Yadda ’yan Najeriya ke jan zarensu a Gasar Serie A ta Italiya

United na zawarcin Victor Osimhen da aka yi wa farashin dala miliyan 100.

Yadda ’yan Najeriya ke jan zarensu a Gasar Serie A ta Italiya

A Gasar Serie A ta Italiya, ’yan wasan Najeriya biyu, Victor Osimhen da ke taka leda a Kungiyar Napoli da Ademola Lookman na Kungiyar Atalanta ne suke jan ragamar zura kwallaye a raga a kakar bana.

Yanzu haka Osimhen yana da kwallo 13, inda kwallayen da ya zura suke taimaka wa Kungiyar Napoli darewa kan taburin gasar.

Shi kuma Lookman yana da kwallo 11 a kakar ta bana, duk da cewa a gefe yake buga wa Kungiyar Atalanta.

Osimhen ne na daya a wadanda suka fi zura kwallo a gasar, sai Lookman ke biye masa a gasar da take da zaratan ’yan wasa irin su Dybala na Roma da Dusan Vlahovic na Jubentus da Giroud na AC Milan da sauransu.

Haka kuma bayan zura kwallaye a ragar abokan hamayya, ’yan wasan biyu sun taimaka an zura kwallaye takwas, inda kowane ya taimaka sau hudu.

Lookman ne dan wasan Atalanta na hudu a tarihin kungiyar da ya zura kwallo sama da 10 a kaka daya.

Sauran ukun su ne Leschly Sorensen a 1949 zuwa 1960, sai Karl Aege Hansen a kakar 1949 zuwa 1950, sai Poul Rasmussen a 1952 zuwa 1983, wanda kuma yanzu haka akwai sauran wasanni da dama a kakar ta bana.

Wannan kwarewa da ’yan wasan biyu na Najeriya ke nunawa ta kara musu daraja, sannan ta kara wa kasarsu daraja.

Rahotanni sun ce Kungiyar Manchester United na zawarcin Victor Osimhen, sai dai kudin da Napoli ta yi masa na Dala miliyan 100 ne ya yi wa Man U yawa.

Sai dai a yanzu haka yana cikin ’yan wasan gaba masu tsada a duniyar kwallo, yayin da Lookman yake kara jan hankalin kungiyoyi.