‘Yadda ‘yan kunar bakin wake suka ta da bom a gabanmu’

A karshen makon da ya gabatane wadansu ‘yan kunar bakin wake suka kai hari a garejin Muna da ke wajen birnin Maiduguri, kusa da wata sansanin ‘Yan gudun hijira, inda sukayi nasarar kashe mutane sama da 20, a yayin da wadansu da dama kuma suka ji munanan raunuka, da a halin yanzu suke karbar magani […]

‘Yadda ‘yan kunar bakin wake suka ta da bom a gabanmu’
‘Yadda ‘yan kunar bakin wake suka ta da bom a gabanmu’

A karshen makon da ya gabatane wadansu ‘yan kunar bakin wake suka kai hari a garejin Muna da ke wajen birnin Maiduguri, kusa da wata sansanin ‘Yan gudun hijira, inda sukayi nasarar kashe mutane sama da 20, a yayin da wadansu da dama kuma suka ji munanan raunuka, da a halin yanzu suke karbar magani a Asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri.

Wadansu da al’amarin ya faru a kan idanunsu kuma suka tsira da kyar sun yi wa wakilinmu cikakken bayani.

Malam Bukar Abdu ya yi bayanin cewa, ‘’Mun kammala Sallar Isha’i bai wuce da minti ashirin ba sai muka ga wani yaro da bai wuce shekara 10 ba, da ba mu yarda da shi ba ya zo yana neman ya shiga cikinmu, to a lokacin muna zaune ne muna hira a majalisarmu, a gefe daya kuma wadansu suna shan shayi a wajen mai sayar da shayi, sai muka kore shi daga wajenmu. To a wurin akwai wata karamar kasuwa wanda yawanci ‘yan gudun hijira suke zuwa su yi sayayya a wurin. To bayan da muka kore shi, sai ya matsa wannan karamar Kasuwar  wadda take ci da dare, shikenan sai ya yi kokarin tayar da bom din, amma kafin ya tayar muna kallonsa, kuma muna ta kururuwan a cafke shi, don mu ba mu yarda da shi ba. Kafin mu Ankara ya tayar da bom din, inda shi ya  mutu, kuma ya shafi wadansu da ba su da tazara da shi, ya kashe su, akalla za su kai 15, duk da shi 16 ke nan, amma akwai wadansu da abin ya shafe su amma ba su mutu ba, sun dai ji mummunan raunuka,  da kyar za su kai labara.  Da jin tashin bom din sai kowa ya yi ta kansa, kafin daga baya muka dawo muka fara aikin ceto.’’ 

‘’Wallahi abin ya daure mana kai kuma ya ba mu mamaki, ganin mun saki jikinmu, saboda an dauki dogon lokaci ba a kara samun irin wannan ba a wannan wuri, duk da cewa ba wani abin mamaki ba ne, domin dama haka suke yi, sai sun bari mutane sun saki jikinsu, sai su zo su tayar da bom dim. To kuma ka san nan kan hanyar Gamboru Ngala ne, daga nan Maiduguri,  za a iya cewa hanyar maboyarsu ce, su ‘Yan Boko Haram din, domin da ma Jami’an tsaro suna raka mutane daga nan zuwa Gamboru Ngala da Kamaru da Chadi tun bayan da Jami’an tsaron suka bude wannan hanya kusan shekara biyu ke nan, saboda haka ko lokacin da suke kawo hare-harensu muna cikin zullumi, to amma dai yanzu mun tsira da kyar. Ka san wannan wurin wajen neman abincinmu ne babu yadda za a yi mu bari da garaje. Allah dai Ya tsare mu.’’

Shi ma Malam Kachalla Bukar,  yana yadda aka ta da bom din a  kauyen Muna Dalti, yay in da wadansu ‘yan mata su biyu ‘yan kunar bakin wake suka tayar da nasu, inda ya sha da kyar. Ya bayyana cewa,’’Wallahi wadansu yara mata ne su biyu suka tayar da bom a wannan kauyetamu ta Muna Dalti, kan hanyar Maiduguri zuwa Gamboru Ngala, kuma ita ce za ta kai ka kasar  Kamaru. Wato daya da ta tayar ta ji wa mutane rauni tare da kashe mutum biyu, amma daya kuma kanta kawai ta kashe, sa’annan ita ma wanda ta ji wa mutane rauni tare da kashe mutum biyu kuma ta mutu, kodayake mu muna da tazara daga inda suka tayar da bam din, amma wadansu mutanenmu abin ya shafe su kuma sun la’anta mana kauyenmu, kodayake Jami’an tsaro sun kawo mana dauki, a yanzu haka wadanda suka raunata an kai su Asibitin koyarawa na Jami’ar Maiduguri.’’