Yadda ’yan gida daya ke kamuwa da shanyewar jiki bayan sun shekara 18

Daya bayan daya, shida daga cikin ’ya’ya takwas na wani iyali sun hadu da shanyewar barayin jiki a wani yanayi iri guda. Yanzu hankalinsu ya tashi kan ko hakan zai shafi sauran ’yan uwansu:   Wata cuta ‘mai ban al’ajabi’ ta jawo shanyewar barayin jiki ga shida daga cikin ’ya’ya takwas na wani iyali da […]

Yadda ’yan gida daya ke kamuwa da shanyewar jiki bayan sun shekara 18

Daya bayan daya, shida daga cikin ’ya’ya takwas na wani iyali sun hadu da shanyewar barayin jiki a wani yanayi iri guda. Yanzu hankalinsu ya tashi kan ko hakan zai shafi sauran ’yan uwansu:

 

Wata cuta ‘mai ban al’ajabi’ ta jawo shanyewar barayin jiki ga shida daga cikin ’ya’ya takwas na wani iyali da ke kauyen Gitata a hanyar Keffi zuwa Kachiya a karamar Hukumar Karu da ke Jihar Nasarawa.

Wakilinmu wanda ya ziyarci iyalan ya iske wadanda lamarin ya shafa wadanda marayu ne da suke fama da cutar hade da kuncin talauci ba tare da samun tallafi ba.

A cewar danlami danladi mai shekara 38, mahaifinsu ya rasu ne a 1990, yayin da mahaifiyarsu ta rasu bara, kuma dukansu biyun ba su da wata nakasa a jikinsu, don haka suke mamakin abin da yake shafarsu.

Asabe, wadda ita ce babbar ’ya a iyalin ta yi aure tare da haihuwar’ya’ya biyar, sai Pius na ukunsu da Maikasuwa na hudu da danjuma na biyar da kuma Cecelia ta shida, dukansu sun hadu da shanyewar jikin.

Da yake bayyana halin da suke ciki, danlami ya ce bai lura da wata alama ta rashin lafiya ba daga farko, amma a hankali sai ya lura yana rasa karfi lokacin da yake gudu ko yake daukar abubuwa masu nauyi.

Ya ce, bai hadu da ko zazzabi ko zogi ba, amma ya tuno shanyewar jikin ta faro ne a shekarar 2001, kuma bayan ya je asibitoci da dama ba abin da aka gano da ke haddasa hakan. Kuma ya ce talauci da maraici sun hana shi ya kara zuwa asibiti na gaba domin kula da lafiyarsa.

Kuma ba tare da ya karaya da wannan kalubale ba, sai ya kama harkar bayar da hayar wayoyin hannu don kula da kannensa daga baya ya samu kwantaina inda ya fara cajin wayoyi da kuma gyaransu.

A cewarsa lafiyarsa ta tabarbare ne a bara ta yadda ba zai iya ci gaba da harkokin kasuwancin ko sana’a ba, inda ya koma zaman gida.

danlami ya shaida wa Aminiya cewa, addu’a kawai za su iya yi don samun waraka daga wannan cuta mai ban mamaki. Ya ce biyu daga cikin kannensa wadanda teloli ne da suke taimaka masa da kudi, su ma sun hadu da shanyewar barayin jikin.

Sai ya roki Gwamnatin Jihar Nasarawa ta taimaka musu da magunguna da jinyarsu tare da kula da sauran kannensu biyu da ba su kamu da cutar ba.

Joshua mai shekara 15 kuma autan iyalin ya bayyana wa Aminiya tsoronsa kan abin da yake faruwa da iyalan nasu. dalibin aji biyu a karamar sakandare ya ce: “Ina cike da tsoro, domin ba na son in kamu da wannan cuta, saboda mu ne muke taimakawa da ayyukan gida kamar dafa abinci da debo ruwa da sauran ayyukan gida.”

Ita kuma Hannatu mai shekara 19 wadda cutar ba ta shafa ba, cewa ta yi duk da ba ta hadu da wata alama ta cutar ba, amma tana jin tsoro don haka tana fata gwamnati za ta kai musu dauki da magungunan da suka dace.

Pius, wanda yake da shekara 35, kuma mutum na biyu da cutar shanyewar jikin ta shafa ya shaida wa wakilinmu cewa: “Abin ya fara ne cikin ban mamaki wata rana. Na fara jin kasala. Ba na jin zazzabi ko wani zogi, amma na rasa karfi. Kafin ka ce kwabo na wayi gari da shanyewar kafata. Hakan ya faru ne a shekarar 2011 lokacin da cutar ta mamaye ni. Ba na iya tafiya da kaina ba tun daga lokacin.”

Ya ce rayuwa ta kasance mai wahala sakamakon matsalar rashin lafiyar kuma lamarin ya dada tsanani tun lokacin da shanyewar ta hada da hannuwansa. 

Asabe kuwa cewa ta yi ba za ta iya tuna lokacin da lamarin ya fara shafarta ba, amma ta tabbatar da abin da ’yan uwanta suka fadi na jin kasala a jiki kuma jikinta ya yi mata nauyi amma sai ta dauka saboda gajiya ce.  

Ta tunato cewa a rana ta farko da cutar ta kama ta tana gona ne kuma a kafarta ta hagu sai da aka taimaka mata kafin ta dawo gida.

 “Babban abin da ke damunmu a yanzu shi ne halin rashin lafiyar, domin wannan cuta ta nakasa iyalan. Muna rokon gwamnati da daidaikun mutane su kawo mana dauki wajen samar mana da magani ko daukar nauyin jinyarmu ta yadda rayuwarmu za ta dawo kamar yadda take,” inji ta.

Shi kuwa danjuma mai shekara 26, wanda yake amfani da keken guragu ya shaida wa Aminiya cewa, Allah ne kawai Ya san abin da ya kawo wannan cuta “mai ban al’ajabi” da ta auka wa iyalan.

danjuma ya ce, “Babban abin da muke tsoro a yanzu shi ne sauran iyalan gidan biyu da cutar ba ta kama ba, su ne wadanda suke daukar dawainiyar iyalan. Suna taimaka wa wadanda suke fama da nasakar. Suna daukar danlami zuwa ba-haya su yi sauran ayyuka.”

 “A yanzu ni ina gudanar da shagon cajin wayoyi ne. Kuma suna tura ni a keken guraguna zuwa shagona, sannan in fada shagon. Ba na iya motsawa ko nan da can sai ya zama dole, kuma duk lokacin da nake son gusawa  wani wuri, sai na kira su sun zo sun taimaka min, kuma bayan kammala aiki a wunin, sai in kira su su zo su mai da ni gida. To wadannan sauran yara biyu su ne madogaran iyalan. Don haka muna rokon gwamnati ta hanzarta kawo musu tallafi a fannin kiwon lafiya ta yadda za a kare su daga kamuwa da wannan bakuwar cutar” inji shi.

Lokacin da aka tuntubi wani likita a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Keffi, wanda ya bukaci a sakaye sunansa, saboda ba a ba shi izinin yin magana ba, bayan ya saurari alamun cutar, ya ce ba zai iya cewa komai ba har sai an gudanar da binciken tarihin lafiyarsu da kuma gudanar da bincike kan wadanda cutar ta shafa.

Ya ce, hanya mafi dacewa ita ce majinyatan su tuntubi cibiyoyin lafiya tun daga matakin cibiyoyin lafiya na karkara, inda bayan an fara bincike kan tarihin cutar da gudanar da gwaje-gwajen da suka kamata, za a tura su wata babbar cibiyar kiwon lafiya domin dada gudanar da gwaje-gwaje tare da kara ba su magunguna da jinyarsu.