Yadda ’yan takarar shugaban kasa za su magance matsalar tsaro
Sun bayyana haka ne a taron muhawarar da aka shirya musu, aka kuma tambaye su yadda za su magance matsalar tsaro da ke ci wa Najeriya tuwa a kwarya
Manyan ’yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 sun bayanin yadda za su magance matsalar tsaro a Najeriya idan suka hau mulki.
Dan takarar Jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP da kuma Abdulateef Kola Abiola na PRP sun bayyana da matakan da za su dauka wajen magance matsalar tsaro da ta dabaibaye kasar.
- Akwai kararrakin zaben fidda gwani 600 a gaban kotu —INEC
- Matsalar Tsaro: Dalilin da muke neman hadin kan kasashe —CDI
Sun bayyana alkawuran ne a taron muhawarar ’yan takarar shugaban kasa, inda aka tambayi kowannesu abin da zai yi wajen magance matsalar tsaro, bisa la’akari da harin jirgin kasan Abuja-Kaduna, wanda aka yi garkuwa da mutum 60.
Cibiyar Cigaban Dimokuradiyya (CDD) ce ta shirya taron muhawarar da hadin gwiwar tashar talabijin ta Arise da Daily Trust da Premium Times da kawayensu.
Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu bai halarci taron ba, takwaransa na PDP, Atiku Abubakar kuma ya samu wakilcin abokin takararsa, Ifeanyi Okowa.
Kwankwanso:
Sauya fasali da kara jami’an tsaro
Da yake bayani, Kwankwaso ya ce, mataki na farko shi ne sauya fasalin tsaron Najeriya da kuma kara yawan jami’an tsaro, ta yadda yawan sojojin Najeriya zai haura miliyan daya.
A cewarsa, hakan zai ba su damar yin sintirin samar da tsaro a kowane lungu da son kasar.
Ya shaida wa taron cewa, “A matsayina na tsohon ministan tsaro, ina tabbatar muku cewa da wannan (harin) bai faru ba, amma yanzu sojoji da ’yan sanda 250,000 da ’yan kai da muke da su sun yi kadan matuka.
“Abin da zan yi shi ne kara yawan sojojin su haura miliyan daya, wanda na tabbata idan aka yi hakan za mu kwace ikon kowane taki da ke fadin kasar nan.”
Atiku:
Hadin gwiwa da kafa ’yan sandan jihohi
A nasa bangaren, Atiku na jam’iyyar PDP ya ce amfani da tsarin tara bayanan sirri na bai-daya da kuma aiwatar da hakan shi ne mafita.
Ya ce hakan zai yi nasara ne “ta aiwatar da tsarin ta yadda hukumomin tsaro za su rika bai wa juna bayanan sirri tare da yin aiki tare domin kare kasa.”
A cewarsa, a halin yanzu ba a yin haka a tsakanin hukumomin, shi ya sa ya yi alkawarin tabbatar da ganin hukumomin tsaron kasar nan suna aiki kafada-da-kafada.
Ya ce, “Dole kuma a sauya tsarin aikin dan sanda ta yadda za a kafa ’yan sandan jihohi wanda zai bai wa gwamnatocin jihohin damar samu da kuma gudanar da ’yan sandansu.”
Peter Obi:
Inganta binciken sirri da samar da ayyuka
Da yake amsa tambayar, dan takarar shugaban kasa Peter Obi ya ce idan aka zabe shi zai bunkasa tsarin tarawa da kuma amfani da bayanan sirri.
“A yau kashi 35 na marasa aiki a kasar nan matasa ne. Babu yadda za a yi kashi 60 na matasa masu jini a jika a kasa suna zaman kashe wando kuma a zauna lafiya.
“Abin yi shi ne samar da ayyukan yi da kananan sana’oi a yankunansu domin tallafa wa rayuwarsu da kuma fitar da su daga kangin talauci,” in ji dan takarar.
Kola Abiola:
Sauya fasalin tsaro
A nasa bangaren, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PRP, Kola Abiola ya ce abu mafi muhimmanci shi ne yin gyara a fasalin tsaron kasa.
“An yi shekaru ana kiraye-kirayen neman yin garambawul ga tsarin tsaron kasar nan domin kara masa inganci.
“Idan aka hade sojoji su yi aiki tare da DSS da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro, za a samu jami’an tsaro 800,000 zuwa 900,000, wanda shi ne abin da ya kamata a yi.”