Yadda ’yan IPOB suka kashe makiyayi da shanu 30
Wadansu na ganin kisan bai rasa nasaba da gargadin kungiyar IPOB kan cin naman shanu.
Kisan baya-bayan nan da wadansu da ake zargin ’yan Kungiyar Neman Kafa Kasar Biyafara (IPOB) ne, suka yi wa wani makiyayi a Jihar Enugu ya jefa iyalansa da maigidansa dan kabilar Ibo da wadanda suka san shi a cikin bakin ciki.
Makiyayin mai suna Mohammadu Alarabe wanda aka fi sani da Ogbodo, ya shafe sama da shekara 20 yana kiwon shanun wani fitaccen dan kabilar Ibo kafin a kashe shi a ranar Laraba, 19 ga Janairun bana.
- Gyaran jikin da amarya ya kamata ta yi a jajiberin ranar bikinta
- Za a fara daure ma’aikatan lafiya da na lantarkin da suka shiga yajin aiki shekara 5 a Sri Lanka
Maharan sun kuma kashe wasu daga cikin shanun ubangidan Alarabe, mai, Cif Peter Chukwuani Onyeabor, wani shahararren dillalin shanu a Jihar Enugu, wanda ya gaji sana’ar daga mahaifinsa. Cif Onyeabor fitaccen mai sayar da shanu ne a garin Ugbowka da ke Karamar Hukumar Nkanu ta Gabas da ke jihar.
Ana kyautata zaton dangin Onyeabor ne suka fi shahara a sana’ar shanu a yankin sama da shekara 200.
Kodayake Onyeabor ya bayyana maharan a matsayin ’yan bindiga, amma jami’an Kungiyar ESN sun ce suna daukar mataki kan reshen haramtacciyar Kungiyar IPOB da ta sha kai wa makiyaya hari a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan.
Wadansu ’yan asalin yankin sun ce, watakila kisan bai rasa nasaba da gargadin Kungiyar IPOB ta yi cewa, a daina sayarwa da cin naman shanu a Kudu maso Gabas.
Sanarwar tana dauke da gargadin da Kakakin IPOB Emma Powerful ya fitar. A halin da ake ciki, har yanzu ’yan sanda ba su kama kowa ba game da harin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan lamarin ba, kuma nan gaba zai fitar da sanarwa. Abin bakin ciki, wadansu sun yi murna da kisan Alarabe a shafukan sada zumunta.
Wani faifan bidiyo da aka yada a shafukan sada zumunta a karshen watan jiya ya nuna gawar Alarabe cikin jini da shanu da dama da aka harbe kwance, yayin da wadansu ke fama da munanan raunuka sakamakon harbi dabandaban.
Kodayake an ji wadansu muryoyi a cikin bidiyon na nuna alhininsu game da harin da aka kai, babu wanda ya bayyana inda lamarin ya faru.