Yadda za a gyara matsalolin fina-finan Hausa

Ta yaya za a gyara matsalolin da suka yi katutu a masana’antar fina-finan Hausa? Kafin bullowar fina-finan Hausa, Hausawa sun dogara ne kaco kan ga kallon fina-finan kasashen waje, kamar na Amurka da Chaina da Indiya da Japan da sauransu”.bullowar fina-finnan Hausa ya saka da yawa daga cikin Hausawa cikin farin Ciki domin a ganinsu  […]

Yadda za a gyara matsalolin fina-finan Hausa
Yadda za a gyara matsalolin fina-finan Hausa

Ta yaya za a gyara matsalolin da suka yi katutu a masana’antar fina-finan Hausa? Kafin bullowar fina-finan Hausa, Hausawa sun dogara ne kaco kan ga kallon fina-finan kasashen waje, kamar na Amurka da Chaina da Indiya da Japan da sauransu”.
bullowar fina-finnan Hausa ya saka da yawa daga cikin Hausawa cikin farin Ciki domin a ganinsu  yadda suke kallon al’adun wasu to kuwa suma yanzu za’a fara kallon al’adunsu ana karuwa da su, haka zalika a kuma sansu a sassa daban-daban na Duniya (kamar yadda suma suka san al’adun wasu).
Amma Kash! tuni wannan murna ta koma ciki kasancewar mafi yawan finafinan da ake a yanzu idan ka kallesu zaka tarar ba al’adar Bahaushe ake nunawa ba (za ka tarar al’adar Bahaushe ta yi gabar su kuma wakannan kasusuwa sun yi yamma).
Tun daga tufafin da ake sakawa a wasu finafinnai zaka san cewa ba al’adar ba haushe ake nunawa ba, haka za lika ba bahaushe ake fadakarsuwa ba.
Idan ka kalli fina finnan turawa, China ko Indiya zaka taras sukan yi amfani da tufafinsu da sauran kayansu na al’adu, amma idan ka zo ka kalli fim din Hausa za ka tarar a gunsu ba haka ba ne. Su basa amfani da kayansu sukan kwaikwayi Irin kayan da Turawa ke sakawa tare da yadda turawa ke rayuwarsu.
Bayan kuma Allah Ya Albarkaci al’ummar Hausawa da Al’adu kammalallu, wanda a tunanina Bama Bukatar aron Wasu al’adu Daga Kasashen turawa ko indiyawa ko ma wasu cen daban.
Bayan aro wasu al’adu kuma sai ka taras daga cikin wayannan finafinai da Hausawa keyi sukan kushe Al’adarsu da kansu da sunan barkwanci. Misali, akwai wani fim mai suna ‘DAN GASKE inda a fim din suka nuna, Basakwkwace, a fim din sun nuna wannan Basakwkwacen sam baida ilmin addini da ilmin zamani kuma baida wayo haka zalika bai san kansa ba.
Hakika duk mai hankalin da ya kalli wannan fim din ya san sam ba’a yiwa Hausawa ko kuma sakwkwatawa  Adalci ba, domin In dai ilmi ake nema a nijeriyar nan idan aka zo kan Sakkwatawa sai dai a shafe fatiha a tashi.
Domin kuwa tun kamin zuwan Turawa a najeriya Sokoto Suke da Manyan mashahuran Malamai Wakanda Za’a kirasu Original farfesas.
Shehu Usman wanda ya rayu a karni na 19 (19 centuary), ba a Najeriya ba duk duniya ya wuce a kalle shi a ce masa jahili ko a soke shi, bayan Shehu kan Fodiyo akwai almajiransa da ‘ya’yansa, kamar su Malam
Abdullahi da Muhammadu Bello da Buhari da Nana Asma’u.
Wakannan mutane dukkansu Manyan Malamai ne kuma Ma rubuta littafai kuma masana a harkokin siyasa da tattalin arziki kuma duk sun rayu ne a jahar ta sokoto. Haka zalika har yanzu sakkwatawa basu zauna ba game da neman ilmi don haka nuna Basakkwace a jahili yana nufin suka ga wakannan bayin Allah, da yi musu ungulu da kan zabo.
A binda masu shirya wannan finafinnai basu sani ba (ko sun sani suka take sanin) shine, Wani fa daga ya kalli kaset din fim duk abin da ya gani zai dauka haka ne.
A takaice dai Duk wanda ke biye da shirye-shiryen fina-finan Hausa, ba zai yiwu ya rasa ganin wani abu na ki ba a cikin finafanan na Hausa, wanda wakannan fina-finan suna haifarda matsaloli masu tarin yawa a cikin al’umma.
Daga cikin Matsalolin akwai Lalata tarbiyyar yara da samari ta hanyar koyon sata, ko fashi da makami, da kuma shan miyagun kwayoyi.
Haka kuma akwai batanci ga addini, da siffanta malaman addini da mummunar siffa, tare da koya wa matasa dabarun yaudarar ‘yan mata. Da koya wa samari hanyar yadda za su raba wani saurayi da budurwarsa. Su ma ‘yan matan haka, sukan koyi makirci da hanyoyin kwace wa ‘yan uwansu mata samari.
Babu shakka Fim wata kafa ce daga cikin kafafen yaka labarai, sannan kuma hanya ce ta fakakarwa, Nishakantarwa da Ilmantarwa. Haka kuma hanya ce ta kasuwanci. Domin kuwa akwai matasa da wakanda suka manyanta da yawa, wakanda ta nan ne suke samun abin da suke biyan bukatunsu na yau da kullum.
Wanann na nufin ke nan idan har harkar fim ta gurbace gaba kaya to kuwa, an samu ‘Ammatil Balwa’ (Ma’ana wani abu da ya game al’umma ya zama musifa da  ke da wuya a samu wani wanda zai kubuta daga bala’inta). Babu shakka idan har fina-finnan Hausa suka ci gaba da tafiya a ma’aunin da suke a yanzu to kuwa za a yi ta samun baraka a kowane bangare da muke a yanzu.
Idan har gyara ake so, dole ne hukumar tace fina-finai ta fito da dokokin yin fim a kan dacewarsa da addininmu da kuma al’adunmu. Idan kuwa ita wannan hukuma ba za ta iya ba, to gwamnati ta kafa wakannan dokokin da kanta ga wakannan fina-finnai.
Gyara ba zai yiwu ga hukuma ko gwamnati kakai ba, dole ne marubuta fina-finai su san cewa, mutuncin kowace al’umma ya dogara ne ga yadda ta mutunta komai na ta daidai da addininta da kuma al’adu. A ganina ya kamata marubutan fina-finan Hausa su farka su rika rubutu mai ma’ana tare da mutunta al’adar Bahaushe.
‘Yan kallo na da wata rawa da za  su taka domin yin wannan gyara ta hanyar yin ca! ga duk wani fim marar kyau, tare da kaurace wa duk wani fim marasa ma’ana haki da kaurace wa sayen fim kin kamfanin da ya shirya shi.
Ina ganin idan aka bi wakannan hanyoyin za a iya cimma nasara, tare kuma da bunkasa al’adar Hausa.
Hakika  zuba wa wannan sana’a ta fim ido ba tare da tsawatar musu (akan wasu daga cikin kura-kurran da suke yi) ba, to kuwa ana nufin babu wata matsala don al’adar Malam Bahaushe ta ruguje kasa warwas.
Al’ada ita ce hanyoyin rayuwar mutane, ta kunshi harsunansu da addininsu da abincinsu da sana’o’insu.
A ganina, abu ne mai wuya a raba rayuwar Hausawa da addinin Musulunci;  shi ke nan lalacewar al’adun Malam Bahaushe kamar lalacewar addinisa ne.
Daga, Jamilu Sani Rarah, Sokoto. 07031960698. Gmail, [email protected]. Manazarta Zauren
[email protected]

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya