Yadda za a kula da tafin kafa saboda hunturu
Kasancewar a wanann lokaci da iskar hunturu ta fara kadawa akwai bukatar mutum ya ba tafin kafarsa kulawa ta musamman, don guje wa kamuwa da faso ko kaushin kafa wanda ka iya zamowa abin kunya ga mutum. Muna sane da yadda kaushi ko faso ke hana mutum sake wa wajen mike kafarsa a cikin taron […]
Kasancewar a wanann lokaci da iskar hunturu ta fara kadawa akwai bukatar mutum ya ba tafin kafarsa kulawa ta musamman, don guje wa kamuwa da faso ko kaushin kafa wanda ka iya zamowa abin kunya ga mutum. Muna sane da yadda kaushi ko faso ke hana mutum sake wa wajen mike kafarsa a cikin taron mutane, baya ga illar da hakan ke jawo wa ga lafiya, domin a wasu lokutan idan faso ya yi yawa a kafa yakan haifar wa kafar tsattsagewa wanda ke zama barazana wajen hana mutum tafiya yadda ya kamata, sai dai ya rika dage kafafuwa sakamakon radadin da kafar ke yi a duk lokacin da ya taka wurin da fason yake.
Ga wasu hanyoyi da ake bi wajen kula da tafin kafa:-
- Kafin a kwanta barci da daddare a shafe kafa da man kadanya
- A sanya safa
- Idan gari ya waye a zuba ruwan dumi a mazubi kamar robar wanka sannan a zuba gishiri ko kuma ruwan sabulun wanke kafa na kanti a ciki sannan a sanya kafafuwa a ciki a barsu tsawon mintuna goma.
- Sai a dauko dutsen goge kaushi a wanke saman da kuma tafin kafar da shi.
- Idan kafar ta yi kaushi sosai za a ga fata ta taso don haka za a iya amfani da reza a rerrede fatar sama-sama a zubar.
- Sannan sai a zubar da wanann ruwan a sake zuba wani ruwan dumin a cikin robar a mayar da kafar a ciki. Shi ma za a bar shi tsawon mintuna biyar.
- Sai a sami soso a wanke kafar sosai da shi.
- Idan an gama sai a fito da kafar a goge ruwan jiki sannan a shafe ta da man sanya laushin tafin kafa na kanti ko kuma idan babu a sake shafa man kadanya.
- Sai a sake sanya safa (a kula za a yi ta sa safa har sai an sami biyan bukata) idan mutum ya bi wannan hanyoyi wajen kula da tafin kafarsa zai ga bambanci cikin kwanaki kadan.