Yadda ’yan matan kasar Togo kan yaudari ’yan Arewa a Legas

Ga dukkan alamu soyayya ta yi nisa tsakanin ’yan matan kasar Togo da ake kira Kwatakwali da ’yan Arewa da ke yin cirani a Legas, har ta kai ga wasu daga cikin ’yan Arewan kan manta da matansu na aure da ’yan uwansu su zauna tsawon lokaci ba su ziyarci gida ba.Binciken Aminiya ya nuna […]

Yadda ’yan matan kasar Togo kan yaudari ’yan Arewa a Legas

Momi ke nan daya daga cikin matan da ke da farin jini a LegasGa dukkan alamu soyayya ta yi nisa tsakanin ’yan matan kasar Togo da ake kira Kwatakwali da ’yan Arewa da ke yin cirani a Legas, har ta kai ga wasu daga cikin ’yan Arewan kan manta da matansu na aure da ’yan uwansu su zauna tsawon lokaci ba su ziyarci gida ba.
Binciken Aminiya ya nuna wasu daga cikin ’yan Arewan na kama dakuna su ajiye ’yan matan a matsayin daduro kuma su rika daukar dawainiyarsu fiye da matansu na aure. dawainiyar ta hada da biyan kudin abinci da na kayan kwalliya da kudin adashi da kayan salla, sannan kuma da yi musu sayayya idan za su je Togo ganin gida.
Aminiya ta gano cewa wasu ’yan Arewan ’yan matan ne ke damfararsu daga baya su yi watsi da su bayan sun raba su da abin hannunsu. Wasu ’yan Arewa da Aminiya ta zanta da su sun bayyana mamakin yadda soyayyata yi kamari a tsakanin ’yan matan da ’yan Arewa, wasu kuwa zargin ’yan matan suka yi na yin amfani da sihiri don mallake ’yan Arewan da ke neman su.
Wani dan Arewa daga karamar Hukumar Madobi ta Jihar Kano mai suna Hasan Madobi ya ce, “Sai ka sami mutum ya shekara da shekaru bai je gida ba, yana nan ya tare da kwatakwali yana yi mata hidima. Ya ba ta kudin abinci, ya yi mata zubin adashi, amma matarsa ta gida ko sisi bai bar mata ba. Ban da haka ma akwai kudin ‘anko’ da suke bayarwa daga lokaci zuwa lokaci idan wani biki ya tashi.
Hassan Madobi, daya daga cikin samarin da ke tashe a Legas“Akwai wani da ya nemi wata yarinya da yayansa ya ji labari, sai ya mayar da shi gida, amma ko da yarinyar ta dawo daga Togo ta sami labari, sai ta yi masa asiri, dole ya dawo wurinta ya yi kwana biyu wajenta lokacin azumi, ko azumi ma bai yi ba. Kai, daga karshe da aka yi kokarin raba su, sai kawai ya cinna wa kansa wuta zai kashe kansa. A yanzu yana nan ya zama mahaukaci”. Inji shi.
daya daga cikin ’yan matan mai suna Momiyo ta yi watsi da zargin da aka yi musu na yin amfani da sihiri don mallake ’yan Arewa da ke nemansu. “Mu ba wani magani, kawai so ne da kauna ke tsakaninmu da su. Muna yi musu duk abin da suke so, wajen biyayya da ladabi kuma muna taimaka musu idan sun shiga matsala ta rashin kudi. Idan kina da saurayi ya shiga matsalar kudi ke za ki ba shi. Kuma idan kin ba shi, babu maganar wai sai ya biya ki kudin. Kuma idan kama shi aka yi, ke za ki shiga ki fita ki tabbatar ya fito. Shi ya sa muke zuba adashi muke tara abin da suke ba mu. Wani lokaci ma babu riba, saboda idan ba ka yi sa’ar saurayi ba, babu abin da za ki rika samu, sai duka da zagi”.
Da yake magana a madadin sarkin Agege, Hakimin Gabas kuma dan’iyan Agege, Alhaji danjuma Yakubu ya bayyana cewa jahilci ne ke sanya wasu fadawa cikin irin wannan al’amari. “Wasu ba sa sauraron wa’azi. A shekarun baya irin haka ta taba faruwa a Agege inda za ka ga har wasu magidanta suna tarewa a dakunan irin wadannan ’yan mata, amma yanzu ya zama tarihi saboda matakan da masarautar Agege ta dauka na fargar da mutane su gyara halayensu. Cikin matakan da sarkin Agege ya dauka akwai fadakarwa da hada gwiwa da shugabannin al’umma da malamai domin yin wa’azi ga al’umma, da wahala ka samu masarautar da ake yin haka a nan kudancin Najeriya. Mai marataba sarkin Agege yakan yi taro da majalisar malamai don fadakar da su halin da ake ciki. Mun sami nasara ne saboda jajircewa da mai martaba sarkin Agege ya yi”.
Wani mai wa’azin Musulunci a Legas, Malam Suraj Sa’id ya ja hankalin jama’a da su guji aikata sabo. “Ya kamata mu ji tsoron Allah. Zina haramun ce ko kusantarta ba a so, balantana ka aikata. Ko da wadanda ba musulmi ba sun amince cewa zina ba ta da kyau. Ya kamata mu nusance ta domin samun rahamar Allah”. Inji shi.