Yadda ’yan Kannywood suka yi jimamin rasuwar Sarkin Zazzau
Taurari manyan ‘kan masana’antar Kannywood sun girgiza da rasuwa Sarkin Zazzau
A ranar Lahadi ce Allah Ya yi wa Sarkin Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris rasuwa a Asibitin Sojoji na 44 bayan fama da gajeriyar jinya.
Rasuwar sarkin, ta jefa mutane da dama cikin jimami da damuwa, kasancewar sarki ne da ya kwashe sama da shekara 45 yana sarauta.
Ita ma masana’antar Kannywoood ba a barta a baya ba, domin jarumai da dama daga ciki da wajen Kaduna sun nuna jimaminsu tare da ta’aziyar rasuwar sarkin.
Adam A. Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya nuna cewa sun yi babban rashi.
- Gwamnonin Kaduna 20 da suka yi zamani da marigayi Sarkin Zazzau
- Masu zaben Sarkin Zazzau sun kebe
- Waiwaye kan rayuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris (1937-2020)
- Yadda dubban jama’a suka halarci jana’izar Sarkin Zazzau
“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. Allah Ya jikan Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris. Allah Ya sa Aljanna ce makomarsa. Mun yi babban rashi”, inji shi.
A wani sakon da ya wallafa tare da hoton marigayin, Adam A. Zango ya kara da cewa, “Ba zan taba mantawa da kai ba, Mai Martaba Sarki Dokta Shehu Idris, Sarkin Zazzau”.
Jarumi Ali Nuhu, wanda ake yi wa lakabi da sarki cewa ya yi, “Ina mika ta’aziyyata ga iyalai da daukacin jama’an Zazzau. Allah Ya jikan Alhaji Dokta Shehu Idris CFR, Ya sa mutuwa hutu ce gare shi”
Shi ma fitaccen darakta, Falalu Dorayi ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya ce, “Allahu Akbar! Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un. Allah Ya jikan Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris, CFR. Allah Ya yafe masa kurakuransa Ya haskaka kabarinsa”.
Furodusa Naziru Auwal, wanda aka fi sani da Naziru Danhajiya ya ce, “Arewa ta yi rashin jigo da rasuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris na Masarautar Zazzau. Allah Ya jikan shi Ya sanya shi a Aljanna”.
- Wakar ta’ziyyar Sarkin Zazzau
A nasa sakon ta’aziyar, Rabiu Rikadawa cewa ya yi, “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun. Allah Ya jikan ka Balaraben Sarki, Sarkin Zazzau. Allah Ya sa Aljannar Firdausi ce makomarka”.
Aminu Ala, ya wallafa ta’aziyarsa yana cewa, “Allah Ya kyautata makwancin Sarki Shehu Idris Mai Zazzau.
“Hidimar da ka yi wa al’umar Zazzau daga Shekarar 1975 zuwa 2020 Allah Ya ba ka sakamako da Aljannah.
“Allah Ya kyautata bayanka da alheri,” inji shi, sannan ya rera masa wasu baitoci cikin hikima yana cewa:
Rabbu don RahamarKa Ka sa a wanke shi da Almiski,
Rabbu don tausayinKa da kankara marashin sa Raki,
Rabbu don gafararKa Ka kankare zunubansa na aiki,
Rabbu don tausayinKa dukkan su’ali su zam masa sauki,
Rabbu sa kabbarinsa Min Raudhatun min riyadhul Hakki
Darakta Ishaq Sidi Ishaq ya ce, “Allah Ya gafarta wa Sarkin Zazzau, Ya sada shi da Manzon Allah SAW, amin. Mun yi babban rashi”.
Ita ma jaruma Umma Shehu ta wallafa a shafinta na Instagram tare da hoton marigayin cewa, “Allah Ya jikan ka da rahama. Allah Ya sa Aljanna ce makomarka, amin”.
Ita ma jaruma Hafsat Idris ta sake yada hotonsa da sakon ta’aziya, inda sakon ke cewa, “Allah Ya yafe masa kurakuransa”.
Sauran jarumai maza da mata ma sun ta wallafa hoton marigayin tare da yi masa addu’ar samun dacewa da rahamar Allah.
Sarki Zazzau, Alhaji Dokta Shehu Idris shi ne Sarkin Zazzau na 18 na Fulani kuma ya kwashe kimanin shekara 45 yana Sarkin Zazzau, kafin Allah Ya masa rasuwa a ranar Lahadin 20 ga Satumba, 2020 a Kaduna.