Yadda ’yan gudun hijira ke rayuwa ta cin ganyen albasa

Jihar Bauchi jiha ce da ta karbi bakuncin ’yan gudun hijira daga sassa daban-daban na kasar nan. Kauyen Rindabe na daya daga cikin wuraren da ’yan gudun hijira suke zaune a Bauchi, inda matsalar yunwa da fatara suka gallabe su har yunwa ta sa suke cin ganyen albasa, lamarin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta karyata. […]

Yadda ’yan gudun hijira ke rayuwa ta cin ganyen albasa

Makarantar Firamare ta garin Rafin Gora da ba ta tava yaye dalibi ba a shekara 40

Jihar Bauchi jiha ce da ta karbi bakuncin ’yan gudun hijira daga sassa daban-daban na kasar nan.

Kauyen Rindabe na daya daga cikin wuraren da ’yan gudun hijira suke zaune a Bauchi, inda matsalar yunwa da fatara suka gallabe su har yunwa ta sa suke cin ganyen albasa, lamarin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta karyata.

Idan mutum ya isa garin zai ga yara ’yan kasa da shekara uku zuwa biyar suna cin ganyen albasa da na itatuwa saboda yunwa da ta gallabi matsugunin wadansu baki ’yan kabilar Shuwa Arab da ke zaune a Rindaben kimanin kilomita biyu daga kauyen Inkil da ke Karamar Hukumar Bauchi.

Mazauna matsugunin sun ce sun kai sama da mutum 200 kuma sun fito ne daga Jihar Borno daga kananan hukumomin Marte da Mafa da kuma Jere.

Lokacin da wakilin Aminiya ya isa mazaunin ya same su a gindin wata itaciya akasarinsu sun kasa kayan miya yayin da wani yaro kuma yake cin ganyen albasa.

Wadansu daga cikin mata iyayen yaran  da ke wurin da suka ba da sunansu da Ajidda Ahmad da A’ishatu Musa sun ce a yanzu ba su da wani abinci sai ganyen albasa saboda ita albasa tana da albarka tana da dadi kuma tana maganin abubuwa da yawa.

Suka ce ba su da bayan gida sai dai su je daji su yi bahaya kuma watakila ruwan da suka wanke bahayan ya koma cikin koramun da suke shan ruwa.

Matan sun ce bara kimanin mata masu juna 20 ne suka haihu a wajen kuma babu kiwon lafiya da za su iya kare kansu daga kamuwa daga cututtuka.

Mazauna wwurin sun ce suna fama da matsalar yunwa, fatara da rashin sutura da rashin aikin yi ga uwa uba ba isashshen abinci kuma yanzu rayuwa za ta kara wahala a gare su ganin ga damina kuma wadansu cikin bukkokin da suke zaune ba za su iya tare ruwan sama yadda ya kamata ba.

Sun ce sun yanke kauna cewa rayuwa za ta iya inganta a gare su.

Darakta a Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Bauchi, Alhaji Kabiru Yusuf Kobi ya musanta zargin cewa mutanen ba su da abinci sai ganyen albasa, inda ya ce, “Gaskiya a Jihar Bauchi ba mu da wani takamaiman matsuguni da za a ce na ’yan gudun hijira ne, domin dukkan ’yan gudun hijirarmu mun riga mun mai da wasu garuruwansu wadansu kuma sun zama ’yan gari.”

Daraktan ya ce lokacin da suka zo sun shaida musu cewa ba su da inda za su sauke su domin ba su da sannsanin ’yan gudun hijira.

Kabiru Kobi ya ce a Jihar Bauchi aka lissafa sananonin ’yan gudun hijira da ba a yi wa rajista ba sama da 2000, amma wadannan mutane an tura su aiki ne a wata gona sai kuma suka yanke shawarar zama a wurin, kuma Jihar Bauchi ta karbe su cikin karamci don ba su da wurin da za su koma, kuma tana shirye-shiryen zaunar da su cikin al’ummar jihar.

Ya ce gwamnati na shirin tallafa musu kuma ana samun tallafi daga kungiyoyi ciki har da shirin Shugaban Kasa na Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI).

Shugaban ’yan gudun hijira na Jihar Bauchi Buba Musa Shehu ya ce Hukumar NEMA daga Gombe sun zo sun ziyarce su, sun duba yanayin da suke ciki domin tallafa musu. Ya musanta cewa ganyen albasa suke ci don su rayu, inda ya ce suna cikin wadanda ake ba su tallafi da agajin kayan abinci.