Yadda za a fitar da ‘yan takara a Jam’iyyar APC

Babban Sakataren Shirye-Shirye na Jam’iyyar APC, Mista Emma Ibediro ya bayyana yadda APC za ta gudanar da zaben fid da ’yan takara da kuma kudaden sayen fom na duk kujeru. Sabon tsarin da ya fito mai neman tsayawa kujerar Shugaban kasa zai biya Naira miliyan 45 domin sayen fom din takara, wato Naira miliyan 5 […]

Yadda za a fitar da ‘yan takara a Jam’iyyar APC
Yadda za a fitar da ‘yan takara a Jam’iyyar APC

Babban Sakataren Shirye-Shirye na Jam’iyyar APC, Mista Emma Ibediro ya bayyana yadda APC za ta gudanar da zaben fid da ’yan takara da kuma kudaden sayen fom na duk kujeru.

Sabon tsarin da ya fito mai neman tsayawa kujerar Shugaban kasa zai biya Naira miliyan 45 domin sayen fom din takara, wato Naira miliyan 5 na sha’awar tsayawa sai kuma Naira miliyan 40 na fom. 

Mista Ibediro ya ce za a yi rangwame ga mata da kuma nakasassu da suke da sha’awar tsayawa takara a APC, inda za a rage musu kashi 50 na kudin.

Masu neman tsayawa takarar Gwamna kuma za su biya Naira miliyan 22 da rabi, sai kujerar Majalisar Wakilai za a biya Naira miliyan 3 da dubu 800, ta Sanata Naira miliyan 7, sai kuma ta Majalisar Jiha, Naira dubu 850.

Ya ce an fara sayar da fom din daga shekaranjiya Laraba 5 ga  Satumba, kuma za a rufe sayarwa a ranar 10 ga Satumba,  kuma daga ranar 12 ga Satumba za a daina karbar fom din.

Haka kuma za a yi taron fid da wakilan jam’iyyar wadanda za su yi zaben fid da dan takara a duk fadin kasar nan a ranar 12 ga Satumba. Sai kuma ranakun 13 da 14 da aka ware domin sauraron kararraki a kan zaben fid da wakilan. Sai kuma a zauna domin sauraron kararrakin a ranakun 19 zuwa 20 ga watan.

Za a gudanar da zaben fid da dan takarar Shugaban kasa ne a ranar 20 ga Satumba, kuma za a saurari kararraki a kan zaben ranar 22 ga watan.

Sai kuma ranar 25 a gudanar da zaben fid da ’yan takarar gwamnoni, sannan ranakun 26 da 27 za a saurari kararraki a kan zaben fid da ’yan takarar Gwamna.

A ranar 6 ga Oktoba ne jam’iyyar za ta yi babban taron tabbatar da dan takarar Shugaban kasa a zaben 2019.

Sakataren Shirye-Shiryen ya kara da cewa duk masu sha’awar tsayawa takarar Shugaban kasa da Gwamna da Sanata da dan Majalisar Wakilai za su sayi fom dinsu ne a Sakatariyar Jam’iyyar ta kasa a Abuja.

Sai masu sha’awar tsayawa takarar Majalisar Jiha su sayi fom din a ofisohin jam’iyyar a jihohinsu.

 

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa