Yadda ’yan Boko Haram suka sace matar mataimakin Firayiministan Kamaru

’Yan kungiyar Boko Haram sun dade da fara yunkurin kutsawa kasar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya, amma sai a makon jiya ne suka kai ga taba daya daga cikin jami’an gwamnati kasar. A ranar Lahadi ne rahotonni suka bayyana cewa wasu mutane masu dauke da makamai da ake kyautata zaton cewa ’yan Boko Haram ne […]

Yadda ’yan Boko Haram suka sace matar mataimakin Firayiministan Kamaru
Yadda ’yan Boko Haram suka sace matar mataimakin Firayiministan Kamaru

’Yan kungiyar Boko Haram sun dade da fara yunkurin kutsawa kasar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya, amma sai a makon jiya ne suka kai ga taba daya daga cikin jami’an gwamnati kasar.
A ranar Lahadi ne rahotonni suka bayyana cewa wasu mutane masu dauke da makamai da ake kyautata zaton cewa ’yan Boko Haram ne suka kai farmaki gidan Mataimakin Firaministan Kamaru Amadou Ali, a garin Kolofata mai iyaka da Najeriya.  Inda suka yi awon gaba da uwar gidansa da kuma wasu daga cikin ’ya’yansa.
Har ila yau, ’yan bindigar sun sace basaraken garin. Sai dai kuma rahotonni sun bayyana cewa an yi ta musayar harbe-harbe a tsakanin jami’an tsaro da kuma mutanen, sakamakon dirar mikiyar da maharan suka yi wa garin.
Kakakin Gwamnati Minista Issa Tchiroma Bakary ya tabbatar da wannan labarin.
Faruwar wannan al’amarin ya haifar da wani yanayi na firgici ga jama’ar  lardin arewa mai nisa inda runtsawa ta gagari mutanen garuruwan  Balgaram da Hile Halifa da Fotokol da kuma Amchide. Ana cikin wannan zaman zullumin ne, sai ga wasu bayanai suna cewa, jami’an tsaro sun samu nasarar kubutar da uwar gidan mataimakin firaministan da basaraken da kuma sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.
Sai dai kuma tuni jama’a suka fara sa shakku game da dangantakar da ka iya kasancewa tsakanin jami’an gwamnati da kuma jami’an tsaro hadi da ’yan kungiyar Boko Haram. Daga bisani kuma sai wani rudani ya fara kunno kai game da labarin kubutar da mai dakin mataimakin firaministan da aka ce sojoji sun yi. Duk da cewa kuma kakakin Gwamnatin, bai musanta labarin farko da ya nuna cewa an kubutar da daukacin jama’an da ’yan kungiyar Boko Haram suka sace a ranar Lahadi ba, amma kuma har idan bai gayyaci kafofin yada labarai ba, wannan ya nuna cewa kenan babu wani abinda zai bayyana.  
Wasu bayanai kuma sun nuna cewa Mataimakin Firaminista Amadou Ali wanda a lokacin kai hari ya ke bulaguro a birnin Maroua, dalilin da ya sa kenan wannan harin bai rutsa da shi ba. Sai dai kuma wani bayani da ba na hukuma ba ne ya ce an so kai hari a inda yake a lokacin, sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar murkushe wannan yunkuri.
Dangane da haka ne washegari Litinin wadda take ranar bukukuwan karamar Salla ce a fadin kasar, daukacin huduba da kuma wasu jawabai da limamai da wasu jami’an gwamnati suka yi sukai Allah-wadai da irin ayyukan da suka ce kungiyar Boko Haram take haddasawa, wadanda suka saba wa addinin Islama.