Yadda ‘yan sanda suka bude wuta akan ‘yan kasuwa a Abeokuta
Jami’an ‘yan sandan da ke sashin yaki da aikace-aikacen ‘yan kungiyar asiri sun yi harbin kan mai uwa da wabi a kasuwar kayan gwari ta Olomore da ke kwaryar birnin Abeokuta a jihar Ogun, kasuwar da mafi akasarinta ‘yan Arewa ke hada-hada a cikinta. Sarkin Hausawan Abeokuta Alhaji Ibrahim Hassan, ya shaidawa Aminiya cewa hatsaniya […]
‘Yan sanda tare da ‘yan kasuwar kayan gwari ta Olomore
Jami’an ‘yan sandan da ke sashin yaki da aikace-aikacen ‘yan kungiyar asiri sun yi harbin kan mai uwa da wabi a kasuwar kayan gwari ta Olomore da ke kwaryar birnin Abeokuta a jihar Ogun, kasuwar da mafi akasarinta ‘yan Arewa ke hada-hada a cikinta.
Sarkin Hausawan Abeokuta Alhaji Ibrahim Hassan, ya shaidawa Aminiya cewa hatsaniya ta barke a kasuwar kayan gwari ta Olomore bayan da wasu ‘yan sanda suka biyo wasu da ake zargi ‘yan kungiyar asiri ne.
” ‘Yan sandan sun biyo mutum biyu da ke kan babur wadanda suka tserewa ‘yan sandan, kodaa suka gaza kame su akan hanyar dawowarsu sai suka iske yaran motar da ke sauke tumatur a kasuwar suna karkashin motocinsu suna hutawa, sai ‘yan sandan suka farmasu nan take ‘yan kasuwar suka ce, baza a kama yaran motar ba, nan take ‘yan sandan suka fara harbin kan mai uwa da wabi lamarin da ya yi sanadiyar raunata ‘yan kasuwar biyu, inda harsashi ya sami daya a kai ɗaya kuma a kafa wadanda zuwa ‘yanzu ake basu kulawa a cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Abeokuta.
Kwamishina ‘yan sanda ya zo ya bamu baki ya kuma bada tabbacin binciko tare da hukunta ‘yan sandan dake da hannu a lamarin, ya kuma sha alwashin biyan kuxin asibiti na wadanda aka jikkata” inji Sarkin Hausawan Abeokuta.
Ya ce, ‘yan sanda sun bashi yaran motar su biyar da suka kai ofishinsu na Lafenwa, “Kasan daman wannan al’adar ‘yan sanda ce, idan sun biyo wadanda ake zargi da aikata laifi muddin basu cin masu sun kama su ba, to sai suyo kan mai uwa da wabi, su kama wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, wannan shi ne abin da ya janyo rikicin.” In ji shi.

Zuwa yanzu hankali ya kwanta a yankin kasuwar ta Olomore bayan da ‘yan kasuwar suka yi zanga-zangar nuna bacin ransu ga yadda ‘yan sandan suka kame masu mutane suka kuma harbi mutum biyu.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewa ba a sami salwantar rai a hargitsin kamar yadda wasu ke yadawa ba.