Yadda ’yan makarantar gwamnati suka ba na kudi kunya a mahawara

kwazon da ‘yan makarantar gwamnati Hajara Mustapha da Shedrack James  suka nuna a yayin gudanar da gasar mahawara ta kasa da aka yi a Abuja ya nuna cewa har yanzu makarantun gwamnati suna da sauran mutunci.Hajara dai daliba ce a makarantar firamare ta Bashir Abubakar da ke Unguwar dankali a danmagaji da ke Zariya, shi […]

Yadda ’yan makarantar gwamnati suka ba na kudi kunya a mahawara

Hajara Mustapha da Shedrack Jameskwazon da ‘yan makarantar gwamnati Hajara Mustapha da Shedrack James  suka nuna a yayin gudanar da gasar mahawara ta kasa da aka yi a Abuja ya nuna cewa har yanzu makarantun gwamnati suna da sauran mutunci.
Hajara dai daliba ce a makarantar firamare ta Bashir Abubakar da ke Unguwar dankali a danmagaji da ke Zariya, shi kuma Shedrack yana makarantar firamare ta Daniel Gowon ne da ke Wusasa a Zariya. Wadannan daliban biyu su ne suka wakilci jihar Kaduna a gasar mahawara da ma’aikatar ilimi ta tarayya ta shirya, inda suka zama zakaru.
Wadanda suka shiga gasar sun fito ne daga makarantun gwamnati da kuma masu zaman kansu daga jihohi 36 na kasar nan da kuma Abuja. Hajara, ‘yar shekara 10, ita ce ta zama zakara a fannin iya nuna misali, shi kuma Shedrack ya zama zakara a fannin iya jawabi, wanda ya sanya aka dauki nauyin karatunsu har zuwa jami’a.
Wadannan dalibai guda biyu dai suna koyon karatu ne a kan dabe a azuzzuwan makarantunsu, domin kamar yadda Aminiya ta gano, babu kujeru da tebura da kuma sauran muhimman kayan koyarwa a azuzzuwan nasu kamar yadda ake samu a makarantu masu zaman kansu.
Hajara ta ce daukar nauyin karatunta da aka yi zai ba ta damar cim ma burinta na zama lauya, ‘’na yi matukar farin ciki da samun wannan nasarar, ina godiya ga iyayena da malamaina da kawayena.Baya ga daukar nauyin karatunmu da aka yi , an kuma ba mu wadansu kudi, da yake kuma ni mace ce an kara mun da keken dinki. Wannan karfafa gwiwar da na samu zai taimaka mun wajen cim ma burina na zama lauya.’’ Inji Hajara.
Shi kuwa Shedrack cewa ya yi nasarar da ya samu ya karfafa masa gwiwa, “yanzu ina daukar kaina kamar kowane dalibi, ba na tunanin ni kaskantacce ne a tsakanin dalibai, domin na fafata ne da daliban da suka fito daga makarantun da ake jin cewa su ne na kawarai a kasar nan, kuma sai muka kasance a cikin zakaru, na ji dadi kwarai, ina matukar farin ciki.’’
Burina shi ne in zama likita, yanzu da yake an dauki nauyin karatuna, an sauwake wa iyayena nauyin karatuna ke nan, wadanda da ma masu karamin karfi ne. Ina godiya ga Allah da Ya ba ni wannan damar, ina kuma godiya ga shugaban karamar Hukumar Zariya saboda saya mini keke da ya yi da kuma sa da ya saya mana, baya ga wadansu taimakon da ya yi mana.’’ Inji Shedrack.
Shugabar makarantar firamare ta Bashir Abubakar, Hajiya Hauwa Muhammad, cikin farin ciki ta bayyana cewa, Hajara, wadda ‘yar aji hudu ce, ta zama zakara ce a fannin iya nuna misali a babbar gasar mahawara ta kasa da aka gudanar a Abuja.
Ta ce, ‘’nuna misali yana nufin dalibi ya kware a wajen kwaikwayo da ban dariya a yayin gudanar da mahawarar, idan na ce kwaikwayo, ina nufin yin amfani da hannaye da baki da sauran gabubban jiki wajen bayyana abin da mai mahawara yake cewa. Iya yin haka yana kara maki da kara armashin gasar, to Hajara ce ta zama zakara a wannan fannin.’’
‘’Wannan ya nuna cewa ashe ba kyawun aji ko makaranta ne ke samar da ingantaccen ilimi ba, kwararrun malamai ne suke samar da haka. Na san cewa mutane da yawa sun yanke tsammani da makarantun gwamnati irin namu, amma ina tabbatar maka cewa matsayinmu ya wuce inda mutane suke zato, har yanzu mu ne muke samar da wadansu daga cikin daliban da suka fi kwazo a kasar nan, wannan gasar ta kasa da aka yi Hajara Mustapha (a hagu) da Shedrack James suna zaune a kasa a ajujuwansuta kara tabbatar da ingancinmu.’’ Inji Hajiya Hauwa.
Ta ci gaba da cewa,’’Idan ka tuna, mafi yawan shugabannin kasar nan makarantun gwamnati suka yi, domin haka wannan gasar ta kasa ta kara nuna cewa har yanzu muna iya samar da daliban da suka fi basira a kasar nan.’’
‘’Abin lura shi ne, makarantu daga kowane bangare na kasar nan ne suka hadu a wurin gasar, har da makarantu masu zaman kansu da ake takama da su, amma duk da haka dalibanmu suka zama zakaru.Duk da cewa ba mu da kyawawan azuzzuwa da kujeru da wadansu muhimman abubuwa, amma muna da kwararrun malamai.’’
Shi ma shugaban makarantar firamare ta Daniel Gowon, Malam Nuhu Aminu, ya bayyana matukar farin cikinsa da nasarar da dalibin makarantarsa Shedrack ya samu a gasar.
Ya ce, ‘’Shedrack ya zama gwarzo ne a fannin iya jawabi a yayin gasar, iya jawabi yana nufin dalibin da ya fi zakin baki a yayin gasar, hakan na nuna cewa dalibin mai basira ne sosai. Muna tabbatar maka cewa yanzu makarantun gwamnati ba kanwar lasa ba ne, domin gwamnati tana taimaka mana, idan aka ci gaba da haka, ina tabbatar maka kwanan nan mutane za su daina kai ‘ya’yansu makarantu masu zaman kansu.’’ Inji Malam Aminu.
Da yake tofa albakacinsa bakinsa game da nasarar da daliban suka samu, shugaban karamar Hukumar Zariya, Alhaji Lawal Balarabe ya ce ya yi matukar farin ciki, tare da bayar da tabbacin cewa karamar hukumarsa za ta ci gaba da inganta harkar ilimi ta hanyar samar da muhimman abubuwan koyarwa da daukar kwararrun malamai da kuma karfafa sashin kula da makarantu na karamar hukuma.