Yadda ’yan mata suka koma fasakwaurin shinkafa a Kudu

Hukumar Kwastam ta dage wajen kara tsaurara tsaro a yankin domin dakile harkokin fasa-kwaurin.

Yadda ’yan mata suka koma fasakwaurin shinkafa a Kudu

A yanzu haka ’yan mata marasa aure a Kudu maso Yammacin kasar nan, suna barin kasuwanci suna shiga harkar da take ‘tashen kawo kudi’ wato fasa-kwaurin shinkafa.

’Yan matan sun shiga harkar fasa-kwaurin shinkafa ka’in-dana’in inda suke shigowa da ita daga Jamhuriyyar Benin ta hanyoyin kauyuka da dazuzzukan da ke makwabtaka da kasar.

Aminiya ta gano cewa wasu daga cikin ’yan matan sun koma Legas da zama ne daga jihohin Kudu maso Yamma da wasu jihohin da ke makabtaka da Nijeriya suka shiga harkar shinkafar.

Yayin da Aminiya ta kai ziyara a wasu shaguna da kasuwanni a Legas da suka hada da Kasuwar Alabar Rago da Daleko dukkansu a kananan hukumomin Ojo da Mushin wakilanmu sun gane wa idanunsu yadda ’yan kasuwar ke hada-hadar shinkafar kasar waje a fili.

Lokacin ziyarar Aminiya a Alabar Rago, wakilanmu sun ga yadda ake sauke buhunan shinkafar daga motoci wadanda aka ajiye su a gefen titi, inda aka yi saurin adana su a wani wuri da aka yi shi da katako da ake amfani da shi a matsayin ma’ajiya.

Wakilanmu sun ga yadda ’yan kasuwar ke ta farin ciki saboda ribar da suke samu a hada-hadar shinkafar, abin da yake nuni da cewa haramtaccen kasuwancin zai ci gaba zuwa wani lokaci.

A cewar majiyarmu a jihohin Legas da Ogun masu fasakwaurin suna cin karensu babu babbaka musamman a lokacin bukukuwa.

Yara mata da shekarunsu ba su wuce 30 ba, suna fasakwaurin kayayyaki a wurare daban-daban a kan iyaka ba wai kawai da daddare ba har ma da rana-tsaka.

A kullum da zarar gari ya waye ana fara hada-hada a kauyukan da ke kusa da kan iyakokin Seme da Idiroko.

Za a ga yadda wasu mazauna yankin ke tafiya a kafa wasu kuma a kananan abin hawa inda suke hada-hadar shinkafa zuwa cikin kasar nan.

Adenike Odugayo wacce uwa ce da suka rabu da uban ’ya’yanta ta ce, tana amfani da ribar da take samu a wannan kasuwanci wajen daukar nauyin ’ya’yanta.

“Ina zuwa nan ne tun daga Ibadan don sayen shinkafa. Shekaru da dama mijina ya yi watsi da ni ya samu wata.

“Kawata wacce ita ma ba ta da miji ta jawo ni cikin wannan harka. Kasuwancin shinkafar nan na da hadari domin mace na fuskantar cin zarafi daga jami’an tsaro maza da ke kan iyaka.

“Abin da ke yi wa mutum dadi a harkar shi ne kudin da ake samu a kowane karshen lokacin da aka yi tafiya.

“Akwai wani lokaci da na yi asarar dukkan kudin da nake tarawa a lokacin da jam’ian Kwastam suka kwace kayana.

“Duk kokarin yi musu bayanin dalilin da ya sa na shiga wannan harka ba su yarda da ni ba.

“Bayan wani lokaci sai na samu bashi daga banki inda na koma sana’ata. Saboda ta fi sana’ar da nake yi a baya. A da ina tallar magungunan kawar da radadi ne,” in ji ta.

Wata mai sayar da shinkafar wadda ta bayyana sunanta da Folashade ta ce ta bar harkar sayar da kifi ne ta shiga wannan harka ta shinkafa.

A cewarta kifi ya yi tsada don haka ta koma sayar da shinkafar da kudin da ta tara daga sayar kifi.

Ta ce, “Na san cewa fasakwauri na da hadari. Sai dai dole ne ta sa na shiga saboda mijina ya rasu bayan shekara shida da aurenmu.

“Ina da ’ya’ya uku namiji daya da mata biyu, wadanda nauyin kula da su ya hau kaina.

“Rayuwa babu sauki a matsayina na macen da ba ta da miji.

“Muna zuwa Kasuwar Kwatano mu sayo shinkafar. Bayan mun sayo sai mu bayar da shinkafar ga mutanen da za su tsallako mana da ita kan iyaka.

“Idan kuma kana so su kai maka wani wuri daban, to, sai ka kara musu kudi,” in ji ta.

Shi kuwa Ebangelist Enoch Ojota ya shaida wa wakilanmu a Badagiri inda mata da yawa suka bar kasuwancinsu suka koma harkar shinkafar inda ya ce suna samun kudi sosai a harkar.

“Ba za su zauna a kananan shagunansu a cikin ruwa da tsanani zafin rana suna jiran masu sayen shinkafa su zo ba.

“Abin da suke bukata shi ne su taka su je Benin su sayo shinkafa buhuna biyu su raba su a kananan buhuna su taho da su kan iyakar Nijeriya inda za su hau mota don ta kai su wurin da suke,” in ji shi.

A cewarsa matan suna kwana a budaddun motoci da kuma wannan ma’ajiyar tasu abin da ke iya jawo cin zarafi gare su.

An gano cewa jami’an tsaro da tsofaffi a wasu lokutan suna daukar dakon kayan inda ake biyan su Naira 500 zuwa Naira 1,000 inda suke shirya su a cikin ma’ajiyar da ke kan iyaka Mafi yawa daga cikinsu suna kaiwa da komawa da dama domin su kara samun kudi.

Ashipa da Gbetrom da Topo da Suntan Beach da OwodeApa da J5 Park, suna daga cikin kauyukan da ake tsallakawa zuwa Badagiri da kananan buhunan shinkafa daure a kugunsu yayin da wasu kuma ke dorawa a kan kafadunsu.

Yankin Seme da Idiroko da ke Legas da Ogun sun hada iyaka da Benin

Wani dan dakon shinkafa a Idiroko mai suna Jide Kalajaiye mai kimanin shekara 52 ya ce, ‘‘Masu kudi sosai sun kafa ma’ajiya a kan iyaka inda muke ajiye shinkafar a ciki.

Ma’ajiyar da aka fi sani ita ce wacce ake amfani da wani gida da ba a kammala gininsa ba a duk mako ana karar da shinkafar da aka shirye a cikinsa a kai ta cikin gari,” in ji shi.

Ya ce ’yan dako suna yin aikinsu ne da asuba inda suke daukar shinkafar zuwa wurare masu nisa don kai shinkafar.

“Muna yin tafiya mai tsawo a kafa inda muke daukar buhunan shinkafar muna auna nauyin buhun ya kai kilo10.

Ya ce kashi na biyu na masu aikin za su fara nasu aikin da misalin karfe 9:00 na dare a daidai lokacin da sauran mutane ke barci.

Wasu ’yan dakon suna kai shinkafar ce da almuru suna ratsawa ta tsakanin itatuwan kwakwa.

Ba su fiye yin wannan tafiye-tafiye cikin tsakar dare ba domin a wannan lokaci an fi kama su.

Majiyarmu a Rundunar ’Yan sandan Seme ta ce mafi yawan mutanen da suka shiga harkar shinkafar ba su da aikin yi.

Wadannan mutanen kauyen suna daukar shinkafar daga dillalai su kai Legas ko Idiroko.

A wasu lokutan matasan da ba su da aiki maza da mata suna dakon shinkafar.

A wasu lokutan ma tsofaffi suna yin harkar. Duk da hukumomi suna kokarin ganin bayan an daina fasa-kwaurin shinkafa sai dai irin kudin da ake samu daga haramtaccen kasuwancin ya sa ana ci gaba.

Masu sayar da shinkafar gida sun ce a ’yan watannin nan farashin shinkafar ya yi tashin gwaron-zabo a Kudancin kasar nan.

“Kuma hana shigo da shinkafa daga waje ya janyo tashin farashin shinkafar da ake sayarwa a kan Naira 30,000 a shekarar 2023 ta zama Naira dubu 70,” in ji Tawa Ojo wani mai sayar da shinkafar gida a Sanga-Ota a Jihar Ogun.

Hukumar Kwastam ta ce ta kama buhunan shinkafar waje dubu 222 da 285 wato kusan tirela 379 daga hannun masu fasa-kwauri a cikin shekara uku, daga watan Satumba 2021 zuwa Afrilun 2024.

Wani tsohon kwanturolan a hukumar, Kehinde Ejubunu ya ce babban kalubalen da ya fuskanta a lokacin da yake aiki shi ne yadda ake yawan kai wa jam’iansu farmaki a lokacin da suke bakin aiki.

“Don a yi maganin wannan kai farmaki sai aka fara shirya taron wayar da kai inda muka rika kai ziyar ga sarakunan gargajiya na al’ummomi da ke kusa da kan iyaka.

“Lamarin da ya kawo raguwar kai farmakin sosai,” in ji shi.

Ya ce jami’ansu sun kama wadanda ake zargi su 386 wadanda suke da nasaba da kayan da aka kwace inda kotu ta hukunta mutum 22 wadanda aka samu da laifuffuka daban-daban.

Ya ce, “Abin takaici a lokacin da jami’anmu ke gudanar da aikinsu takwas daga cikinsu sun hadu da raunuka daban-daban yayin da biyar daga ciki suka riga mu gidan gaskiya.”

Kwanturola Timi Bomodi da ke kula da Iyakar Seme ya ce a tsakanin watan Janairu zuwa Fabrairun 2024, Hukumar Kwastam ta kama buhun shinkafa 2,198 kimanin tirela uku da litar man girki dubu 81 da 930 da motoci tara da kunshin harsasai 265 da bindiga kirar gida guda biyu da kayan maye da suka hada da katan din kodin 149 da wasu kayayyaki.

Bomodi ya ce duk kayayyakin da suka kama suna dauke da shaidar biyan kudin haraji na DPB kimanin Naira miliyan 366.

Ya ce an kama mutum 13 da ke da alaka da kayan da aka kwace, inda aka bayar da belin shida daga cikinsu, yayin da aka mika mutum uku ga Hukumar Hana Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi (NDLEA), don daukar matakin da ya dace.

“Mun mika daya daga cikinsu ga ’yan sanda yayin da ukun ke tsare a hannunmu.

“A nan ina sake nanata irin alfanun da ke tare da yin aiki tare, wanda ya samu ne sakamakon samun hadin kai da tattaunawa da muke yawan yi a tsakanin jami’an tsaro da ke wannan waje,” in ji shi.

Da yake bayani kan alfanun hanyar Legas zuwa Abidjan, ya ce babbar hanyar da za ta sadar da kai wannan wuri ita ce ta Legas zuwa Badagiri.

“Hanya daya tilo ita ce ta ruwa, shi ya sa muke hada kai da Rundunar Sojin Ruwa.

“Su kansu sojin ruwan da na kasa suna ba mu hadin kai a wannan lokaci da muke fama da masu fasa-kwauri.

“A matsayin hukumarmu ta mai ruwa -da-tsaki a abin da ya shafi iyaka mun san amfanin karkasa ayyuka a tsakanin masu ruwa-da-tsakin.

“Saboda mun san cewa masu fasa-kwaurin ba za su hakura ba, za su ci gaba da neman wasu sababbin hanyoyi don su mayar mana da martani.

“Muna ba a’lumma tabbacin cewa za mu ci gaba da aikin da muke yi ba za mu ji tsoron hare-haren da ake kaiwa kan jami’anmu wadanda aka kashe yayin da aka jikkata wasu da dama,” in ji shi.

Ya ce, “Wannan ne lokacin da muke fuskantar kalubale sakamakon yadda batagari ke son cin karensu ba babbaka ko ta halin kaka.

“Mu da muke a kan iyakar Seme da Krake za mu tabbatar mun kare kanmu daga hare-haren.”

Kwastam na tsaurara tsaro

Da alama Hukumar Kwastam ta dage wajen kara tsaurara tsaro a yankin domin dakile harkokin fasa-kwaurin.

Kwanturola Mai kula da Shiyyar Tekun Yammaci, Paul Bamisaiye ne ya bayyana hakan, inda ya ce suna samun nasarar dakile harkokin a bata-garin.

Ya ce jami’ansa suna sintiri da kananan jiragen ruwa a yankin ba dare ba rana.

Kakakin Sashen Idiroko, Hameed Oloyede ya ce yanayin yankin na ruwa na taimakawa wajen ta’azzarar fasa-kwaurin.

Sai dai ya ce jibge jami’ansu da suka yi a yankin ya taimaka wajen rage matsalar bata-garin sosai.

“A wasu lokutan muna samun sauki da taimako daga mutanen kauyen, wadanda sun fi tausaya wa masu fasakwaurin.

“Suna ganin harkar fasa-kwauri a matsayin halattacciyar aba wadda babu laifi ko kankani a ciki. Muna iya kokarinmu don ganin ba mu yi amfani da karfi ba.

“A wasu lokutan muna shiga don wayar da kan sarakunan gargajiya kan bukatar da ke akwai wajen shawartar yaransu su bar harkar fasa-kwaurin.

“Abu ne mai wahala, amma dai muna dauki-ba-dadi da masu wannan harkalla, kuma za mu samu nasara a kansu,” in ji shi.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa