Yadda za a kula da fata a lokacin sanyi

Yanzu da sanyi ya shigo, hazo da hunturu da iska da ake yi na sanya fatarmu ta lalace. Sai a ga mutum ya fara kauje da kurarraji a fata. Yana da matukar mahimmanci a kula da fata, musamman a wannan lokacin. Don haka ne a yau na kawo muku abubuwa da dama wanda za ku […]

Yadda za a kula da fata a lokacin sanyi

Yanzu da sanyi ya shigo, hazo da hunturu da iska da ake yi na sanya fatarmu ta lalace. Sai a ga mutum ya fara kauje da kurarraji a fata. Yana da matukar mahimmanci a kula da fata, musamman a wannan lokacin. Don haka ne a yau na kawo muku abubuwa da dama wanda za ku bi don kare fatarku.
·         A kasance ana shan ruwa sosai kamar kofi 8 a rana. Yin hakan na dada hasken fata.
·         Ana shafa man jiki kamar su ‘moisturizers’, yin hakan na kare fata daga zama mai gautsi.
·         Kada a rika kwanciya da kwalliya a fuska. Yin hakan na sanya kurarrajin fuska. A rika wanke fuska da sabulun wanke fuska kullum kafin a kwanta barci.
·         Yana da kyau a rage zama a cikin rana, domin hakan na sanya maikon fuska da kurarraji da kuma canza wa fatar launi.
·         Shin ko kun san cewa barci na dada kyau? Kwanciya da wuri domin samun barci na awa 8 na dada lafiyar fata.

Abubuwan da za a yi don samun fata mai sulbi a hunturu.
·         A kwaba ayaba da danyar madara, sannan a shafa a fuska. A jira na tsawon mintuna 20 kamin a wanke da ruwan dimi. Hakan na sanya fata sulbi.
·          A shafa kwababbar gwanda a fuska da wuya. Sai a jira na tsawon mintuna 15 kamin a wanke.
·         A tafasa kabeji, sai a rika wanke fuska da ruwan. Yin hakan na gyara fata sosai.