Yadda za a farfado da ilimi a Sakkwato – Aminu Bala Sakkwato
Alhaji Aminu Bala Sakkwato tsohon sojan sama ne da ya kai mukamin Sikwadiran Lida kafin ya yi ritaya, fitaccen dan siyasa a Jihar Sakkwato kuma jigo a Jam’iyyar APC a jihar, ya taba shugabanta kwamitin tsabtace birnin Sakkwato inda suka samu nasarar kawar da shara daga birnin a zantawarsa da Aminiya ya bayyana yadda aka […]
Alhaji Aminu Bala Sakkwato tsohon sojan sama ne da ya kai mukamin Sikwadiran Lida kafin ya yi ritaya, fitaccen dan siyasa a Jihar Sakkwato kuma jigo a Jam’iyyar APC a jihar, ya taba shugabanta kwamitin tsabtace birnin Sakkwato inda suka samu nasarar kawar da shara daga birnin a zantawarsa da Aminiya ya bayyana yadda aka yi suka samu waccan nasara kuma ya tabo wasu al’amura da suka shafi jihar da tarayya:
Aminiya: A matsayinka na tsohon shugaban Kwamitin Tsabtace Birnin Sakkwato da Kewaye yaya kake kallon tsarin tsabtace birnin a yanzu?
Aminu Bala: Kwamitin da na shugabanta na tsabtace birni da kewaye a kawata shi da cire haramtattun abubuwa kan hanya, ka sani ni dan siyasa ne saboda kishin jihata da ganin yadda garin ya zama a hargitse ya sanya na karbi aikin da zuciya daya na gaya wa mambobin kwamitin cewa za mu yi aiki ba tare da nuna bambancin siyasa ko kusanci ba don ciyar da jihar gaba a bangaren tsabta don haka duk wanda ya saba dokar tsara birni, hukuma za ta yi aikinta a kansa. Da farko na samu matsala da jama’a daga baya suka fahimci aikinmu musamman na gefen hanya inda muka fito da sharar titunan Sakkwato da kasa ke kokarin mamayewa. Da kudina na yi wannan aikin a titin Abdullahi Fodiyo daga baya ne Gwamna a lokacin ya kira ni ya yaba min har ya biya ni kudin da na kashe a aljihunsa sai aka fadada shirin sharar zuwa saura tituna 12 muka dauki ma’aikatan wucin-gadi da muke biya Naiar dubu 15 a wata da
yawansu ya kai 350. Mun saya musu kayan aiki isassu sukan fito tun da safe kafin mutane su fara fita duk wanda ya zo zai ga hanyoyinmu fes. Har a gari suna maganar ba masu aiki sai kwamitinmu musamman gaba da bayan tashar mota ta jiha da muka gyara tsaf aka rika ajiye motoci, wanda kafin haka kashi ake yi a wuraren, ta gefen ma’aikata kuwa duk wanda ba ya son aiki sallamarsa muke yi. Sarki goma zamani goma da gwamnatin Aminu Waziri ta zo ma’aikata na bin bashin albashi na wata biyu, mu ’yan kwamiti muna bin wata hudu mun gaya musu amma ba mu bar aiki ba saboda kishin jiha kai-tsaye suka soke kwamitinmu. Ana ganin za a sanya wasu ko ba mu ba don ci gaba da aikin, amma shiru ake ji sai can aka
ce an kafa kwamiti a karkashin Babban Sakataren Ma’aikatar Muhali, tun lokacin da aka kafa shi an kashe sama da Naira miliyan 300 amma ba wani alfanu. Gaskiya yanzu ko an ba ni wannan aikin ba zan yi ba sai dai in ba da shawara ga gwamnati ta mayar da aikin ga ’yan kasuwa ko ta sake kafa =kwamiti irin namu in har ana son kawar da shara a birnin Sakkwato.
Aminiya: Tattalin arziki kasa na cikin matsala kuma ga shi Sarkin Kano ya ba da shawara kan a kaya darajar Naira amma Shugaban kasa bai aminta ba, yaya ka ga lamarin?
Aminu Bala: Sarkin Kano masanin tattalin arzikin ne da ya shugabanci babban bankin kasa, ban san dalilin da ya sa a lokacin da yake saman kujera bai zo da wannan shawarar ba, fito da wannan zance gaya wa jama’a ne wani abu daban. kasashen da suka kayar da darajar kudinsu suna da kayan da suke kerawa su fitar waje amma mu komai ba ma yi, kamfanoninmu a mace suke, ya kamata a bai wa Buhari lokaci. Ko da ya zo Dala ta kai Naira 200, sabanin hawansa na farko da Dala ke kasa da Naira.
Aminiya: Kai tsohon soja ne yaya kake kallon yaki da Boko Haram da sojoji ke yi da kuma yakar rashawa da gwamnati ke yi?
Aminu Bala: To harkar yakar Boko Haram an samu nasara, ban zaci akwai wata karamar hukuma na hannunsu ba, a yanzu an karya lagonsu domin da motoci suke kai hari suka koma da babur suka sake komawa da dawaki da kekuna yanzu a kasa suke kai hari can da nan, sun koma inda ’yan gudun hijira suke ko kasuwa. Hakan ke kara nuna sun yi rauni duk da suna fitowa da dabaru daban-daban, sojoji da gwamnati duk sun yi kokari a wannan yaki. Tafiye-tafiyen Shugaban kasa sun samar da alfanu abin da ya rage mu hada kai mu yi hakuri. Ba a kawar da masu tada kayar bai lokaci daya, dubi Somaliya da sauransu. Yaki da cin hanci abu ne mai kyau, ko PDP kake yi in ka dubi yadda gwamnatin baya ta so cin bashin Dala biliyan daya ashe tana da sama da biyu da ta wawure sai yanzu asiri ke tonuwa. Ya dace a yi wa dokar kasa gyaran fuska duk wanda aka kama da cin kudin kasa a harbe shi.
Aminiya: Shugaban kasa Buhari ya ce ya fi son ya yi aiki da ma’aikatan gwamnati fiye da ’yan siyasa ga shi kuma ana rikita-rikita kan kasafin kudi yaya kake son ya dauki ma’aikata a yanzu?
Aminu Bala: Su ma’aikatan gwamnati a jaye suke duk in da aka yi da su can suka yi, daga shugaba in na kwarai ne haka za su zama. Akasin haka matsalar da aka samu ta kasafin kudi sun zaci wannan gwamnatin irin wadda ta gabata ne a zabga kudi son rai a zo kowa ya dauki kasonsa, Buhari ba zai kyale su ba. Kuma ina kira a dawo da wannan kasafi da aka yi tabargaza a cikinsa kada a bar shi a majalisa a zo a gyara shi sannan a binciko wadanda suka yi wannan don hukunta su. Dubi yadda shirmen yake a ce Ma’aikatar Ilimi za ta gina gada kuma Ma’aikatar Cikin Gida za ta yi bincike a fannin ilimi da sauransu haka suka yi shirme cikinsa. Mutane su yi hakuri a dawo da shi a gyara ina goyon bayan Buhari duniya na tare da shi.
Aminiya: Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kaddamar dokar ta-baci kan harkar ilimi ka gamsu da shirin?
Aminu Bala: Hakikanin gaskiya ban san abin da suke nufi da dokar ta-baci ba, na farko dukkanmu mun san yadda harkar ilimi take a lokacinmu da yanzu ba wani abu sai abin bakin ciki a jihar nan, akwai inda har yanzu ba su da makarantar firamare kuma na san garuruwan da kwaryar birnin ba za ta wuce kilomita goma sha ba irin su Dogon Marke da Kardaye da Tindi da sauransu. Ni kaina na taba rubuta takarda kan wannan matsalar amma ba abin da aka yi ana bayar da muhimmanci ga abin da bai kamata ba. Tun farko ya kamata a yi wa hukumar ba da ilimin firamare garambawul kafin a magance kowace matsalar da ta addabi ilimin, akwai abin ban haushi a ce a Sakkwato akwai inda babu makaranta kuma da jama’a a wurin. Na biyu dole a dawo da makarantar horar da malamai da aka kashe tana da rawar da za ta taka wajen samar wa malamai dabarun koyarwa ba wai da ka kammala karatu ba ka shiga aji ba sanin ilimi koyarwa. Kuma a fito da kwamitin da zai kula da ilimi in har dai dokar ta-baci aka sanya ba surutu ba.