Yadda ’yan gudun hijirar Gamboru ke rayuwa a Kamaru
Dubban ’yan gudun hijiran garin Gamboru Ngala da suka fito daga jihar Barno da ke Tarayyar Najeriya saboda rikicin Boko Haram, a yanzu suna rayuwa ne a cikin wani mawuyacin hali a kasar Kamaru. Akasarin ’yan gudun hijiran mata ne da kananan yara wadanda suke rayuwa a waje, wasu kuma a karkashin bishiyoyi. Kodayake wadanda […]
Dubban ’yan gudun hijiran garin Gamboru Ngala da suka fito daga jihar Barno da ke Tarayyar Najeriya saboda rikicin Boko Haram, a yanzu suna rayuwa ne a cikin wani mawuyacin hali a kasar Kamaru.
Akasarin ’yan gudun hijiran mata ne da kananan yara wadanda suke rayuwa a waje, wasu kuma a karkashin bishiyoyi. Kodayake wadanda sukai sa’a suna zama ne tare da wasu jama’a da suka sani, inda suke rayuwa tare da su a cikin gidajensu.
Rahotanni daga garin Fotokol na Kamaru, mai makwabtaka da Gamboru Ngala, na cewa ana iya iske mutane a wani lokacin fiye da 100 a cikin gida guda. A wani lokacin ma adadin na dara haka.
’Yan gudun hijiran sun kaurace wa muhallansu ne biyo bayan karbe iko da garuruwansu da ’yan kungiyar Boko Haram suka yi, a farkon watan jiya. Wasu jama’a sun shaida wa Aminiya cewa, sun fito daga gidajensu ne ba tare da sun dauki komai ba. Saboda haka kwanciyar da suke yi a waje ba su da wani abin kare lafiyarsu daga sanyin damina kuma wannan ya sa yaransu fama da mura da kuma zazzabin cizon sauro . Wasu kuma da ba su samu matsuguni a cikin garin ba, sun shiga cikin daji suna zama a cikin duhu, da ruwan sama hadi da laka. Wadanda kuma suke da karfinsu sukan yi tafiya da kafa ta tsawon Kilomita fiye da 120 zuwa garin Kousseri cikin hatsari, saboda suna tsoron kada ’yan Boko Haram su shiga garin Fotokol su hallakasu. Bayanai sun bayyana cewa, “duk mutumin da ya shiga hannunsu sukan yi masa yankan rago ne”. Hakannan ma mace har idan ba ta manyanta ba sosai, suna “gallaza mata har ya kai ga harbi a wasu lokuta.”
Wadanda suke samun kubuta daga harinsu su ne mata dattawa, wadanda suke barinsu shiga Gamboru domin su dauko abin amfaninsu da suka bari.
A nata bangaren, Gwamnatin Jihar Barno ta aika wa ’yan gudun hijiran kayan abinci domin taimaka musu. Kayan tallafin sun kunshi shinkafa da mai da kuma gishiri. Kuma sun isa garin Fotokol ne a cikin manyan motoci kusan guda biyar. Sai dai duk da raba kayayyakin agajin da aka yi daukacin jama’a bai kai garesu ba. A yayin da jami’an da suke kula da raba wadannan kayayyakin kamar Alhaji Bakari yake cewa “jama’a ne suka yi yawa suka kasa hakuri a mika musu kayan taimakon a hannunsu, suka yi dafifi akai suna ta wawa,” inji shi
Wasu jama’a cewa suka yi “ana rabon ne da son zuciya, ana bai wa wasu kaso da dama, wasu kuma a ba su abinda bai taka kara ya karya ba, wasu kuma ana hanasu kayayyakin ne ma kwata-kwata” inji su.
Daga bangaren gwamnatin Kamaru ita ma ta tallafa wa masu raba kayan agajin da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa komai ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana. Hakazalika, ta fara aikin kwasar ’yan gudun hijira zuwa wani sansanin da ta tanada a garin Minawaou da ke lardin Arewa-mai-Nisa.
Sai dai a can ma akwai raguwar aikin da za a yi domin samar ma wadannan ’yan gudun hijira abubuwan more rayuwa, kamar su ruwan sha da kuma muhalli da sake kafa wasu tantuna. A yanzu haka abinda ake jin wa tsoro shi ne bullar annobar cutar Kwalara, ganin cewa a duk shekara wannan yankin na fama da annobar a lokacin damuna.