Yadda yunkurin samar da kudin Eco ke kawo fargaba

Bayan shafe tsawon lokaci, kasashen Afirka ta Yamma a karkashin Kungiyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma (ECOWAS) na tattaunawa kan yadda za su samar da kudin bai-daya domin amfaninsu, har yanzu akwai fargaba kan fara amfani da kudin bai-daya na Eco da suka samar, kamar yadda Sashin Hausa na BBC ya ruwaito. Ya ce […]

Yadda yunkurin samar da kudin Eco ke kawo fargaba

Shugaba Buhari da takwarorinsa na Afirka ta Yamma a wani taro kan kuxin na Eco

Bayan shafe tsawon lokaci, kasashen Afirka ta Yamma a karkashin Kungiyar Tattalin Arziki ta Afirka ta Yamma (ECOWAS) na tattaunawa kan yadda za su samar da kudin bai-daya domin amfaninsu, har yanzu akwai fargaba kan fara amfani da kudin bai-daya na Eco da suka samar, kamar yadda Sashin Hausa na BBC ya ruwaito.

Ya ce tuni wasu daga cikin kasashen suka amince su fara amfani da kudin Eco daga bana, sai dai daga Gwamnatin Najeriya ta bukaci a jinkirta kaddamar da kudin na bai- daya. Najeriya ta ce ta bukaci haka ne saboda akasarin kasashen ba su cika ka’idojin da aka gindaya ba wanda ta ce akwai bukatar a dage lokacin kaddamar da kudin.

Gidan rediyon ya ce a bara ce Kungiyar ECOWAS ta ce ta tsara samar da kudin bai-daya na Eco don fara aiki da shi a bana.

Gwamnatin Najeriya ta ce kasar Togo ce kadai daga Yammacin Afirka ta cika dukkan ka’idojin shiga tsarin kudin na bai-daya.

Kasashen Afirka ta Yamma 15 ne suka amince su fara amfani da kudin na Eco da suka hada da Benin da Burkina Faso da Guinea-Bissau da Ibory Coast da Mali da Nijar. Sai kasashen Senegal da Togo da Saliyo da Liberia da Najeriya da Gambiya da Guinea Conakry da Cape Berde da kuma Ghana.

An fara maganar amfani da Eco tun a shekarar 2000, sai dai an jinkirta batun tare da yin kwan-gaba-kwan-baya, sai a bara da Shugaban Cote d’Iboire, Alassane Ouattara ya sanar da matakin kasashe takwas rainon Faransa da kuma kasar Faransa da suka amince da sauya kudin da suke amfani da shi wato CFA (Sefa) zuwa ECO.

Sanarwar da aka yi a watan Disamban bara, ta zo da ba-zata musamman ga wasu kasashen yankunan.

Kasashen yammacin Afirka 15 sun amince da sunan ECO ne a wani taro da suka gudanar a watan Yunin 2019.

A wata tattaunawa da Sashin Hausa na BBC, wani masanin tattalin arziki kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Mista Obadia Mailafiya ya ce “Eco kudi ne da gwamnatin Faransa da shugabannin kasashe rainon Faransa da ke Afirka ta Yamma irin su Code d’Iboire da Togo da Mali da Nijar da wasu kasashen suka kulla yarjejeniyar kafa sabon kudi “Eco”.

Mailafiya ya ce kudin Eco zai maye gurbin CFA da a baya kasashen rainon Faransa ke amfani da shi. “Ita Faransa ta dauki nauyin ba da tabbaci na wannan kudi a duniya baki daya.” A cewar Mailafiya, an kirkiri kudin ne domin an dade ana amfani da CFA tun 1945 kuma a Paris ake buga kudin, sannan gwamnatin Faransa ce ta dauki nauyin lura da asusun dukkan kasashen. “An duba cewa kasashen ECOWAS suna son su hada kudadensu da na kasashe rainon Faransa don a samun kudin bai-daya.” inji Mailafiya.

Ya ce an jima kasashen na tattauna hanyoyin da za su cimma wannan tsari saboda “kasashe rainon Ingila kamar Najeriya da Ghana da Saliyo da Gambiya da Liberia suna tattauna yadda za su kafa nasu kudin.” A watan Disamban bara ne, Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Alassane Ouattara suka sanar da cewa za su kafa kudin Eco kuma idan sauran kasashen suna da sha’awa za su iya zuwa su hada kai domin samar da kudin.

Daga baya Ghana ta amince cewa za ta shiga cikin gamayyar, amma Najeriya ta ce ba ta amince ba sannan za ta ci gaba da tattaunawa domin ganin yadda za ta bullo wa lamarin.

Mene ne alfanun kudin Eco

Kudin Eco yana da matukar alfanu ta bangare da dama, a cewar Farfesa Kabiru Isa Dandago wani masanin tattalin arziki da ke koyarwa a Jami’ar Bayero ta Kano. Ya kuma bayyana hanyoyin da za a samu alfanu kamar haka:

  1. Bunkasa cinikayya

Farfesa Dandago ya ce “Wannan tsari yana da alfanu ga ’yan kasuwa ta kowane bangare. Da farko ’yan kasuwar Afirka ta Yamma suna da damar shiga kasashen 15 ba tare da sun je ofishin jakadancinsu sun karbi biza ba.”

“Idan ma za a yi musu bizar zai zamana biza ce idan aka zo shiga cikin kasar, abin da ake so kawai mutum ya samu shaidar tafiye-tafiye a tsakanin kasashen wato fasfo.” inji Farfesa Dandago.

Kudin Eco kuma zai kawo karshen rashin daidaiton da ake fama da shi a yankin da kuma ci gaba a fannin tattalin arzikinsa saboda yanzu kasashen Afirka ta Yamma za su rika kallon dukkan kasashen ne idan za su samar da kaya domin amfaninsu.

  1. Ci gaba ga masu sana’ar canjin kudade

Ga masu sana’ar canjin kudade, su ma hada-hadar cinikayyarsu za ta bunkasa domin za su rika kokarin yin canji tsakanin kudin Eco da kudaden kasashen Turai da sauran kudaden kasashen duniya kamar yadda masanin ya fada. Hakan a cewarsa, zai sa kasashen Afirka su bunkasa su kuma yi kokarin kamo sauran kasashe da suka ci gaba ta fuskar tattalin arziki.

  1. Raguwar hauhawar farashi

Farfesa Dandago ya ce idan har aka samu daidaito a batun kudin na Eco sannan aka fara amfani da kudin yadda ya kamata, hakan zai haifar da raguwar farashin kayayyaki saboda kudin zai saukaka harkokin kasuwanci ta fuskoki da dama. Gwamnatocin kasashen ba za su samu damar yin amfani da hauhawar farashin kayayyaki ba wajen cike gibin da aka samu a kasafin kudinsu.

  1. Fatara da talauci za su yi kasa

Tsarin kudin Eco zai taimaka wa kasashen da ba su da karfin arziki kamar Saliyo wadda ake kallo a matsayin karamar kasa da ke dogara kan wasu kasashen wajen samun abinci.

  1. Samar da ayyukan yi

Hada-hadar cinikayyar da za a yi za ta taimaka wajen samar wa mutane ayyukan yi da za su taimaka musu su tsaya da kafarsu saboda tsarin zai samar da karuwar kasuwanci ga ’yan kasuwa tare da ba da damar fitar da kayayyakia  tsakanin kasashen. Ya ce samun wannan zai sa dan kasuwa ya shiga a dama da shi a kasashen saboda ana sa ran “kudin zai samu a wata cibiya daya kamar babban banki wanda zai rika ba da kudaden ga bankunan da suke kasashen 15, kuma a rika bayarwa ga ’yan kasuwa domin cinikayya.”

  1. Samar da hadin kai

A cewar wani malami a Sashin Tattalin Arziki a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe, Dokta Mustapha Kabara ya ce “Kasashen Yammacin Afirka za su zama suna magana da murya daya ta yadda duk wata barazanar tattalin arziki da ga kasashen da ba sa cikin tsarin kamar kasashen Turai da Amurka ba za ta yi musu illa ba.”

Zai kasance ba komai kasashen Yamma za su gabatar wa kasashen Yammacin Afirka zai samu karbuwa ba saboda suna da hadin kai da tsarin tattalin arziki kuma suna magana da murya daya. Sai dai duk abin da yake da alfanu yana da akasinsa kuma masana na ganin akwai kalubale idan har aka fara amfani da wannan kudi na bai-daya a tsakanin kasashen yankin. Kasashen za su rasa ikon da suke da shi kan kasashensu musamman ta bangaren tattalin arziki kamar fito da kayyade adadin kudin ruwa.

Duk da kananan kasashe za su samu habaka a tattalin arzikinsu, alfanun tsarin zai fi yin tasiri kan kasashen da suke da karfin tattalin arziki. Sai kuma bambancin harshe a tsakanin kasashen rainon Ingila da na Faransa na iya shafar zirga-zirgar ma’aikata sannan  zai iya ta’azzara matsalar rashin ayyukan yi musamman a kasashen da suke da karamin karfi.

Ra’ayin wadansu jama’ar kasashen

Wani mai sana’ar canjin kudade Abdulhadi Rabi’u Kura ya bayyana wa Sashin Hausa na BBC cewa “tsarin ci gaba ne saboda mutum zai dauki kudi zuwa kasashen ba tare da fargabar samun canji ba.” Ya kara da cewa matakin zai sa kudin ya yi karfi har kasashen duniya su rika mu’amala da shi.

A cewarsa “Abin dubawa shi ne da kasashen Turai suka yi irin wannan tsari har suka samar da Euro wane irin ci gaba aka ga an samu a tattare da su.”

Ya ce Ingila ta yi hikima saboda “ba ta yarda ta soke kudinta ba kamar yadda Jamus da Italiya suka soke nasu.” Ya yi fatar Najeriya ma ba za ta soke nata kudin ba “ta yi irin na Ingila don ganin yadda tsarin zai kasance.”

Ita ma Jamila da ga Ghana cewa ta yi tsarin kudin na Eco zai taimaka wa ’yan kasashen da suke kasuwanci su gudanar da kasuwancinsu ba tare da wata fargaba ba. “Idan ka yi tafiya ka je wani gari ba sai ka canja kudi don yin ciniki ba” inji ta.

Shi kuwa Abdulbasit Ibrahim a Abuja, Babban Birnin Najeriya, yana ganin “Ba za a samu wani alfanu ba daga tsarin saboda akasarin kayayyakin da suke samar da ci gaba na karkashin ikon kasuwannin duniya ne.” Ya kara da cewa tsarin kamar wani abu ne da zai dauke hankali amma idan shugabannin suka yi abin da ya kamata, tsarin zai kawo karshen hauhawar farashin kaya.”

Makomar Eco

Obadia Mailafiya ya ce tun a baya kasashen Faransa da na Afirka ta Yamma suna amfani da CFA kuma abin ya kara karfafa tattalin arzikinsu, ya sa kudinsu yana da dan karfi a sha’anin kasuwancin duniya.” A ganinsa, idan har aka sasanta da kyau, kudin na Eco yana iya taimakawa wajen karfafa tattalin arzikin kasashen da za su yi amfani da shi.

Sai dai ya ce abin damuwar shi ne yadda aka zo aka kafa kudin ba tare da an sasanta da Najeriya da sauran kasashen rainon Ingila ba inda masanin ya ce zai iya kawo cikas. “Faransa ta ce ta ba da tabbaci kan kudin na Eco, sai dai ba mu san ko Najeriya za ta amince ko ba za ta amince ba.” Ya ce idan har aka bi sha’anin da kyau kuma har Najeriya da sauran kasashe renon Ingila a yankin Afirka ta yamma suka amince, za su iya hada kai da sauran kasashe renon Faransa har a samar da Eco.

Ya ce yin hakan zai taimaka sosai a sha’anin kasuwanci da karfafuwar tattalin arziki.

“Amma sai an bi abin a hankali, an samu ra’ayin kowa da kowa kuma kowa ya amince da abin da ya kamata a yi da matakan da ya kamata a dauka domin a samu ci gaba a Afirka ta Yamma gaba daya,” inji Mailafiya.

 

Rahoto daga Sashin Hausa na BBC