Yadda ’yan fim suka nuna soyayyar da masoyansu ke yi musu a Instagram
A kwanakin nan ne fitattun jaruman fina-finan Hausa da suka hada da Ali Nuhu da Adam A. Zango da Nafisa Abdullahi da mawaki Nura M. Inuwa suka baje-kolin hotuna da kuma bidiyo a shafin sada zumunci na Instagram, inda suka bayyana yadda masoyansu suke nuna musu tsananin soyayya.Jarumi Ali Nuhu ne ya fara sanya wasikar […]
A kwanakin nan ne fitattun jaruman fina-finan Hausa da suka hada da Ali Nuhu da Adam A. Zango da Nafisa Abdullahi da mawaki Nura M. Inuwa suka baje-kolin hotuna da kuma bidiyo a shafin sada zumunci na Instagram, inda suka bayyana yadda masoyansu suke nuna musu tsananin soyayya.
Jarumi Ali Nuhu ne ya fara sanya wasikar da wata yarinya ’yar shekara 9 mai suna Husna ta rubuto masa. Yarinya ta rubuta wasikar da Turanci ne, inda ta ce: Zuwa ga Ali Nuhu, sunana Husna Sani ’yar shekara 9 daga unguwar Hotoro Tsamiyar Boka, Kano. Ina so in sanar da kai cewa dukkan ’yan uwana mata suna son fina-finanka, ni ma ina son fim dinka, haka ma mahaifiyata. Kawu, ina so in gan ka, zan ji dadi idan hakan ta tabbata. Taka Husna Sani.”
Jarumin ya bayyana tsananin farin cikinsa, inda ya bayyana shi ma yana shaukin ganin wannan masoyiyar tasa ’yar shekara 9.
Bayan wadansu kwanaki ne kuma, sai jarumin ya sanya hotonsa da Husna, inda ya bayyana Allah Ya kaddara haduwarsa da ita.
Daga nan ne fitaccen jarumi Adam A. Zango ya sanya bidiyon yadda wata mata mai suna Maryam take kukan murna a lokacin da ta gan shi. Jarumin ya sanya bidiyon ne a shafin Instagram, a lokacin yake cikin motar da ke tsaye sai ga wata mata nan sanye da hijabi ruwan omo, inda ganinsa ke da wuya ta barke da kukan murna. An nuna shi a cikin motar da ke tsaye.
A cikin kuka ne ta ce: “Allah Ka rage min son ka a raina. Ni ba so nake in aure ka ba, kawai Allah ne Ya hada jinina da kai.” Daga nan ta bukaci jarumin ya ba ta lambarsa, kuma ya ba ta, inda shi ma ya karbi tata lambar wayar.
Sannan a karkashin bidiyon ya rubuta bayani kamar haka: “Allah Sarki! Ba ta boye irin farin cikin da ya mamaye ta a lokacin da ta gan ni ba. Wadansu ka iya cewa hakan shirme ne ko kauyanci ne, amma a ganina hakan cikakkiyar kauna ce. Na gode wa Allah da Ya ba ni irin wadannan masoya.”
Haka jarumin ya sanya hoton bidiyo a lokacin da ya ziyarci wani masoyinsa mai suna A. Zango Mai Kayan Miya a Kano, jarumin ya tsaya a cikin motarsa, inda suka gaisa da masoyin nasa, sannan suka yi musayar lamba, a lokaci guda suka dauki hoto. A jikin bidiyon an nuna allon tallar masoyin jarumin, inda aka rubuta A. Zango Mai Kayan Miya.
A karkashin bidiyo ne jarumin ya rubuta: “Ina girmama wanda ba ya kyama ta, wanda yake ado da sunana a ko’ina a fadin duniya.”
Haka ne ya sanya jaruma Nafisa Abdullahi ta sanya wani bidiyo, inda dandazon yara maza da mata suke bin ta, a kusa da ita wani matashi da ke rike da littafin yadda aka tsara labarin fim (script), sannan wani mutum sanye da farin yadi da farar hula rike da bulala yana korar yaran da ke bin jarumar kamar yadda kudaje ke bin kwallon mangwaro, amma ba su daina bin ta ba. A gefen jarumar wata yarinya ce sanye da atamfa ruwan madara tana ta yi mata magana, amma ba ta saurare ta ba. Yaran suka rika gudu suna bin ta a lokaci guda suna kiranta da ’Ya Daga Allah.
A karkashin bidiyon ne jarumar ta rubuta: “daukaka da farin jini Allah ne Yake ba mutum. Allah ne Ya ba ni farin jinin jama’a. Ina gode wa masoyana. Allah Ya bar mu tare.”
Daga nan mawaki Nura M. Inuwa ya sanya hoton hannun wata budurwa da ta rubuta: “I Lobe You Nura M Inuwa,” Wato Ina sonka Nura M Inuwa. Ta rubuta hakan ne da biro amma yanayin yadda aka tsara rubutu da kuma adon da aka yi masa, hakan zai ja hankalin duk wanda ya gani.
A yanzu dai ’yan Fim suna ta sanya hotunan yadda masoyansu ke nuna musu kauna.