Yadda za a kula da farce
Farce na daya daga cikin ababuwan da ke kara wa mata kyawu, don haka, ya kamata mata su kula da farcensu na hannu da kuma na kafa. Yadda ake lura da farce zai sa a fahimci mace mai tsafta ce ko kuma kazama, saboda haka, bai kamata a yi tuya a manta da albasa ba, […]
Farce na daya daga cikin ababuwan da ke kara wa mata kyawu, don haka, ya kamata mata su kula da farcensu na hannu da kuma na kafa. Yadda ake lura da farce zai sa a fahimci mace mai tsafta ce ko kuma kazama, saboda haka, bai kamata a yi tuya a manta da albasa ba, ma’ana bai kamata a rika lura da sauran sassan jiki ba tare da an hada da faratu ba.
Hanyar lura da farce
· Kada a rika amfani da rezar da kowa yake amfani da ita, domin yin hakan na janyo kamuwa da cutar mai karya garkuwar jiki. A tabbata an rika tsaftace faratu ta hanyar yanke su kowane mako.
· Domin kulawa da farcen kafa, sai a rika sanya takalmin da ya dace da kafa. Sanya takalmin da ya yi matsi na hana fitowar farce mai kyawu, sai a ga yatsu na kumbura, ko su rika ciwo.
· A rika amfani da man hannu a kodayaushe domin kulawa da farcen hannu. Idan aka dade ba a yi amfani da man hannu (hand cream) ba, za a ga farce na tsagewa.
· A tabbatar da duk wajen da za a je sai a sanya takalma, domin kulawa da farcen kafa. Sanya takalmi a kodayaushe na kare farce daga illar tuntube.
· A rika amfani da abin kankare farce (nail file) bayan an yanke farce, domin samun farce mai haske da tsafta.