Yadda ’yan gudun hijirar Borno ke rayuwar ƙunci a Ibadan

Tafiyar tamu ta mata zalla da ƙananan yara akwai ban-tausayi da tsautsayi.

Yadda ’yan gudun hijirar Borno ke rayuwar ƙunci a Ibadan

Wasu ’yan asalin Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno da suke gudun hijira a Ibadan babban birnin Jihar Oyo, sun ce sun shafe shekara 10 suna zaune a cikin ƙuncin rayuwa a cikin kangwaye da ruɓaɓɓun gidaje da suke biyan ɗimbin kuɗin haya ba tare da samun taimakon gwamnatocin tarayya da jihohin Borno da Oyo ba.

A farkon makon nan ne mutanen suka yi dafifi a babban ofishin Ƙungiyar Matan Arewa a Unguwar Sabo a birnin Ibadan inda suka miƙa kukansu ga Shugabar Ƙungiyar Hajiya A’ishat Isma’il.

Aminiya ta zanta da wasu daga cikinsu da suka haɗa da A’isha Abdullahi mai kimanin shekara 40 da ke ɗauke da goyon yaro, wacce ta ce sun guje wa bala’in Boko Haram a garuruwan Ƙaramar Hukumar Gwoza inda suka fito da ƙyar suka isa garin Ibadan.

“Bayan mazanmu sun bar mu a can cikin damuwa da rashin sanin halin da muke ciki, sai muka yanke shawarar biyo su.

“Tafiyar tamu ta mata zalla da ƙananan yara akwai ban-tausayi da tsautsayi, amma muka fito babu komai a hannunmu inda muka yi zagaye ta ƙasar Kamaru.

“Mun yi doguwar tafiya a ƙasa babu takalma a ƙafa kafin mu samu taimakon wasu masu motoci da babura wajen fito da mu daga sassan da ’yan Boko Haram suka mamaye a yankin Gwoza zuwa ƙasar Kamaru,” in ji ta.

Kuma ta ce wasu masu ɗauke da juna biyu har da ita, sun haihu a kan hanya, wasu kuma Allah Ya karɓi rayukansu a yayin da suka bar waɗanda suka kasa ci-gaba da tafiya a cikin dazuka har zuwa yau ba su sani ba ko suna raye.

Ta ce babu maganar komawa gida gare su don sun gwammace su sha wahala tare da mazanmu a Ibadan maimakon komawa gida.

Wani mai suna Muhammed Abdullahi ya ce yanzu haka babu kowa a garuruwansu da suka baro sai dai tsuntsaye da ƙwari.

 “Amma duk da haka muna sha’awar komawa ƙauyukanmu idan komai ya gyaru kasancewar ƙuncin da muke ciki a Ibadan,” in ji shi.

“Yawanmu maza da mata da yara da muke gudun hijira a Ibadan ya haura 400. Muna zaune tare da iyalinmu ne cikin kangaye da ruɓaɓɓun gidaje, inda muke biyan ɗimbin kuɗaɗen haya.

Sana’ar acaɓa da leburanci da gadi muke yi mu samu ɗan abin da muke ci da kuma biyan buƙatun yau da kullum,” in ji shi.

Wani magidanci mai suna Mustapha Isa, ya yi wa Aminiya bayani cikin damuwa da hawaye yana cewa cikin shekara 10 da suke gudun hijira a Ibadan cikin ƙuncin rayuwa ba su taɓa samun gudunmawa daga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohin Borno da Oyo ko ƙananan hukumominsu ba.

“Don haka muna so Gwamna Babagana Umara Zulum ya taimaka ya yi wa takwaransa Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo magana a kan halin da muka samu kanmu a ciki domin wataƙila ba su san da zamanmu ba.

 Idan mahukunta suka shawo kan matsalar tsaro a yankunanmu, za mu zauna cikin shirin jiran lokacin da za su kwashe mu su mayar da mu gida,” in ji shi.

Haka ma A’isha Abdulahi ta yi irin wannan kuka tan cewa, “Tun da muka iso Ibadan ba mu taɓa samun taimakon gwamnatocin Tarayya da jihohin Borno da Oyo ba.

 Muna yin kira ga dattijon arziki Sanata Ali Indume da ke wakiltar mazaɓarmu ta Gwoza a Majalisar Dattawa ya taimaka ya zo ya gane wa idanunsa ko ya aiko wakilai su ga halin ƙuncin da muke ciki a Ibadan,” in ji ta.

Da take yi wa Aminiya ƙarin haske a kan matsalar ’yan gudun hijira, Shugabar Ƙungiyar Mata ’Yan Arewa a jihohin Kudu maso Yamma, Hajiya A’ishat Isma’il cewa ta yi, sun fara gano matsalar ’yan gudun hijirar ne lokacin da ɗaya daga cikin matan ta kawo ƙarar mijinta.

Ta ce sun sasanta ma’auratan tare da bin su zuwa matsugunin da suka don gane wa idanunsu mummunar rayuwar da suke ciki tare da Yarbawan da suke Takura musu a kan ɗimbin kuɗaɗen hayar ruɓaɓɓun gidajen da suka karɓa a hannunsu.

“Wani lokaci a baya, ɗaya daga cikin waɗannan gidaje ya rufta ya yi sanadin mutuwar yara biyar.

Don haka a madadin ƙungiyarmu ta Matan Arewa a wannan sashe ina kira ga dukkan shugabannin Jihar Borno musamman Gwamna Babagana Umara Zulum da Sanata Ali Ndume su hanzarta ɗaukar matakin tsame waɗannan bayin Allah daga halin damuwa da suke ciki domin ƙungiyarmu ba za ta iya ba,” in ji ta.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja