Yadda ’yan tsibirin Hawaii suka yi hajjin bana

Yadda ’yan tsibirin Hawaii suka yi hajjin bana   Mutan e daga ko’ina a fadin  duniya na ziyarar birnin Makkah a kasar Saudiyya don sauke farallin aikin Hajji, inda a bana aka samu wasu iyalai daga kasar Hawaii da suka shafe kilomita dubu 15 don cika burinsu na zuwa aikin hajjin bana. Mutumin dan asalin […]

Yadda ’yan tsibirin Hawaii suka yi hajjin bana

Yadda ’yan tsibirin Hawaii suka yi hajjin bana

 

Mutan e daga ko’ina a fadin  duniya na ziyarar birnin Makkah a kasar Saudiyya don sauke farallin aikin Hajji, inda a bana aka samu wasu iyalai daga kasar Hawaii da suka shafe kilomita dubu 15 don cika burinsu na zuwa aikin hajjin bana.

Mutumin dan asalin Amurka da matarsa ’yar Indonesiya Andhini da ’ya’yansu mata biyu, wadanda shekarunsu suka kama daga 13 zuwa 15 sun shafe sa’ao’i 26 suna tafiya a jirgin sama, har da shiga mota sannan suka isa birnin Makkah.

“A hakikanin lamarin aikin hajji,  mu alhazai ne,” a cewar Galliban lokacin  da yake dariya, domin “shekaru daruruwa da suka gabata, alhazai kan yi tafiya a kasa da jirgin ruwa na tsawon  watanni. Don haka ba sabon abu ba ne a yi tafiya mai  nisan  zango.”

Uwargida Andhini, wadda malamar makaranta ce, ta ce ta shafe watanni “tana kimtsa kanta,” saboda wannan tafiya zuwa aikin hajji, mai inganta karfin jiki da ruhi.

Ta yi watani tana kwatanta tafiya a kasa.

“Ina da tabbacin  cewa na yarda da abin da zuciyata ta kudure,” inji ta. “Na dade ina jiran wanan rana tsawon shekaru. Na yi kuka lokacin da na samu gayyata. Babban farin cikin lamarin shi ne tafiya tare da ’ya’yana.

Shi kuwa Galliban wanda tuni ya yi ritaya daga aikin gwamnati cewa ya yi: “Aikin Hajji ba hutu ba ne, inganta ruhi ne kuma kira ne na kawar wa mutun son duniyta, don kasancewa tare Allah.”

“’Ya’yana mata ba su taba yin irin wannan tafiyar ba, amma saboda na yi a shekarar da ta gabata sai na samun kwarin gwiwar cerwa za su iya, sai muka taho tare,” a cewarsa.

Na samu izinin shiga Saudiyya daga adadin mnahajjatan da aka ware wa Amurkawa, don haka iyalan Galliban za su shafe kwanaki 16 a tsakanin Makkah da Madina.

Kamfanin jigilar mahajjata na Sara International ne ya kai su kasa mai tsarki. Kuma shugaban kanan kamfani Mohammad Sattaur ya ce bana an smau dimbin mutane da suka yi fafutikar ganin sun yi wanan tafiya daga yankin Karibiyan da Amurka.

An kiyasta kalla mutum miliyan biyu ne suka halarci aikin hajjin bana. Kuma alhazan kasar Iran da ba su halarta a bara ba, bana sun isa kasar Saudiya don aikin hajjin bana.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista