Yadda za a ci moriyar noman albasa
Kashi 85 cikin 100 na albasa ana samunsa ne a lokacin sanyi.
Albasa tana daya daga cikin kayan lambu da ake amfani da su a duniya, saboda muhimmin dandanonta a girki.
Saboda samar da ita da kuma ajiyarta bayan cire ta, yana da muhimmanci manoma su yi hankali da zabin iri da za su shuka.
- An sace amarya awanni kafin bikinta a Filato
- Bello Turji ya sako mutum 52 da ya yi garkuwa da su a Zamfara
Kashi 85 cikin 100 na albasa ana samunsa ne a lokacin sanyi, saboda yanayin da take bukata.
Tabbas, manomanta dole ne su gano kwayoyin halitta da kayan lambu ke so tare da shirya wajen ajiya da za ta dauki lokaci mai tsawo bayan cire ta.
Ana noman albasa a kan kunyayyaki masu tazarar mita 1 tare da tazarar tushe a kan a tsakanin shuka da shuka.
Ana dasa irin albasar ne ta hanyar dasa ta kai-tsaye a kan kunya, bayan nome ciyawa da yin ban ruwa don fitar da irin.
Ya kamata a kula da wajen da ake rainon irin albasar na tsawon kwana 40 kafin dasa ta a gona.
Bayan sharar gonar da za a yi dashen albasar, za a iya shirya ta a cikin buhuna da tukwanen shuka fure, kuma ya kamata kasar shukar ta zama yashi-yashi domin amfanin gona ya dogara da tushensu don habaka ganye da kuma gina su.
Albasa ta fi son tsaka-tsakin ingantacciyar kasa da ba tabo ba kuma ba yashi ba.
Tana son kasar da take tare da taki mai gishirigishiri, kuma a gyara gonar da za a dasa albasar don samun kyakkyawan sakamako.
Dasa albasa ya fi dacewa da maraice bayan ban-ruwa a gonar da aka shirya ko matsakaicin wurin da za a yi shukar.
Ana dasawar a tazarar tsawon santi-mita 5 domin albasa matsakaiciya, babba kuma ta kai tazarar santi-mita 7.5.
Saboda bambancin albasa da sauran amfanin gona koyaushe ta fi son kasa mai yashi-yashi ko mai laushi, tun kafin a fara shirin nomanta.
Yana da muhimmanci a rika nome ciyawa akalla kowane mako biyu; kuma a yi mata ban-ruwa sau biyu a mako, musamman a lokacin sanyi.
A yi feshin maganin cypermathrine sau daya a kowane mako lokacin da ganyen ke bushewa, ko kuma a madadin hakan ana iya amfani da maganin mancozeb tare da copper odide sau daya kowane mako.
Ana iya sanya takin zamani samfurin NPK 20:10:10 mako biyu bayan dasawa don shukar farko. Ana iya sanyawa a karo na biyu. A karshe, a sanya takin zamani samfurin calcium nitrate.
Albasa tana girma a tsakanin kwana 85 zuwa 100 bayan dasawa, ko kuma bayan ganyen ya zama launin ruwan kasa, ya fara bushewa yana faduwa.