Yadda za a karrama gwarazan marubuta uku na Gasar Aminiya
Za a karrama su tare da gabatar da maburuta 12 suka taka rawar gani a gasar.
Asabar 5 ga watan Yuni, 2021 ce ranar da za a bayyana gwarzon shekara na gasar rubutun kirkirarrun gajerun labarai da Aminiya-Trust da hadin gwiwar kamfanonin Gandun Kalmomi da Open Arts suka shirya.
A ranar za bayyana marubucin da ya ciri tuta a matsayin na daya a gasar, da wasu mutum biyu a matsayin na biyu da na uku.
Aminiya za ta kawo muku yadda bikin zai gudana kai-tsaye a shafinmu na intanet na aminiya.dailytrust.com da kuma ta Facebook da Instagram ta shafukanmu masu suna @aminiyatrust.
Za a karrama zakarun guda uku da kyaututtuka, tare da gabatar da wasu murubuta 12 da ke bi musu baya wurin taka rawar gani a gasar.
Taron, zai kuma kaddamar da littafi da ke dauke da labaran marubutan da suka yi zarra a gasar wadda jigonta shi ne siyasa.
“An shirya ta ce domin samar da ingantattun labarai na nishadi cikin Hausa da suke kunshe da matsalolin da suke jibge a tsarin dimokuradiyya da dambarwar siyasa a Najeriya.
“Wadannan labarai bayan kammala gasar, kuma an buga su a matsayin littafi, kuma ana sa ran su zama wata hanya ta nusar da jama’a, musamman matasa kan muhimmancin da ke tattare da inganta tsarin dimokuradiyya da tsabtace siyasar kasa baki daya,” kamar yadda Shugaban Kwamitin Shirya Gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi ya bayyana.
Zakarun gasar:
Labarai uku da suka yi zarra a gasar, wadanda daga cikinsu za a fitar da gwarzo su ne:
Tufka da Warwara:
Marubucin wannan labarin shi ne Mubarak Idris Abubakar.
Tufka da Warwara, labarin wani Gwamna ne da ya kammala wa’adin mulkinsa amma yana kyashin ya mataimakinsa ya gaji kujerar; duk kuwa da cewa mutane na son sa.
“Sai gwamnan ya yi amfani da tuggu da lissafi irin na siyasa, ya kifar da mataimakin nasa; ya dora wanda yake ganin zai ba shi damar cimma burinsa.
“Sai dai hakan ya faskara, inda labari ya sha bamban,” kamar yadda Marubucin ya bayyana a kunshiyar labarin.
Dimokuradiyyar Talaka:
Rufaida Umar Ibrahim, wadda ta rubuta labarin ta ce, “Wannan labari ne game da wani matashi mai suna Rabi’u, wanda ya tsoma kansa cikin harkar siyasa. Sai dai a karshe lamura suka juye, sabanin tunaninsa; wanda ya yi silar rusa dukkan mafarkansa.”
Ranar Kin Dilllanci:
Labarin da Ubaida Usman ta rubuta, “An gina shi ne a kan jigon jan hankalin shugabanni, su gane cewa ba kullum ake kwana a gado ba, sannan duniya ba matabbata ba ce.
“Duk mukamin mutum da karfin ikonsa, akwai ranar da zai mutu. Da zarar mutuwa ta riske shi kuwa, karfin mulkin ya kare.
“Baya ga haka, labarin ya tabo al’amarin fyade a matsayin wani babban al’amari da ke ci wa al’ummar yau tuwo a kwarya. Labarin ya nuna halin ko-in-kula da wadansu shugabanni ke yi dangane da al’amarin fyade,” inji marubuciyar.
Komai nisan dare. Na Yaseer Kallah
Hassada ga mai rabo. Na Mustapha Sufyanu Jikan Malam
Baki guba ne. Na Basira Sabo Nadabo
Tsaka mai wuya. Na Salim Yunusa
Kawalweniya. Na Mujaheed Ameen Lilo
Kazar kwanci. Na Maryam Umar Sakkwato
Ci ga rashi. Na Isma’il Gambo
Igiyar Linkaya. Na Hajara Ahmed Hussaini.