Yadda ’yan kasuwar rake suke gudanar harkokinsu a Jos
An kafa kasuwar rake da ke unguwar Farar Gada a garin Jos babban birnin Jihar Filato fiye da shekara 30 da ta gabata. Ta yi fice wajen sayar da rake, inda har daga wadansu jihohi ake zuwa saya, ko a yi safara zuwa jihohin Kudu. Mataimakin Shugaban kasuwar raken Alhaji Abdullahi Labaran ya bayyana cewa […]
An kafa kasuwar rake da ke unguwar Farar Gada a garin Jos babban birnin Jihar Filato fiye da shekara 30 da ta gabata. Ta yi fice wajen sayar da rake, inda har daga wadansu jihohi ake zuwa saya, ko a yi safara zuwa jihohin Kudu.
Mataimakin Shugaban kasuwar raken Alhaji Abdullahi Labaran ya bayyana cewa an kafa wannan kasuwa ne tun lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Janar Muhammad Buhari.
Ya ce “Kafin mu taso zuwa wannan waje muna zaune ne a Katako da kuma bayan babban masallacin Juma’a na garin Jos da Nasarawa, inda a lokacin gwamnatin mulkin soja tsohon shugaban kasa Janar Muhammad Buhari saboda shirin tsaftace muhalli da ta fito da shi, sai aka taso mu daga wadannan wurare aka dawo da mu wannan waje muka kafa wannan kasuwa.”
Ya ce sun samu nasarori masu tarin yawa a wannan kasuwa, inda suke sayo raken da suke sayarwa daga yankin Saminaka da ke Jihar Kaduna.
“Akalla akwai ’yan kasuwa sama da 500 da suke gudanar da harkokin kasuwancinsu a wannan kasuwa, kuma muna zaune lafiya, sannan dukkan ’yan kasuwar da suke gudanar da harkokin kasuwanci a wannan kasuwa suna samun rufin asiri.
Ya bukaci gwamnati ta taimaka musu wajen inganta tsaro a kasuwar.
Da yake zantawa da Wakilin Aminiya wani da yake sayar da rake a kasuwar mai suna Malam Balarabe Yakubu ya bayyana cewa a kullum yakan sayo kayan rake ya sauke a wannan kasuwa, inda yake sayar wa masu yankawa su sayar wa sauran jama’a.
Ya ce “Wata rana mu yi ciniki da yawa; wata rana kuma mu yi kadan, a gaskiya akwai tarin albarka a wannan kasuwa.”
Idris Kano ya ce a kullum yana zuwa wannan kasuwa ya sayi rake kamar kaya daya zuwa daya da rabi, ya yanka ya zuba a baro ya shiga cikin garin Jos talla.
Ya ce “Idan na shiga talla wata rana na samu riba mai yawa, wata rana na samu riba kadan. Ina samun abin biyan bukata a wannan kasuwanci.”
Auwalu Garba mai kankare rake ne a wannan kasuwa ya ce a kullum yana zuwa wannan kasuwa ya yi aikin kankare rake.
Ya ce “Muna kankare kaya rake guda daya kan Naira 100, kuma a kowace rana ina kankare rake kamar kaya 7.”
Ya ce yana samun abin da yake iya dawainiya da iyalinsa ba tare da takura ba.