Yadda za a karrama zakarun Gasar Gajerun Labarai ta Aminiya-Trust
Za a karrama gwarazan shekara da wasu ’yan takara na gasar Aminiya-Trust ta 2020.
A ranar Asabar 5 ga Yuni, 2021 ake sa ran gudanar da bikin mika kyaututtuka ga gwarazan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Aminiya-Trust ta 2020 a birnin Kaduna.
Tuni dai alkalai suka tantance rubutu da marubuta uku da za a zabi na daya zuwa na uku daga cikinsu don lashe gasar.
- Ba labari mara ma’ana a Gasar Aminiya-Trust – Dokta Aliya
- Gasar Rubutu ta Aminiya ta bambanta da sauran —Dokta Aliya
Jagoran gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi ya fadi a wata sanarwa cewa an tsamo mutum uku a matsayin wadanda suka kasance gwarazan gasar ta 2020 don karrama su a ranar.
Kuma ya ce akwai ’yan takara 12 da su ma za a yaba wa kwazonsu a yayin taron wajen ba su kyaututtuka.
Zakarun Gasar Rubutu ta Aminiya-Trust ta 2020
Sunayen gwarazan da rubutunsu suka samu nasara da za a zabi na daya zuwa na uku sun hada da:
Dimokuradiyyar talaka, na Rufaida Umar Ibrahim.
Ranar kin dillanci, na Ubaida Usman
Tufka da warwara, na Mubarak Idris Abubakar
’Yan takara 12 da za a yaba wa kwazonsu a yayin taron su ne:
- Komai nisan dare. Na Yaseer Kallah
- Hassada ga mai rabo. Na Mustapha Sufyanu Jikan Malam
- Baki guba ne. Na Basira Sabo Nadabo
- Tsaka mai wuya. Na Salim Yunusa
- Kawalweniya. Na Mujaheed Ameen Lilo
- Kazar kwanci. Na Maryam Umar Sakkwato
- Ci ga rashi. Na Isma’il Gambo
- Igiyar Linkaya. Na Hajara Ahmed Hussaini.
Yadda bikin zai gudana
Za a gudanar da bikin ne a Hotel 17 da ke garin Kaduna da misalin karfe 7:00 na dare insha Allah.
Sai dai kuma wadanda aka gayyata ne kawai za a bari su shiga harabar bikin, wadanda su ma dole ne su zo da takunkumi tare da kiyaye ka’idojin yaki da cutar COVID-19.