Yadda ’yan siyasa ke kawo matsala ga aikin jarida – Musa Waziri Hardawa

Alhaji Musa Waziri Hardawa yana daya daga cikin fitattun ’yan jaridar da suka yi suna a Najeriya, tsohon ma’aikacin Rediyon Tarayya na Kaduna, ana iya cewa shi ya fito da mashahurin shirin nan na Jakar Magori. A tattauwarsu da wakilinmu ya yi fashin baki kan halayen ’yan siyasa da ke kawo matsala ga aikin jarida […]

Yadda ’yan siyasa ke kawo matsala ga aikin jarida – Musa Waziri Hardawa
Yadda ’yan siyasa ke kawo matsala ga aikin jarida – Musa Waziri Hardawa

Alhaji Musa Waziri Hardawa yana daya daga cikin fitattun ’yan jaridar da suka yi suna a Najeriya, tsohon ma’aikacin Rediyon Tarayya na Kaduna, ana iya cewa shi ya fito da mashahurin shirin nan na Jakar Magori. A tattauwarsu da wakilinmu ya yi fashin baki kan halayen ’yan siyasa da ke kawo matsala ga aikin jarida a Najeriya:

Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?
Sunana Alhaji Musa Waziri Hardawa an haife ni a garin Hardawa da ke karamar Hukumar Misau, Jihar Bauchi a 1954. Na fara makaranta a firamaren Hardawa a 1961 daga nan na zarce zuwa makarantar sakandaren Azare a 1968 na gama a 1972 a watan Disamba. Daga nan sai na fara aiki da kamfanin jiragen sama da ke Zariya daga bisani na nemi a sauya min wurin aiki sai aka dawo da ni Bauchi. Ban jima ba sai aka tura ni Kwalejin Horar da Ma’aikata da ke Potiskum a Jihar Yobe. Ina can sai aka bude makarantar kimiyya da fasaha ta Bauchi (BACAS) sai na dawo da karatu nan duk da cewa na yi shekara daya a can. Ina BACAS ne sai aka bude sabon gidan rediyon (MBC) wanda yanzu ake kira (BRC) mallakar Jihar Bauchi, da aka bude gidan rediyon sai na fara aiki a wurin. Bayan wani lokaci sai na koma gidan Rediyon Tarayya (FRCN) da ke Kaduna. Kuma a shekara ta 2005 ne na bar Rediyon Tarayya na Kaduna inda aka dawo da ni gidan rediyon Globe FM da ke Bauchi a matsayin Janar Manaja.
A shekara ta 2007 na sake komawa Rediyon Tarayya na Kaduna da Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya zamo gwamna sai ya nada ni Manajan Daraktan gidan Rediyon Jihar Bauchi (BRC).
Ina da diploma a kan aikin jarida daga Jami’ar Bayero da ke Kano, kuma na je kwasa-kwasai a wasu daga kasashen Afirka.
Yaushe ka fara aiki da gidan Rediyon Bauchi?
Na fara aiki da gidan Rediyon Bauchi a 1977 inda muka fara gabatar da shirye-shirye a gidan rediyon kuma ni ne mutum na farko wanda aka fara jin muryansa a gidan rediyon BRC wadda a da ana kiransa da BBC ne.
Da su wa kuka yi aiki a gidan rediyon tarayya na Kaduna?
Alhaji Yusuf Ladan dan Iyan Zazzau shi ne shugaban sashin labarai da al’amuran yau da kullum na gidan rediyon wanda mun yi aiki na tsawon shekaru tare. Bayan shi akwai Alhaji Hassan Suleiman da Alhaji Halilu Ahmed Getso da Ahmed Aminu da sauran mutanen da lokaci ba zai ba mu dama mu lissafo su daya bayan daya ba. Madina Dauda wacce take aiki a rediyon Muryar Amurya tana daya daga cikin wadanda muka yi aiki tare, sannan akwai abokina Habibu Tabare. Lokacin da na je gidan rediyon Kaduna an so a ba ni shirin Jakar Magori sai na ki karba. Sai aka ce me ya sa ba zan karba ba? Na ce abin da ya sa ba zan karba ba shi ne wanda yake gabatar da shirin ya iya saboda haka a bar shi ya ci gaba.
Akwai wasu sababbin shirye-shirye da aka kirkiro amma babu masu gabatarwa sai aka ba ni shirin Jihohinmu ni ne jagoran shirin na farko da kuma shirin Shafa Labari Shuni. Lokacin da muke gabatar da shirin Shafa Labari Shuni babu littattafan Hausa kamar yanzu.
Daga bisani wanda yake gabatar da shirin Jakar Magori, Ibrahim ya daina sai na ce a ba ni shirin zan ci gaba da gabatarwa. Na shafe sama da shekara 10 ina gabatar da shirin Jakar Magori a Rediyon Tarayya na Kaduna. Lokacin da Janar Ibrahim Badamasi Babangida yake Shugaban kasa mun je jihohi daban-daban domin gabatar da shirye-shirye na kai- tsaye.
Wane kalubale ka fuskanta a lokacin da kake aiki?
Hakika na fuskanci manyan kalubale da suka fara da gabatar da shirin yau da gobe a gidan rediyon Bauchi (BRC), wanda har yanzu ana ci gaba da yin shirin. Dalilin da ya sa na daina shirin shi ne na je na yi hira da Garkuwan Gombe Alhaji Sa’idu Umar Kumo sai na sa muryarsa a cikin shirin. To wannan hirar ba ta yi wa gwamnati dadi ba, Alhaji Adamu Misau shi ne Janar Manajan gidan rediyon, dukkanmu sai aka dakatar da mu daga aiki saboda wannan hira. Daga bisani aka tilasta mu da mu rubuta cewa mun ajiye aiki, amma aka dawo da Adamu Misau. Ni da Sale Amos sai muka rubuta mun ajiye aiki, a lokacin mulkin marigayi Alhaji Abubakar Tatari Ali ne Gwamnan Jihar Bauchi. Bayan haka na fuskanci matsaloli a lokacin da nake Janar Manaja a gidan rediyon Globe FM a lokacin mulkin Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu. Gwamna Mu’azu ya kira ni gidan gwamnati inda ya umarce ni na daina sa duk wani talle sai na PDP kawai a lokacin kuma Malam Isa Yuguda yana neman Gwamna a Jam’iyyar ANPP.
Sai na ce masa a gaskiya aikin jarida aiki ne da ke mukatar yin adalci ga kowa da kowa, saboda haka zan ci gaba da aikina ba tare da fifita wani bangare ba. Kuma dokokin Hukumar Zabe ta kasa (INEC), ya ba da dama ga dukkan jam’iyyu su tallata ’yan takararsu, daga nan sai Mu’azu ya ce to zan gani. Sai na masa ko yanzu na bar aiki alhamdullahi, domin na bi doka ne aka kore ni daga aiki. Ana cikin haka Ministan Watsa Labarai ya zo ziyarar aiki Jihar Bauchi, sai Gwamna Mu’azu ya kai karana wurinsa cewa na sa mutanen garin suna jifansa. Ba tare da ya gudanar da bincike ba, sai ya ba da umarnin a kore ni daga aiki. Sai daga baya aka kira ni daga ofis na Abuja me ya faru sai na fada musu sai aka ce babu wani laifi da na aikata saboda haka za a koma da ni Kaduna in ci gaba da aikina. Bayan da na koma Kaduna lokacin da aka rantsar da Malam Isa Yuguda a shekara ta 2007 sai ya nada ni a matsayin Manajan Daraktan gidan rediyon Bauchi. Da ma a kan tallar Isa Yuguda aka so kora ta daga baya aka daga ni daga gidan rediyon Globe FM.
Me ya faru ka bar BRC?
Bayan zaben shekara ta 2011 ina zaune a ofis a BRC sai aka kawo takardar labarai cewa an dana sabon shugaban gidan rediyon Bauchi, amma babu wata takarda da gwamnatin Isa Yuguda ta ba ni a rubuce, kora da hali aka yi min. Abin da ya sa aka min haka shi ne, ana ganin ina iya bakin kokarina na kwatanta adalci ga kowa da kowa. Wannan shi ya sa aka yi min kora da hali a BRC. Ni mutum ne wanda ba zan taba bari a cuci na kasa da ni ba. Akwai wani lokaci ina zaune sai Gwamna Yuguda ya kira ni a waya cewa ina ina? Sai na ce masa ina Yola ya ce kana me sai na ce masa ina aiki.
Sai ya ce aikin BRC ne ko, sai na ce a’a an kore ni daga BRC. Sai ya ce wallahi ba ya da labari amma zai bincika har zuwa wannan lokaci shiru kake ji kamar an shuka dusa. Yau shekara biyu ke nan da wasu watanni. Yanzu an bude wasu gidajen rediyo masu suna rediyon al’umma (kwamitini) kuma kudin da aka kashe wajen bude gidajen rediyon ya kai a gyara BRC, ta yadda za a saurari gidan rediyon a duk kananan hukumomi 20 na jihar. A bisa dokokin hukumar NBC, gwamnatin jiha ko ta tarayya ba ta da izinin bude gidan rediyon, sai dai su al’umma su tara kudi su bude gidan rediyonsu. Don haka ka ga yanzu dukkan gidajen rediyon da aka bude ana kiransu da BRC kawai ba kwaminiti rediyo ba. Lokacin da nake Manajan Darakta mun nemi a ba mu Naira miliyan 600 da wani abu za mu gyara BRC ta yadda za a ji tashar a duk kananan hukumomi 20 na jihar aka ki ba mu. Amma yanzu an kashe Naira miliyan 900 da wani abu wajen bude rediyon kwaminiti. NBC ta sa dole a kira gidajen rediyon da BRC Kirfi, ko BRC Ganjuwa amma ba kwaminiti rediyo ba. kungiyar manoma za su iya bude kwaminiti rediyo amma ban da gwamnati. Har yanzu Azare ba su da kwaminiti rediyo wanda ake ta yayata cewa gwamntin jiha ta bude.
Mene ne bambancin shirye-shiryen da da na yanzu da ake gabatarwa a gidan rediyon Kaduna?
Tabbas akwai bambanci tsakanin shirye-shiryen da, da na yanzu tunda aka dawo da tallace-tallace sai abubuwa suka rafa canjawa, lokacin da babu tallace-tallace babu matsalar kudi a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna. Gwamnati ta rage kudin da take bayarwa ga gidan rediyon wannan na daya daga cikin manyan matsalolin da gidajen rediyon gwamnati suke fuskanta yanzu wato karancin kudi. Babu kudin da za a sayi sababbin kayan aiki na zamani wadanda za a ji gidan rediyon a kowane sashi na Najeriya. Akwai shirye-shirye masu yawa da aka daina gabatarwa a gidan rediyon Kaduna sakamakon karancin kudi.
Mece ce matsalar ’yan jarida a Najeriya?
Babbar matsalar ’yan jarida a Najeriya ita ce da ana aikin ne don sha’awa, amma yanzu ana aikin ne saboda son abin duniya, kudi kwadayi sun yi yawa a tsakanin wasu daga cikin ’yan jarida. Lokacin da muka yi aiki a shekarun baya abin da muke bukata shi ne labari mai kyau wanda al’umma za su amfana, yanzu wasu ’yan jaridar ’yan neman kudi ne.
Mene ne sakonka ga ’yan baya masu tasowa?
Sakona ga matasa ’yan baya shi ne ya kamata ku yi aikinku tsakaninku da Allah ba tare da bambadanci ba. Matukar ka fara aikin jarida duniya za ta san ka, amma ba za ka taba yin kudi a sana’ar ba. Kullum gidan wannan jarida na Media Trust Limited yana rubuta wa a shafukan jaridunsa cewa kada ka ba da sisin kwabo ga ma’aikacinsu mun gode. Ya kamata kafafen watsa labarai na Najeriya su yi koyi da wannan kamfani.
Mene ne ra’ayinka kan abin da ke faruwa a yankin Arewa maso Gabas?
A gaskiya ba ma jin dadin abubuwan da ke faruwa a yankin Arewa maso Gabas na tashe-tashen hankula da suka yi sanadiyar hallaka dimbin rayukan jama’a. Kuma babban abin da ya haifar da haka shi ne yarda da muka yi aka raba kawunanmu. Da ma tuntuni akwai masu son raba kan ’yan Arewa inda wasu suke amfani da kabilanci da addini. Shekarun baya ana zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista, amma yanzu abubuwa sun sauya. Lokacin da Marwa Maitatsine ya kunno kai a Najeriya cikin kankanen lokaci aka gama da shi, ga shi yanzu sai tarihi. A gaskiya duk Musulmin da zai kashe mutum haka kawai to tabbas ba Musulmin kirki ba ne, ya kamata kowa ya fahimci haka.
Kana matan aure da da ’ya’ya nawa?
Ina da mata biyu da ’ya’ya goma sha biyu da jikoki kusan goma sha biyu.
Kana da sako ga wadanda suka shafe shekaru ba su ji muryarka?
Sakona shi ne ina fatar alheri ga dimbin al’ummar da suka san ni a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna kuma ina godiya, na yi zaman lafiya da mutane a dukkan wuraren da na yi aiki.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya