Yadda za a iya magance fata mai gautsi
Tana mayar da fata mai gautsi ta yi santsi.
Idan kina da fata mai gautsi, ko kuma fatar ta koma mai gautsi saboda sanyi ko hunturun da ya shiga gari, ga abubuwan da ya kamata ki yi.
Zuma tana da matukar inganci musamman wajen gyara fatar jiki domin tana sa fatar ta zama mai dan maiko.
Zuma tana rike mai a fata tsawon lokaci mai yawa. Kuma zuma tana kare fata daga kyankyanin abubuwa da yawa.
Kwallon inabi yana da inganci sosai musamman wajen gyaran fata, kuma magani ne ga cuttuttukan fata kamar su kyanda da sauransu.
Tana sa fata santsi kuma tana da sinadarin vitamin E wajen gyaran jiki, gyaran kurarrajin fuska (stubborn acne).
Tana mayar da fata mai gautsi ta yi santsi, bayan kin gwada wannan lakanin kwalliyar, za ki ga fatarki ta zama mai taushi da sulbi da kuma kyau.
Abubuwan da za a bukata wajen hadin:
• Cokali biyu na zuma
• Cokali biyu na cocobutter
• Cokali biyu na man zaitun
• Digo daya na man ganyen sha’i Tee tree oil (za ki iya samun wannanman a manyan shaguna ko kasuwa).
Hadi:
Ki hada zumar da narkakken man Cocobutter da man zaitun da man ganyen sha’i a karamar robar man da ba rika amfani da ita ba.
Sai ki kwaba su, sannan ki shafa a fuskarki da dukkan gabban jikinki.
Za ki iya mayar da wannan mai, manki. Sai ki ajiye shi amma zai daskare in ya huce. In za ki yi amfani da shi gobe, sai ki sa ya narke a tukunya ko a rana.
Kwallon Inabi da abubuwan da za a bukata
• Kofi biyu na zuma
• Rabin kofin man Inabi
• Cokali shida na (chocolate) mara zaki ko cocoabutter
• Kofi biyu na gishirin rafi
Hadin:
Ki samu murta, sai ki hada zuma da man inabi, ki juya su a wata roba na man chocolate da gishirin rafi.
Ki juya su ko ki kada su sosai har sai hadin ya yi kauri. Ki shafa wannan hadi a jikinki, kina dirzawa kamar man dilke.
In har ya shiga jikinki, sai ki wanke shi da ruwan dumi ko ki yi wanka. Wannan hadi ana shafa shi ne kafin a yi wanka.
Hadin mai zuma da man zaitun da sauransu, shi ne za ki shafa bayan kin yi wanka.
Wannan hadi na sa fata mai gautsi ta yi sulbi da santsi da kuma taushi.
Amfani da shi na tsawon wata uku yana mayar da fata ta zama mai taushi.