Yadda za a biya matasa tallafin Naira dubu biyar – Lai Muhammad
A ranar Talatar da ta gabata ce Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammad ya kawo wa Aminiya ziyara a ofishinta da ke Abuja, a yayin wannan ziyarar Aminiya ta zanta da shi kamar haka: Aminiya: Mai girma Minista a matsayinka na kakakin gwamnati, a lokacin yakin neman zabe kun yi alkawarin bayar da Naira dubu […]

A ranar Talatar da ta gabata ce Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammad ya kawo wa Aminiya ziyara a ofishinta da ke Abuja, a yayin wannan ziyarar Aminiya ta zanta da shi kamar haka:
Aminiya: Mai girma Minista a matsayinka na kakakin gwamnati, a lokacin yakin neman zabe kun yi alkawarin bayar da Naira dubu biyar-biyar ga marasa aiki. Muna son sanin hanyoyin da za ku bi wajen biyan wadannan kudi na wata-wata, kuma yaushe za a fara biya?
Lai Mohammed: Abin da ke faruwa akwai ganawa a gobe (Talatar da ta gabata) a ofishin Mataimakin Shugaban kasa inda za a fito da tsarin yadda za a gudanar da shirin ta hanyar hada hannu da wata hukuma ta Majalisar dinkin Duniya. Wannan tsari ana gudanar da shi a wasu jihohi, ina jin wasu jihohin Arewa maso Yamma suna biya bisa wani sharadi na bashi tare da karancin abin da kake so ka yi. Ina da yakinin ta yin aiki da jihohi da kananan hukumomi za mu samu saukin gano wadanda muke ganin su ne suka dace su ci gajiyar wannan tallafin kudi. Sai dai ina ganin mutane suna mancewa da wasu tallafi a fannonin rayuwa wadanda da muka yi alkawarin biyan Naira biliyan 500 domin bayar da bashi ga mata ’yan kasuwa da masu sana’a’o’i da makada da mawaka da wadanda suka kammala makaranta ba su da aikin yi. Amma wannan za a yi ne ta hanyar kungoyoyin gama-kai, domin an lura kudin da aka bayar rance ta hanyar kungiyoyin gama-kai an fi maido da su a kan na daidaikun mutane. Kuma gwamnatin ta yi alkawarin daukar wadanda suka kammala makaranta rabin miliyan a horar da su a matsayin malaman makaranta a duk sassan kasar nan. Wadannan suna daga cikin tallafin inganta rayuwa da wannan gwamnati ta yi niyyar aiwatarwa.
Aminiya: Har yanzu kan wannan batu, ko akwai adadin lokacin da mutum zai dauka yana karba idan aka fara biyan wannan tallafi?
Lai Mohammed: Wadannan suna daga cikin abubuwan da muke aiki a kansu a cikin kwamitin, kamar yadda na fada muna son mu ga yadda shirin ya gudana a sassan kasar nan da suka gwada shi. Akwai dimbin zumudi kan wannan tallafi na biyan Naira dubu biyar. Idan kasa tana da mutum fiye da miliyan 100 da suke rayuwa cikin kuncin talauci, wajibi ne ka fara wani abu na shirin kawo dauki mai dimbin yawa. Naira dubu biyar kudi ne mai gwabi ga mutane da dama. Sharadi na farko muna son karfafa gwiwar mutane su tabbatar cewa sun sa yara a makaranta sun samu ilimi, a karfafa musu gwiwa su ba ’ya’ya mata ilimi. Manufa a karfafa wa jama’a su samu dogaro da kansu ta hanyar fara samun abin yi. Kuma ina ba ku tabbaci nan da ’yan makonni masu zuwa za a fito da dabarun tafiyar da shirin.
Aminiya: Game da kwato dukiyar sata daga tsofaffin jami’an gwamnati, ba mu sani ba ko Minista yana sane da adadin kudin da aka kwato zuwa yanzu?
Lai Mohammed: Kun san akwai kudin da aka kwato, amma Shugaban kasa ya ce zai zamo an gaggawa idan aka bayyana adadinsu don kada a yi kafar ungulu ga kokarin kwato kudin da ake yi. Kuma in kun lura za ku ga saboda gaskiyar wannan gwamnati da yin komai a bayyane da rikon amanar shugabanninta, kasashe da dama da a baya suke gum da bakunansu, yanzu suna fitowa fili suna tallafa mana. Wasu kudin da ake zargin na almundahana ne kasashen sun rike su saboda suna da yakinin cewa ko an dawo da kudin za a sake almubazzarantar da su ne, amma yanzu da suka ga gwamnatin da take yi da gaske kuma mai gaskiya sun fara kiranmu mu zo mu karbi kudin, hakan na gudana a hankali, amma ba na jin ya dace a bayyana nawa aka kwato a yanzu.=
Aminiya: Sunan Najer ya ya baci a kasashen waje, wane yunkuri kuke yi wajen kyautata sunanta a kasashen duniya?
Lai Mohammed: Masu iya magana suna cewa idan ka iya talla, sai ka sayar da kaya da yawa. A bangaren shugabanci a ’yan watannin baya ana kyamarmu. Ba wata kasar da take son a jinginata da mu. Amma bayan zuwan Shugaba Muhammadu Buhari, al’amarin ya fara canjawa, matakan da yake dauka martabarmu ta fara daukaka fiye da biliyoyin Naira da aka kashe da sunan sake fasalin Najeriya (a gwamnatin baya). Yau muna alfaharin kasacewa ’yan Najeriya, ana girmama mu fiye da yadda ake yi a da. Shugaban kasarmu mutum ne mai kazar-kazar mai kwazo don canja fasalin Najeriya. Kun san kafin a zabi mutum ya zama Minista a Najeriya sai ya kashe Naira miliyan 100 kafin a tantance shi a Majalisar Dokoki ta kasa, amma yanzu ina tabbatar maka babu Ministan da zai ce ya kashe ko sisin kwabo don a tabbatar da shi a matsayin Minista. Babu Ministan da zai zo ya ce, sai na mayar da Naira miliyan darina da na kashe kafin a amince da ni, sannan in fara aiki. Wannan babban ci gaba ne, amma wasu ’yan Najeriya ba su ganin haka. Sannan lokacin da aka tunkari Shugaban kasa kan ya sa hannu a kan wata takarda don sayen sababbin motoci na Naira miliyan 400, sai ya ki yarda. Ya ce, motocin da na gada daga magabacina sun ishe ni in yi aiki da su. Ba ma kawai ya tserar wa Najeriya Naira miliyan 400 ba ne har ma ya nuna misali ta yadda babu Ministan da zai ce yana so a sayo masa sababbin motoci hudu ko fiye. To a hada wannan Naira miliyan 40 sau jihohi 36 ba karamin kudi za a kubutar ba. Wannan ne ya sa a yau ake girmama ’yan Najeriya, kuma duk da matsalar faduwar tattalin arzikin kasa da duniya ke fuskanta masu zuwa jari suna haba-haba don zuwa su zuba jari, suna son san cewa idan suka zuba jari a kasar nan za a yi musu adalci kuma wannan shi ne abin da ake ciki. Babban abin da muke farahri da shi yanzu muna da gwamnati muna da shugabanci muna da Shugaban da yake nuna misali nagari wanda zai kai kasar nan ga tudun mun tsira. Irin surutai da soke-soken da ake yi a baya yanzu babu su. Wannan ya sa talaka yana alfahari da gwamnatin da ake da ita, yana ganin ga ministoci masu saukin kai, yana gani ga Shugaban kasa mai saukin kai, Shugaban kasar da ba ya rayuwa ta almubazzaranci da facaka. Don haka kimar aiki da gaske da kimar sadaukar da kai da gaskiya da rikon amana sun haifar da da mai ido, wannan ne ya sa daukacin kasar nan ta sauya.
Aminiya: Akwai bayanan da ke cewa za a farfado da shirin Yaki da Rashin da’a (WAI) a ina aka tsaya kan wannan manufa?
Lai Mohammed: Idan gwamnati ta hau karagar mulki akwai bukatar ta mika kasafin kudi, komai kyan shirinka kana bukatar kudi don ka tafiyar da shi. Wannan kudi tilas ya samu amincewa majalisa sannan a sarrafa shi. A bisa fatar za a amince da wannan kasafi, Ma’aikatar Watsa Labarai ta yi nisa wajen tsara wannan shiri. Sai dai ba za mu kira shi Yaki da Rashin da’a (WAI) ba, za mu kira shi ne da “Canji Ya fara ne daga kaina.” Saboda mun san cewa abin da ke damun Najeriya a yau ba za a magance shi ba, idan sama ko tsakiya ne kawai za su canja dabi’unsu. Mun gano matsalar Najeriya ta yi muni ta yadda muke ganin canjin da muke nema ba zai samu ba, idan muka ci gaba da kallon al’amura ko gudanar da su ta hanyar da muke gudanar da su a yanzu. Misali dukkanmu mun bayar da gudunmawa ta wannan hanya ko waccan wajen samun kanmu a halin da muke ciki a yau. Tun daga kan Minista zuwa mai facin taya zuwa mai sayar da magani zuwa bakanike. Don haka kamfe din da muke gudanarwa misali a fara da Shugaban kasa shi kansa, zai ce ne: “Sunana Muhammadu Buhari. Ni ne Shugaban Tarayyar Najeriya. Ba na bukatar na goro daga masu yin kwangila. Canji ya fara daga kaina!” Sai a je ga mutumin da yake sayar da magani ya ce: “Ni mai sayar da magani ne. Ba zan sayar da jabun magani ba. Canji ya fara daga kaina!” Haka bakanike ya ce “Ba zan sayi jabun kayan gyara ba. Canji ya fara daga kaina!” Wajen gudanar da wannan kamfe zai kasance na dukkan kafofin watsa labarai ne, zai shafi kowa. Dukkanmu masu laifi ne ta wannan hanya ko waccan, misali ko direbanka idan ka ba shi kudi ya sayo maka man fetur raba kudin zai yi ya sayo na rabi. Muna sa ran fara wannan kamfe a farkon watannin uku na bana ko watanni uku na biyu.
Aminiya: Dangane da batun wadanda yaki ya tarwatsa daga gidajensu, gwamnati na duba yiwuwar mayar da su garuruwansu; wasu kuma na ganin babu cikakken tsaron da zai bayar da damar yin hakan. Ko ina aka tsaya?
Lai Mohammed: A’a. Na ziyarci yankin Arewa maso gabas na ga dimbin barnar da aka yi na asarar dukiyoyi da rayuka, wanda kuma ya danganta ne daga gari zuwa gari. Alal misali Bama, babu wanda zai yi tunanin sake tsugunnar da al’umma a Bama yanzu, har zuwa nan da wasu watanni, musamman idan an yi la’akari da irin mummunar barnar da aka yi a garin Bama. Idan kuwa ka tafi Konduga a yau, za ka ga ana aikin gyaran garin da gine-gine, ana kuma kokarin sake tsugunnar da mutanen garin da suka yi kaura; kuma garin zai samu cikakkiyar kariya idan mutane suka dawo suka zauna a cikinsa. Sai dai gwamnati ba za ta dawo da kowa garinsa ba, har sai ta gamsu da cewa an samu cikakken tsaro da sauran kayan more jin dadin rayuwa. Saboda haka dole ne mu yaba wa gwamnatin tarayya da ta Jihar Barno, saboda irin jajircewar su wajen sake gina garuruwan da aka barnata dukiya da rusa gidaje, don sake dawo da wadanda aka tarwatsa garuruwansu. Mafi yawan kason kasafin kudin Jihar Barno na wannan shekarar zai tafi ne a bagire uku, wato sake ginawa da gyarawa da tsugunnar da al’umma a garuruwansu. A wasu wuraren za a samu sauki mayar da al’ummar fiye da wasu garuruwan in an yi la’akarin da dimbin barnar da aka yi.
Lallai ya kamata mu fahimci cewa, batun wadanda yaki ya tarwatsa su al’amarin ya wuce misali, don haka sai mu karfafa gwiwar irin wadannan mutane su koma gidajensu a garuruwansu na haihuwa. Wasu ya zamar musu dole su fice daga gidajensu, saboda ba su da kariyar tsaro. Jami’an tsaron da suka hada da ’yan sanda da jami’an farin kaya da kwastam suna aikin hadin gwiwa da sojoji da kuma kungiyoyin agaji da na jinkai irin su Red Cross. Ta haka ne za mu yanke matsaya game cancantar komawar wadannan bayin Allah gidajensu.
Aminiya: Dangane da al’amarin da ya shafi cin hanci da rashawa, ma’aikata na taka muhimmiyar rawa a ayyukan gwamnati, ko gwamnati ta shirya musu albashi da zai dauki nauyin bukatunsu, ta yadda son zuciya ba zai rinjaye su ba?
Lai Mohammed: A halin yanzu ba ni da hurumin yin bayani game da ko za a kara albashi ko akasin haka. Sai dai abin da zan iya cewa, shi ne, idan har muka samu nasarar yaki da cin hanci da rashawa, to kowa zai samu isassun kudin gudanar da bukatun rayuwa gwargwadon hali. Ina mai ba ku tabbacin cewa, idan har aka samu nasarar dakile hanyoyin satar dukiyar al’umma, to ko ana sayar da gangar man fetir dala 10 ko biyar za a samu tafiyar da wannan kasa cikin nagarta. Shin ba abin mamaki ba ne a ce mutum 55 ne kawai suka sace makudan kudin kasar nan? Shin wace irin musifa ake jin cewa, mutum 500 irin wadannan za su iya haifar wa kasar nan?
Irie-iren wadannan mutane tuni aka gurfanar da su a kotuna daban-daban. Idan muka samu hanyoyin ababen hawa masu nisan kilomita 600 a Najeriya, wannan na nuni da cewa, kilomita 100 a kowane yanki shida da ke kasar nan. Idan muka samar da babban asibitin kwararru na zamani a kowace jiha, an bude babin sabuwar rayuwa mai inganci. Gaskiyar lamari, ita ce, idan har ba mu dage wajen kwato dukiya da yaki da cin hanci da rashawa ba, zai yi wuya ko da kasafin kudin shekarar 2016 a iya aiwatar da shi. Kuma abin da muka gano shi ne, wadannan kafofi sata da ake amfani da su, su ke kwashe dukiyar kasar nan da aka tara. Shin haka kawai kasafin kudi ke ta karuwa a kowace shekara, kuma duk da haka talauci na dada karuwa? Ko mene ne dalili? Ba wani abu ya haifar da haka ba, illa cin hanci da rashawa?
A shekarar 1999 daukacin kasafin kudin Najeriya Naira biliyan tara da miliyan 700 ne kawai, sai ga shi a shekarar 2016 kasafin ya zama tiriliyan shida. Shin ko talauci ya ragu? To haka yake hauhawa gwargwadon karin da aka yi. Shi ya sa bai kamata a sassauta wajen yaki da cin hanci da rashawa ba. Sai mun yake shi, tamkar yadda muka yaki Boko haram ko fafutikar kawar da cutar Ebola.