana fyade akai-akai suka kuma azabtar da mu

Yadda ’yan bindiga suka yi ta mana fyade —Matan Katsina

Har yanzu jama’ar kauyen Dan’Aji da ke Karamar Hukumar Faskari, Jihar Katsina na cikin kaduwa kan sace mata da kananan yara 26 da mahara suka yi musu. Mutanen kauyen da maharan suka yi wa fashi tare da kona kadarorinsu sun shaid wa Aminiya cewa za su dade ba su manta ba.

A zantawar musamman da muka yi da daya daga cikin matan, ta bayyana yadda aka ‘yan bindigar suka yi ta mata fyade wani lokaci har da duka a tsawon zamanta a wurinsu.

Karon farko ke nan da ake samun labarin abin da ya faru da matan da aka yi garkuwa da su daga bakinsu, sai dai gwamnatocin Zamfara da Katsina ba su ce uffan kan wasu abin da matan suka bayyana ba.

Ana iya tunawa jim kadan bayan bayyanar matan a Gusau ne Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya ce Gwamnatin Jihar Zamfara ya kubutar da su ba tare da biyan fansa ba.

“Mun shafe dare uku muna tafiya a kafa”, inji wata mai shekara 35 daga cikin matan da aka kubutar din.

Tafiyar da muka yi da ’yan bindiga.

Ta ce, “Idan gari ya waye sai su yi mana sansani a daji inda a nan za mu yini idan dare ta yi sai mu ci gaba da tafiya —haka muka shafe dare uku muna tafiya”.

Ta ce kusan takwas daga cikinsu — tsoffi, ’yan mata da masu juna biyu ne masu garkuwar suka ware ba sa musu fyade.

“Sauran matan kuma an yi ta musu fyade akai-akai a tsawon lokacin,” inji ta.

Gabanin abin harin ranar 13 ga watan Oktoba 2020, kauyen Dan’Aji na zaune ne cikin aminci duk da kusancinsa da jejin da ke zama mafaka ga ’yan bindigar da ke addabar iyakokin jihohin Zamfara da Katsina.

A ranar ce lamarin ya sauya inda mahar suka shiga kauyen suna kashe-kashe musamman tsoffi, fashi, lalata kadarori da cinna musu wuta, suka yi kuma awon gaba zuwa cikin jeji da mata da kananan yara da yawa.

Tafiyarmu da su a cikin jeji

Matar ta ce ba za su taba manta abin da ya faru a tafiyar da masu garkuwar suka yi da su a cikin kungurmin jeji ba.

“Duk tsawon dare tafiya muke yi a kafa har sai da muka yi gaza; ana dukanmu ana mana barazana da kisa; daga baya masu ragowar karfi a cikinmu suka rika tallafa mana muna takawa”, inji matar.

Ta ce bayan sun nausa cikin jeji sosai sai masu garkuwa da su suka bullo da sabon salon azabtarwa.

“Mu da ba a yi mana mana, duk dare sai ’yan bindigar sun buga mana ice sau goma-goma a kai, washegari kuma za su dake mu sau biyu-biyu  a baya”, kamar yadda ta bayyana.

Yadda ake ba mu abinci

Da take fadin yadda suke cin abin ci a lokacin da suke tsare, matar ta ce da farko shinkafa da wake da manja da gishiri ake ba su.

Da ta kare kuma sai aka rika ba su tuwon masara da miya.

Ta ce, “Duk idan lokacin girki ya yi za su ce mu tashi mu yi, suna cewa tun da mu mata ne dole mu girka abincin da zai ishe mu gaba daya”.

Sun yi min dukan kawo wuka —Mai juna biyu

Ita ma wata da aka kubutar wadda masu garkuwar ba su yi wa fyade ba saboda tana da juna biyu, ta ce sun yi mata dukan kawo wuka har sai da aka yi mata karin jini bayan da aka kubutar da su.

Ita ma ta ce fadawarsu a hannun masu garkuwar ita ce tashin hankali mafi tsanani da ta taba shiga a rayuwarta.

“A tsawon dare muke tafiya, tsawon yini kuma mu yi sansani. A ranar karshe mun isa wani kududdufi inda a nan muka kwana kafin washegari muka iya masaukin da suka ajiye mu na karshe”, inji mai cikin.

Ita ma wata da aka yi garkuwan da ita ta ce a ranar da ’yan bindigar suka kai harin sai da suka kashe wasu mutane, suka rika bi gida-gida suna duk abin da suka samu sannan suka ce mata da bi su.

“Kwannanmu uku muna tafiya a kafa babu takalma, wasunmu sun ji ciwo wasu kafafunsu sun yi ruwa saboda tsabar tafiya; Gaba daya kwananmu biyar muan tafiya a cikin jejin da aka yi mana sansani”, inji matar.

Ta ce a sadda suke tarin an kawo wata mata da wata budurwa daga wani kauye amma ranar da aka sake su sun bar matar da budurwar a hannun ’yan bindigar.

Yadda muka kai wa ’yan bindiga kudin fansa

Shi ma Muhammad Lawal Amadu (Liman), daya dga cikin wadanda suka wa masu garkuwar kudin fansa ya bayyana mana abin da ya faru da kuma abin da ya biyo baya.

“Maharan kusan su 500 sun far wa kauyenmu Dan’Aji ranar Talata 13 ga Oktoba, 2020 da misalin 5:32 na yamma, suka bincike kauyen, suka kashe mutum 16 sannan suka kona wurare da dama.

“Sun bi kanti-kanti suna kwasar kaya suna kuma cinna musu wuta, haka kuma suka rika bi daki-daki suna bincikewa suna konawa; an kona dakunan amare masu shekara daya zuwa biyu da aure

“Bayan haka suka sace mana mata 24 da kanana yara wasunsu ma ba su kai shekara 10 suka yi cikin jeji da su, inda suka shafe kwana 23”, inji Muhammad.

Sai dai ya ce tun ranar da aka yi garkuwa da mutanen aka sako mutum biyu daga cikinsu.

“Sun ce da suka fada wa ’yan bindigar cewa sun ’yan asalin Jihar Zamfara ne sai suka sake su suka kira mijin dayarsu a waya cewa a je a dauke su a cikin jejin.

“Mu kuma suka kira mu suna neman kudin fansa suka yi masa kashedi cewa kar mu kuskura mu ba kowa kudin sai su kuma kudin gaba daya za a kai musu cikin jejin”.

Mun bida miliyan N6.6 kudin fansa

Muhammad Lawal Amadu ya shaida wa Aminiya cewa da farko sun kai wan ’yan bindigar Naira miliyan 2.1, wanda suka ce musu su ajiye a karkashin wata bishiya.

“Bayan mun ajiye kudin mun juya sai suka kira mu cewa kudin ya yi kadan a saki mutanenmu.

“Sun nemi karin N400,000 domin kudin ya ciki miliyan N2.5, hakan nan muka yi ta fadi tashi muka samo cikon amma suka kara cewa sun yi kadan sai da muka nemo karin miliyan N1.7 muka kara kai musu”, inji Muhammad.

Ya ci gaba da cewa bayan harin da mako biyu, ’yan binidigar sun sake dawowa kauyen suka yi awon gaba da karin ’yan mata biyar cikinsu har da wata da wata da aka yi wa tiyata kwana biyar kafin sake dawowar masu garkuwar.

“Mata mahaifinta ta roke su daga baya suka sake ta da suka tabbatar da rashin lafiyartsa – wannan ne ya sa yawan mata da yaran da aka yi garkuwa da su ya karu zuwa 26.

“Bayan garkuwar da suka yi karo na biyu kuma sai muka fara sabon tattaunawa da su, da haka ne jumullar kudin fansar da muka ba su ya kai miliyan N6.6.

“Daga karshe da suka sake su sai aka gayyace mu zuwa Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara aka ce mana cewa an sako ’ya’anmu ne saboda gwamantin jihar ta sa baki.

“Ba mu yi musu magana ba saboda ba damuwarmu ba ke nan, abin da ya fi damun mu shi ne ’yancin mutanenmu.

“Amma har su da aka yi garkuwar da su sai da aka sa suka ce kwanansu biyar a hannun masu garkuwar alhali ba haka ba ne”, inji shi.

Game da takawar kwana uku a jeji wurin kai wa ’yan bindiga kudin fansa, Muhammadu ya ce, “ba kwanan mu ukun a jere a jejin ba, sau uku dai muna kai musu kudin fansa a yayin da ake tattauanawa da su”.

Ya ce sukan shafe tsawon yini suna tafiya a kafa zuwa inda za a ce musu su ajiye kudin, kuma idan suka juya so suka koma ba su ke isa gida ba sai cikin tsakar dare.

Ya ce akwai matukar tashin hankali tafiya a cikin jejin inda ya ce ’yan bindigar na da mutanensu da ke lura da kai-komon masu kawo kudi.

“Muna ta waya da su tsawon lokacin da muke tafiya a cikin jejin kuma muna haduwa da mutanensu a kan hanya da ke gaya mana cewa muddin muka sake muka yi wata kumbiya-kumbiya mutanenmu za su halaka”, a cewarsa.

‘’Ya’yana hudu da cikin wadanda da aka sace

Abdulkadir Musa Dan’Aji Abdulkadir Musa Dan’Aji na daga cikin ’yan kauyen wanda ’yan bindigaru suka dauke hudu daga cikin ’ya’yansa mata

Ya ce sai da ya sayar da duk abin da ya mallaka kafin ya samu kudin da ya bayar aka sako ’ya’yan nasa.

“Sai da na sayar da amfanin gona na tun kafin lokacin girbi da sauran kadarorina; sai da sauran ’yan uwana na dangi da iyayen matata suka taya ni neman kudi”, iniji shi.

Ya ce bayan sun biya kudin fansar sai da aka sa su biya kudin motar kawo ’ya’yan nasu.

“Sun sa mu biya N1,500 na dauko kowacce daga cikin ’ya’yan namu a kan babur daga cikin jeji kuma muka biya.

“Mun yi ta jira amma ba mu duriyarsu ba sai daga baya muka ji cewa suna hannun Gwamnatin Jihar Zamfara.

“Sun gaya mana cewa an yi musu duka an azabtar da su da yunwa an kuma yi musu fyade.

“Dukkansu an yi musu fyade kuma sun ce a fili suke barci a cikin jejin”, inji shi.

A bangaren, Bala Musa Dan’aji ya ce ya sayar da gonarsa, da gyadarsa da masarar don ya samu ya biya kudi a sako ’yarsa mai shekara 12 wadda ita ma ta sha azabar, har da fyade a hannun masu garkuwar.

Shi ma wani dan kauyen da aka yi garkuwa da matarsa ya ce sai da ya sayar da duk abin da ya mallaka ya kuma yi rancen kudi.

“An yi musu fyade da duka kuma sun gaya mana cewa a kasa suke kwana a lokacin da suke hannun masu garkuwar.

Muna bukatar taimako

Dagacin Dan’Aji, Malam Ammani ya yi kira ga hukumomi da su taimaka su samar da matakan tsaro a kauyen domin kare ragowar amfanin gonarsu.

Ya ce rashin matakan tsaro da kuma lalacewar hanyar zuwa kauyen na daga cikin manya damuwarsu.

“Hanyar Yankara-Dan’Aji-Yan Malamai ta zama tarkon mutuwa inda a nan masu garkuwa ke yin kwato suna kai wa masu bin hanyar hari”, inji shi.

Aminiya ta ruwaito cewa Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Zamfara Muhammad Dauran ne ya mayar da matan da aka kubutar zuwa Katsina.

Da yake hannanta su, ya shaida wa Gwamna Aminu Masari cewa an yi garkuwa da matan ne a kan iyakan jihohin Katsina na Zamfara.

“Za mu inganta tattaunawa da masu garkuwawr domin mun ga alfanon hakan wurin samar da tsaro a jiharmu, saboda haka yana da kyau a ci gaba da tattauanwa da su,” he said.

A jawabinsa, Masari, ya jaddada alkawarin gwamnatocin jihohin biyu na tabbatar da dawowan aminci.