Yadda za a kyautata rayuwar tsofaffi

Daga Auwal Muhammad danlarabawa Rayuwar manya, wato tsofaffi, na tattare da wasu abubuwa da suke faruwa, kuma wadannan abubuwa suna da bukatar a duba su sosai, don samar da mafita mai kyau da za ta inganta rayuwar tsofaffin, da ba su ingantacciyar lafiya da ci gaba, ta yadda za su amfana da shi har zuwa […]

Yadda za a kyautata rayuwar tsofaffi
Yadda za a kyautata rayuwar tsofaffi

Daga Auwal Muhammad danlarabawa

Rayuwar manya, wato tsofaffi, na tattare da wasu abubuwa da suke faruwa, kuma wadannan abubuwa suna da bukatar a duba su sosai, don samar da mafita mai kyau da za ta inganta rayuwar tsofaffin, da ba su ingantacciyar lafiya da ci gaba, ta yadda za su amfana da shi har zuwa karshen rayuwar su ba tare da sun tagayyara ba, ko sun shiga wani hali na kaka-ni-ka-yi, wadanda suka hada da kamuwa da cututtuka na zamani da kuma tsufa.
Wannan babban kalubale ne a wajen mu, wanda matukar muna bukatar canji da rayuwa mai kyau, to sai mun zauna mun duba yadda muka koma wanda a baya can ba haka muke ba, nazari da hangen nesa shi ne zai kai mu ga wannan canji idan har muna neman tabaraki da albarka a rayuwar mu ta duniya gaba dayan ta.
Idan muka duba yanzu za mu ga yadda tsufa yake zuwa da matsaloli da dama, wadanda rashin kula ke haifar da su, ko kuma yawan tayarwa da tsofaffin hankali da jefa su cikin tunani, duk suna daga cikin abubuwan da suke kai tsofaffin ga wani yanayi na fadawa cikin matsaloli marasa misali. Kuma za su yi ta fama har mutuwa tazo a haka, alhali idan mun gane yadda za mu zauna da tsofaffi ina tabbatar da cewar za mu wanye da su lafiya, kuma su yi rayuwarsu lafiya cikin nishadi da kwanciyar hankali, abin sha’awa da son yin hira da su a kowanne lokaci, don jin tarihin abubuwan da ba mu san su bama.
Matsalolin da ake samu a wannan lokaci game da tsofaffi suna da yawa, kuma kowa da kowa ya sani sai dai kawai rashin kulawa da lamarin tunda ba abu ne mai sauki ba, amma dai idan aka dauke shi da sauki zai zo da sauki; idan aka fahimci juna aka san matakin da ya kamata a dauka na inganta rayuwar masu nisan shekaru. Da dama daga cikin tsofaffi ana samun su a cikin tunanin ya aka tsinci kai da iyalai da dangi. Sannan ya aka gama aiki; ina makomar wahalar aikin da suka yi a lokacin kuruciyar su, ya ’ya’yan su suke kula da su a yanzu haka, ya alakar yanzu take a wajen ’yan uwansu, ana tafiya da su a kowacce sabga ko kuwa an barsu saboda yanzu ba su da mamora, tsufa ya kama su; ana yi musu biyayya da hidimar da ta kama a yi musu a yanzu?
Idan suna da bukatu ana biya musu ita matukar da halin biya musu,  ana yi musu kalamai masu dadi don a kwantar musu da hankali tare da yi musu bayanai a natse, don fahimtar da su lamarin zamani;  ana kula da lafiyar su yadda ya kamata, don su ji dadin ta. Ana suturta su yadda ya kamata ba tare da an bar su a cikin najasa ko kazanta ba, ana kula da ibadar su yadda ya kamata?
Wadannan al’amura da aka jero su ne manyan abubuwa da tsofaffi suke bukata idan aka sama musu su lallai zaa gama lafiya sannan za’a samu tabarakin su, kamar yadda suka sha wahala da mu a lokacin ba a samar da mu ba. Su suka raine mu, har muka girma duk suna wahala da mu, har muka kai matsayin tsayawa da kafar mu, muna iya daukar nauyin kanmu da ma wasu da suke karkashin mu. Don haka suma mu tuna da nauyin da ke kanmu nasu, mu inganta musu rayuwar da ta rage musu a duniya, a rabu lafiya duk da cewar ba a san wa zai riga wani ba, don tsufa ba shi ba ne mutuwa, mu dai kasance masu biyayya a gare su da dauke musu wahalhalun da za mu iya dauke musu.
Mu zauna da su zaman fahimta, mu daina cewa suna cikin rudun tsufa kawai, mu san abin da suke so da wanda ba sa so, a ja su a jiki sosai,
Wannan yana daga cikin tsarin da na yi nazari a wannan lokaci da na samu cewar akwai ragwancin biyayya, da kula da ake yi wa tsofaffi. Ina mai kara kira da a kula da wannan kira wajen ganin an kokarta an samar da kulawa mai kyau da inganci akan su, kamar yadda suka kula da mu a baya kafin karfin su ya kare suma. Yana da kyau sosai a rayuwar mu ta duniya da lahira, lallai ne idan muka kyautata Allah zai kyautta mana, ya ba mu masu jin kanmu a gobe muma.
 Mu zama masu rayuwa mai kyau da ban sha’awa a ko’ina a fadin duniya. Allah ya sa mu gane, mu kuma amfana da wadannan bayanai masu mahimmancin gaske a zamantakewar mu da tsofaffin mu da ke raye, wadanda nasu suka riga mu gidan gaskiya Allah yajikansu, sannnan a ci gaba da yi musu addu’a, ita ce kadai za ta kai zuwa a gare su, sannan idan da dama a gina musu wani abu da za su samu lada da shi wanda ake kira Sadakatul-Jariya. Wani abu ne da ake yi a sadaukar da shi ga magabata, kamar gina masallaci da sauran abubuwa na neman lada a duniya.
Allah ya sa mu gane mu anfana gaba daya.
\
Auwal Muhammad danlarabawa
Chairman Muryar Matasan Jihar Kano ( Mumajka )
www.muryarmatasanjiharkano.webs.com
08060257926  kano Najeriya.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50