Yadda ’yan sandan Indiya suka tura giwaye suka fatattaki mazauna gandun daji

’Yan sandan kasar Indiya sun dauki wani mataki na-daban wajen tura giwaye su fatattaki daruruwan mutanen da ke zaune ba bisa ka’ida ba a gandun daji, wani daji da aka kebe a wata karkara da ke Arewa maso gabashin kasar. ’Yan sandan sun yi amfani da motocin rusau da giwaye wajen tursasa mazaunan gandun daji […]

Yadda ’yan sandan Indiya suka tura giwaye suka fatattaki mazauna gandun daji

’Yan sandan kasar Indiya sun dauki wani mataki na-daban wajen tura giwaye su fatattaki daruruwan mutanen da ke zaune ba bisa ka’ida ba a gandun daji, wani daji da aka kebe a wata karkara da ke Arewa maso gabashin kasar.

’Yan sandan sun yi amfani da motocin rusau da giwaye wajen tursasa mazaunan gandun daji su bar wurrin, yayin da su kuma suka rika jifa da duwatsu.

Kwamishinan ’yan sanda Hiren Nath ya ce an raunata mutum biyar daga cikin masu zanga-zangar, a artabun da ’yan sandan suka yi da su, har suka harba musu barkonon tsohuwa, a gandun dajin Amsang da ke Jihar Asam a ranar Litinin din da ta gabata.

Hukumomi dai sun shirrya rusa gidajen katakai da bukoki dubu.

Ministan kula da gandun daji Pramilla Brahma ya ce wurin (da aka fatattaki mutanen) muhallin zaman giwaye ne, kuma an haramta wa mutane zama a wurin, duk da haka suka tursasa wa giwayen pachyderms bazama wajen neman abinci. An samu irin wannan tashin tashin hankali da dama, inda giwayen dajin suka afka wa kauyuka, inda suka lalata amfanin gona, har ma sun halaka mutane.