Yadda za a hana kurajen fuska fitowa
Matasa musamman ‘yan mata na sha’awar su rika kwalliya domin su kara kyawu da daukar hankali. Za su so su fara kare kansu daga kurajen fuska kafin su fito. Idan har kurajen fuska suka fito kafin a magance su sai an sha wahala. Idan za a lura za a ga ‘yan mata na gasar kyau. […]
Matasa musamman ‘yan mata na sha’awar su rika kwalliya domin su kara kyawu da daukar hankali. Za su so su fara kare kansu daga kurajen fuska kafin su fito. Idan har kurajen fuska suka fito kafin a magance su sai an sha wahala. Idan za a lura za a ga ‘yan mata na gasar kyau. Kowace na kokarin ta ga ta fi kawarta kyau; walau a kwalliya ko a ado. Don haka ne muka kawo muku hanyar mafi sauki da za a bi don hana wadannan kurajen fitowa.
· Idan ana son a samu fuska mai santsi kuma marar kuraje, sai a rika wanke fuska kullum da daddare kafin a kwanta barci.
· Idan kurji ya fito a fuska, kada a yi saurin tabawa ko fasawa, domin yin hakan na haifar da wasu kurajen da kuma tabo a fuska.
· Ana amfani da man ‘sun screen milk’. Bayan an shafa sai a jira bayan mintuna 15 kafin a shiga rana. wannan man na dauke da sinadarin da ke kare fuska daga zafin rana, zai kuma hana kuraje fitowa.
· A tabbata ana wanke fuska da sabulu (na jarirai) kafin a kwanta barci. Yin hakan na sanya fata ta yi kyawu da sheki.
· Ana amfani da hodar ‘concealer’ domin dada wa fatar fuska haske. Idan akwai kuraje a fuska kada a rika yawaita shafa hodar fandeshi domin yin hakan na sanya kurajen sake fitowa sosai.
· Bayan haka,kada a manta a rika fesa turare a kodayaushe.