Yadda ’yan ta’adda suka kashe masu gaisuwar ta’aziyya 30 a Katsina
’Yan ta’ddan sun yi wa mutanen kwanton ɓauna ne sannan suma yi musu kisan gilla a Ƙaramar Hukumar Batasri
’Yan bindiga sun kashe masu gaisuwar ta’aziyya kimanin 30 a ƙauyen Baure da ke Ƙaramar Hukumar Batasri a Jihar Katsina.
Masu gaisuwar ta’aziyya ciki har da ’yan banga, suna hanyarsu ta komawa gida ne ’yan ta’addan suka kai musu harin kwanton ɓauna inda nan take mutum 15 suka ce ga garinku nan.
Shaidu sun bayyana cewa mutanen da harin ya rutsa da su sun je ta’aziyyar ne daga ƙauyukan ƙananan hukumomin Safana da Kurfi da Charanchi da Kaita.
Sun shaida wa Aminiya cewa mutum sama da 30 ’yan bindigar suka kasa harin na yankin Ɓaure, wanda ya yi ƙaurin suna da ayyukan ’yan bindiga, tun ranar Talata amma sai ranar Alhamis aka samu labarin.
Wani mazaunin ƙauyen Barebari a Ƙaramar Hukumar Safana ya shaida wa wakilinmu cewa aƙalla mutum 15 ne suma mutu a lokacin da maharan suka buɗe musu wuta.
Ya ce, “Ƙauyen Ɓaure sanannen matattarar ’yan bindiga ne. Su ke iko da yankin, kuma ranar kasuwa ce, suka bi mutane inda suka kashe, yanzu mun gano gawarwaki 15. Sun ƙona wasu gawarwaki, wasu kuma har yanzu ba a gan su ba. Da da farko ma hana a ɗauki gawarwaki suka yi, amma daga baya suka bari.”
Shi kuma wani ya ce, “mun yi nasarar ceto mutane sama da 20, daga ƙauyukan Burji da Charanci da Jibiya da Kaita. Aƙalla mutum 25 aka tabbatar sun mutu, wasu da dama kuma ba a gan su ba.”
Wani wanda ya ce an kashe ɗan uwansa a harin ya ce, daga cikin mamatan har da ’yan banga.
Ya ce, “’yan bangan ba su san cewa ’yan bindiga suna cikin ƙauyen ba. Da ganin su sai ’yan bindigar suka shige gidajen mutane suka ɓoye, suka buɗe musu wuta, suka kashe aƙalla mutum 30.
“Ɗan ɗan uwana na cikin waɗanda aka kashe, sai yau (Alhamis) bayan kwana biyu muka iya ɗauko gawarwakin. Mamatan ’yan banga ne daga ƙananan hukumomi daban-daban da suka je gaisuwa ta’azyyar ɗaya daga cikinsu da ya rasu a ƙauyen Madaddafai,” in ji shi.
Ya ce bayan ta’aziyyar shugabanninsu sun wuce gida, amma wasu suka yanke shawarar zuwa Ɓaure, inda a nan aka yi musu kwanton ɓauna aka halaka su.
Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar da harin, amma ta ce tana ci gaba da tattara bayanai, kamar yadda kakakinsa, Abubakar Sadiq Aliyu ya shaida wa wakilinmu.