Yadda ’yan Najeriya ke juyayin rasuwar Arotile
’Yan Najeriya na ta nuna alhininsu game da mutuwar ’yar kasar ta farko mai tuka jirgin yaki Tolulope Arotile wadda ta rasu tana ‘yar sheakra 23 sakamakon hatsarin mota a jihar Kaduna ranar 14 ga Yuli, 2020. ’Yan kasar na ta mika sakonnin ta’aziyyar rasuwar hafsar sojin saman ne a Twitter da sauran shafukan sada […]
’Yan Najeriya na ta nuna alhininsu game da mutuwar ’yar kasar ta farko mai tuka jirgin yaki Tolulope Arotile wadda ta rasu tana ‘yar sheakra 23 sakamakon hatsarin mota a jihar Kaduna ranar 14 ga Yuli, 2020.
’Yan kasar na ta mika sakonnin ta’aziyyar rasuwar hafsar sojin saman ne a Twitter da sauran shafukan sada zumunta, kamar haka:
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga mutuwar Tolulope Artile matukiyar helikwaftan yaki ta farko a Najeriya.
Kamar yadda mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na twitter@GarShehu cewa shugaban ya yi addu’a ga iyalanta na fatan jurewa wannan babban rashi da su ka yi.
Shugaba Buhari ya jinjina wa Arotile kan kwazonta a filin yaki domin kare kasarta daga ‘yan tada kayar baya.
Sanata Shehu Sani @ShehuSani, tsohon Dan Majalisar Dattawan mai wakilarta Kaduna ta Tasakiya Sanata Shehu Sani ya ce, “Abin takaici lokaci kadan bayan na wuce ta barikin sojin sama da ke Kaduna, hatsarin ya faru wanda ya yi ajalin matukiyar jirgin yaki ta farko ’yar Najeriya Tolulope Arotile. Babban rashi ga Najeriya. Allah Ya jikan ta”.
Shi ma tsohn Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa,
Ike Ekweremadu @iamekweremadu:
Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu ya ce: “Ta’aziyyata ga @NigAirForce da iyalan Tolupe, mace ta farko ‘yar Najeriya matukiyar jirgin sama wadda ta mutu a hatsarin mota a barikin sojin sama na Kaduna. Mai shekara 23, ta kafa tarihi. Ta yi kokari wajen yaki da ’yan bindiga a shirin Operation GAMA AIKI, Allah Ya ji kanta.
__________________________________________________________
ZAZKID | PR | BLOGGER @badmus_fazaz
Ina addu’ar Ubangiji ya sa Tolulope Arotile kin huta, sannan ya bai wa ’yan uwanki juriyar rashin jarumar mace.
_________________________________________________________
“Rashin Tolulope Arotile ta bar babban gibi a ci gaban Najeriya. Duk kalaman da zan fada ba za su dawo da ke ba a raye. Ina godiya da irin hidimar da kika yi wa Najeriya. Allah Ya jikanki”, inji Adewale A. Majofodun @Adewale_Majoff
“Duniya ke nan, watanni kadan da suka gabata muke mika sakon taya murna, amma yanzu rai ya yi halinsa”, a cewar Auntee Rita @mamacitatweet.
Somto Okonkwo @MrSomtoOkonkwo ya wallafa cewa ’Yar Najeriya matukiyar jirgin sama ta farko Tolulope Arotile ta mutu…Ta rasu ta nada shekara 23 kacal. Kin mutu kina da matashiya Tolulope, wannan ya zo ne kamar mafarki.
Nicky Baby @Nickybaby kuma ta ce “yanzu nake samun labarin mutuwar ba-zata na mutuwar matukiyar jirgin sama Tolulope Arotile (Mace ta farko marukiyar jirgin yaki ’yar Najeriya) ta rasu a hatsarin mota muna yi mata addu’ar samun nasara”.
Shi kuma Peter Dumkwu @Peter_Dumkwu ya ce “Mutuwa ta dauke rayukan jama’a da dama da ba a yi zato ba a wannan shekarar. Allah Ya ji kan ki. Shi kadai Ya san dalilin rasuwarki.
Yung denzL @MI_Abaga, ya ce Allah Ya jikan Tolulope Arotile. Jarumar ‘yar Najeriya da ta fara tuka jirgin yaki ‘yar shekara 23!!!! Ba za mu manta ki ba”.