Yadda yaro dan shekara 15 ya kera tifa a Akwa Ibom
Wani matashi dan shekara 15 mai suna Hope Emmanuel Frank ya kera motar tifa a jihar Akwa Ibom ta hanyar yin amfani da katako. Matashin ya yi nasarar kera motar tifa ta hanyar yin amfani da katako, tsofaffin baturan kwamfuta laptop. Zantawar su da Aminiya Hope Emmanuel ya ce babban burin da yasa a gaba […]
Wani matashi dan shekara 15 mai suna Hope Emmanuel Frank ya kera motar tifa a jihar Akwa Ibom ta hanyar yin amfani da katako.
Matashin ya yi nasarar kera motar tifa ta hanyar yin amfani da katako, tsofaffin baturan kwamfuta laptop.
Zantawar su da Aminiya Hope Emmanuel ya ce babban burin da yasa a gaba shi ne ya zama ya shahara a duniya wajen kere-keren motoci da sauran kayan hada motoci. Ya ce, aikin ya dauke shi zuwa wani lokaci tunda sai ya dawo daga wasu harkokin sa da kuma makaranta yake samun sukunin zama ya yi aikin a natse.
Wakilin mu ya tambayeshi ko mai ya jawo hankalinsa ya bashi sha’awar fara kere-kere? sai ya ce, “Tun daga lokacin da na fara ganin motar haka rami da tifa, na ji ina sha’awar son in kera ta to amma na rasa ta yadda zan bullowa lamarin na fara tunanin ma ta yaya zan yi har motar inga ta na tafiya idan na kera ? wadanna na daga cikin irin tunanin da na rika yi”, in ji shi.
Hope Frank, ya ci gaba da yin bayani “To daga nan sai na fara tunanin in fara yin amfani da sirinjin allura a madadin robar da take kai man da ke sanya ta motsa kamar yadda motar haka rami ke dashi.”
Da Aminiya ta tambayeshi ko yaya ya rika kwashewa da mutane idan ya fito kan titi yana jaraba yadda motar zata rika yin aiki sai ya ce, “mamaki abin ya rika ba mutane mamaki musamman idan suka ga na fito ina sarrafa motar tona ramin da kuma tifa wasu suyi mini dariya wasu kuma su kara mini kwarin gwiwa”, in ji matashin.
Ta yaya ma aka yi harka fara wannan kirkira? sai ya kara da cewa, “Karon farko da naga irin wannan mota sai na fara tunanin yadda zan yi ta har ta yi tafiya sai na fara tunanin yin amfani da zare da kuma robar sirinji”.
Ta yaya aka yi ma har motar ta fara sarrafuwa? Ina amfani da tsofaffin baturan kwamfuta laptop da aka dena amfani da su ne na rika aiki, nasa yadda zata rika yin baya da kuma gaba idan ta dauko kaya har ta juye a kasa”.
Da wakilin mu tambaye shi burin sa a rayuwa? Hope Emmanuel frank ya ce, “Ina so nima in yi suna kamar yadda kamfunan da suka kera tantan da motoci irin na tona rami, da tifa da kamfanonin Benjamin Franklin, da Graham Bells Thomas Edison suka yi suka kirkiro wutar lantarki.”
Sannan ina da burin nan gaba kadan in kera motar zuba kaya da kuma jirgi mai saukar angulu”. Matashin ya sha alwashin bunkasa harkar kere -kere musamman idan zai samu tallafi daga gwamnatin Jihar Akwa Ibom ko kuma wata kungiya domin ya kama harkar sosai.