Yadda ‘yan ta’adda suka jefa mata cikin kuncin rayuwa a Arewa

Marubuta da dama sun yi tsokaci akan irin gudunmawar da mata iyayen giji suka jajirce wajen bayarwa wadda kuma ta kai ga samuwar wannan gwamnatin mai ci.Duba da irin gagarumar rawar da suka taka ne yasa na yi tsinkaye cikin azancin Bahaushe dake cewa dan halak ke rama biki. Watau tamkar dai a ce yaba […]

Yadda ‘yan ta’adda suka jefa mata cikin kuncin rayuwa a Arewa
Yadda ‘yan ta’adda suka jefa mata cikin kuncin rayuwa a Arewa

Marubuta da dama sun yi tsokaci akan irin gudunmawar da mata iyayen giji suka jajirce wajen bayarwa wadda kuma ta kai ga samuwar wannan gwamnatin mai ci.
Duba da irin gagarumar rawar da suka taka ne yasa na yi tsinkaye cikin azancin Bahaushe dake cewa dan halak ke rama biki. Watau tamkar dai a ce yaba kyauta, tukuici!
Duk inda ni ken a kan yi tsokaci kan irin mawuyacin halin da iyaye mata kan tsinci kan su dazarar sun samu juna biyu wanda ke zama babbar barazana a rayuwarsu dungurungum. Mun kuma shawarci mahukunta da su rama bikin da matan nan su kai musu ta hanyar kyautata harkar lafiya domin kubutar da rayukan dubban masu juna biyun da ke cikin yanayi na garari sakamokon nauyin da su ke dauke da shi na halittar dake cikin su.
Zan so maida hankali ne akan wani bangaren dake nuna irin halin rayuwa da dubban mata da yara suka tsinci kan su a ciki ta sanadiyyar musibar guguwar tarnakin Boko Haram.
Ya shahara cewa tun bayan gawurtar wannan iftila’i dubunnan rayuka sun salwanta, wasu dubunnan sun samu nakasa, walau ta dukiya ko ta jiki. Wani karin damuwa ma shine yadda wasu da dama kuma Allah Shi kadai ya barma kan Sa sani dangane da irin illar da al’amarin ya haifar mu su a kwakwalwa wanda akasari haka wannan miki zai kasance tare da su cikin dare ko rana, a farke ko cikin barci har illa ma sha Allahu.
Manta wata fitinar ba abu ne mai sauki ba, musamman agun wanda ya ziyarci daruruwan wadanda wannan abu ya rutsa da su.
Akan wannan ne zan so in kulle rubutun nan da igiyar da na tufko da ziyar gani da ido wadda na yi tsawon mako guda akarkashin gayyatar wata baiwar Allah, baturiyar New Zealand wadda ke jagorantar gidauniyar Lobatt Foundation.
Hakika na zaune bai ga rayuwa ba. Zagayawa cikin al’umma ba karamar hanyar samun sahihin hoton rayuwar da ake ciki bane a yau da jiya.
A yayin wannan zagaye Allah ya bani ikon ganawa da mata daban-daban wadanda iftala’in rikicin Boko Haram ya rutsa da su. Na ga yadda wannan fitina ta tarwatsa gidaje, ta yanke da daga nonon mahaifiyar shi badan ta so ba, badon ta shirya ba. Na ga dan da maman shi ta yi tafiyar kilo mita 400 a kafa har nakuda ta riske ta a hanya ta haife shi ba tare da ta samu rahamar ganin fuskar sa ba ballantana ma ta san me ta haifa.
Idan aka ce min ga wani namijin da yai tafiyar kilo mita sama da dari shida (600) a kafa to da hakika na yi mamaki, amma sai gashi na iske matar da ta share wannan milamilan tafiyar a kafa cikin tsananin tashin hankali. Wata matar ma ga nauyin ciki, ga goyon yaro sannan ga wasu yaran a hannu tana janye da su tun daga Baga, Goza, Mubi, ko Damataru. Wadannan sune suka fi cancanta da a kalle su a matsayin gwaraza, bawai wani daya niki gari ba don kawai nishadin samun falalar al’umma ko dansiyasa ba.
Baka ga abin tausayi ba sai ka dubi fuskar yarinyar da bata taba ganin fuskar mahaifinta ko mahaifiya ba. Wasu da dama an tsinka igiyar da ta kulla su da mazajen su, dayawa kuma har abada an rabu kenan. Za ka ga wasu babu iyaye sannan babu mazajen, duk sun salwanta sakamakon wannan musiba. Guguwa ce mai keta alfarmar masu alfarma. Rugugin da ya tarwatsa masoya ya raba kusancin masu kusaci.
Wata yarinya da na gani dududu shekarun ta baza su wuce sha bakwai ba. A garin gudun neman tsira aka harbe ta a cinya. A haka ta kokarta ta sha da kyar kamar yadda abokan gudun hijirarta suka gaya min. Ga yarinta ga tsohon ciki haka suka gurguro da ita har garin Kano tun daga Baga.
A ranar da suka iso a sannan Allah ya nufe ta da haihuwar budurwar da zata taso nan gaba ta iske labarin yadda mahaifinta ya rasa rayuwarsa wajen kokarin kubutar da matarshi (mahaifiyarta) da ke dauke da tsohon cikinta.
An samu wadda a cikin daji nakuda ta zo mata, haka abokan tafiyar suka shinge ta har ta sauka cikin wani yanayi mai tada hankali.
Ilimin dubban yara ya yanke, kasuwancin iyayen su ya tsinke, amincin da da suke lullube a cikin sa shima ya gushe. An raba mata da miji, yara da uba, ko uwa da yaranta. Wannan duk ya rutsa da dubban mata da yara.
Malam Abdullahi Abubakar Dean malami ne a Jami’ar Bayero Kano.