Yadda za a girka ‘Kamoniya’
Barkan mu da sake haɗuwa a zauren girke-girke na watan Ramadana.

Barkan mu da sake haɗuwa a zauren girke-girke na watan Ramadana. Tare da fatan ana cikin koshin lafiya.
A yau na kawo wa uwargida wani girkin shuwa daga Jihar Borno, wato ‘Kamoniya’ domin yin buda baki. A sha ruwa lafiya.
Abubuwan da za ki bukata:
· Hanta · Tumbi · Huhu · Albasa 3 · Lemun tsami · Attaruhu · Man gyada · Curry da thyme · Maggi da gishiri
Yadda ake hadin:
A wanke kayan ciki (banda hanji), sai a yanka su kanana. A zuba man gyada a cikin tukunya, sai a dora a kan wuta.
Sannan sai a yanka albasa a zuba man gyadan kadan a cikin tukunyar.
Bayan haka, sai a zuba curry da thyme da gishiri kadan a wankakken kayan cikin. Sai a gauraya su kafin a zuba a tukunya.
Idan an gama gaurayawa, sai a zuba su a tukunya ana juya su har sai ruwan da man sun shiga cikin kayan cikin.
Za a ga kayan cikin sun koma ruwan kasa. Sai a juye a kula a rufe. Hakan za a rika yi kadan-kadan har sai kayan cikin sun kare.
A wanke attaruhu da lemon tsami. A kirba attarugu ya kirbu sosai, sannan sai a zuba maggi wanda zai kashe zafin attaruhun.
Sai a matsa lemon tsami a kan attaruhun.
Ana cin kamoniya ne da wannan hadin attarugun. Ana dangwalawa a attaruhu don samin dandano mai gamsarwa.