Yadda ’yan ta’adda suka addabi babban layin lantarkin Arewa

Babban Jami’in TCN ya ce ’yan ta’adda sun sha yin barazanar ƙwace Babbar Cibiyar wutar lantarki ta Shiroro

Yadda ’yan ta’adda suka addabi babban layin lantarkin Arewa

Mazaunan yankunan da babban lantarkin Arewacin Nijeriya da ya taso daga Shiroro zuwa Kaduna sun bayyana cewa ’yan ta’adda sun daɗe suna kai wa layukan lantarkin hari.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibril ya bayyana cewa “’yan ta’adda ɗauke muggan makamai sun mamaye yankin da aka samu matsalar wutar lantarki da ta jefa yankin Arewa cikin duhu.

“Amma hukumomin tsaro suna aiki tare da kamfanin TCN domin shawo kan lamarin,” in ji shi a lokacin da yake wa abokan aikinsa bayani.

Manyan layukan sun taso ne daga Babbar Tashar Lantarki da ke Madatsar Ruwa ta Shiroro a Jihar Neja, suka ratsa yankin Chiri da ke Karamar Hukumar Munya, zuwa Sarkin-Pawa da kuma Kafin koro a Ƙaramar Hukumar Paikoro, suka dangana har zuwa Mando a Jihar Kaduna.

Kowanne daga cikin layukan biyu yana da ƙarfin daukar megawat 600 na wuta; amma harin da ’yan ta’adda suka kai suka lalata su ya jefa jihohi 17 daga cikin 19 a yankin Arewa a cikin duhu na kimanin kwanaki 10.

Mazaunan yankunan a Jihar Neja sun bayyana cewa ’yan ta’adda sun sha kai hare-hare kan kayan lantarkin da kuma al’ummomin da ke yankin.

Al’ummar yankin Chiri waɗanda ’yan bindiga suka sha kai wa hari sun tabbatar wa wakilinmu cewa ’yan ta’adda sun sha kai wa manyan turakun lantarkin hari.

Wani basarake a yankin ya ce abin da ya sa jami’an Kamfanin Samar da Lantarki ta Nijeriya (TCN) ke ɗari-ɗari da shiga yankin shi ne, layukan wutan suna kam hanyar da ’yan ta’adda ke bi ne, kuma a kodayaushe ’yan ta’adda na iya kawo hari.

Sai dai ya ce, “Amma gaskiya an samu sauƙin hare-hare a baya-bayan nan, duk da cewa mutanen da suka yi ƙaura ba su dawo gidajensu ba.

“Abin tsoron shi ne ’yan ta’adda ba su da tabbas, a koyaushe za su iya kawo hari,” in ji basaraken wanda ta nemi a ɓoye sunansa.

Shi ma wani mazaunin yankin, Mustapha Ahmed, ya tabbatar da cewa, “An samu sauƙin hare-haren, amma babu tabbas, ’yan ta’adda za su iya kawo hari duk lokacin da suka ga dama.

Aminiya ta gano cewa ’yan ta’adda sun sha kai hare-hare a kan al’ummomin Chiri da Kuchi da ke Karamar Hukumar Munya da kuma Kafin-Koro a Ƙaramar Hukumar Paikoro, waɗanda layin wutar ya ratsa ta cikinsu.

Fargabar harin ’yan bindiga ya kawo cikas wajen aikin gyara wutar zai ɗauki tsawon lokaci.

Sai da aka kai ga shugaba Tinubu ya sa baki domin hukumomin tsaro sun taimaka wajen samar da tsaro domin Kamfanin Lantarki na Ƙasa (TCN) ya samu gyara wutar.

Ana iya tuna cewa da farko TCN ya bayyana cewa harin ’yan ta’adda ne ya lalata layin wutar na Arewa amma jami’ansa ba za su iya zuwa su gyara ba, saboda rashin tsaro kuma sun samu gargaɗi daga Ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, cewa akwai haɗari a zuwa wajen.

Janar Manaja na Kamfanin Samar da Lantarki na Ƙasa (TCN) Reshen Shiroro, Maiwada Sarkin-Bello Paiko, ya taɓa fada a shekarar 2023 cewa ’yan ta’addan sun sha barazanar kwace dam ɗin Babbar Cibiyar Wutar Lantarki ta Shiroro

Ya bayyana haka ne a lokacin wani taron kamfanin TCN na yankin Shiroro a Jihar Neja a shekarar da ta gabata.

Amma ya ce gwamnati ta ɗauki matakin tura jami’an tsaro domin hana faruwar hakan.

A lokacin ya shaida wa taron cewa duk da cewa TCN ya sabunta wasu muhimman kayan aiki a tashar ta Shiroro, amma rashin tsaro na kawo cikas ga kuma da su da ma wurin.

Ya ba da misali da lokacin da wuta ta lalace suka jami’ansu da rakiyar jami’an tsaro domin gyarawa.

“Abin takaici sai aka kai musu hari aka kashe jami’an tsaro uku,” in ji shi.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara